Man City na jiran tayin Madrid kan Rodri, Man Utd za ta ba Juve aron Zirkzee

Asalin hoton, Getty Images
Paris St-Germain ba ta da niyyar taya ɗanwasan tsakiya na Manchester City da Spain Rodri. (Sky Sports)
Sai dai kuma City na jiran tayi daga Real Madrid kan ɗanwasan mai shekara 30 amma tana fatan zai sabunta yarjejeniyarsa. (Guardian)
Leeds United na dab da amincewa da yarjejeniyar fam miliyan 40 domin ɗauko golan Ingila James Trafford daga Manchester City.(Athletic - subscription required)
Manchester United na tattaunawa kan bayar da ɗanwasanta aro na Netherlands Joshua Zirkzee mai shekara 25 zuwa Juventus tare da zaɓin saye kan fam miliyan 30. (Sun)
Paris St-Germain na son golan Parma da Japan Zion Suzuki, mai shekara 23 wanda ake alaƙantawa da Aston Villa da Juventus. (Sky Sport - in Italian)
Crystal Palace ta cimma yarjejeniya da Brest kan ɗanwasan baya na Faransa mai shekara 19 Raphael Le Guen. (L'Equipe - in French)
An yi wa Liverpool da Manchester City tayin ɗanwasan Paris St-Germain Ibrahim Mbaye bayan wakilinsa ya ce ɗanwasan na Senegal ba zai tafi Aston Villa ba a wannan bazara. (Teamtalk)
Real Madrid ta tattauna da wakilan Vincius Jr tare da fatan zai amince ya tsawaita kwantaraginsa duk da Arsenal ta nace wa ɗanwasan na Brazil. (Sky Sports, external)
Real Madrid ta sake taya ɗanwasan gaba na Ivory Coast Yan Diomande da aka bayyana darajarsa Fam miliyan 94. (Sky Sport - in German, external)
Sevilla na son sayar da Ruben Vargas, mai shekara 22, kan fam miliyan 17 yayin da Brighton da Newcastle da Aston Villa ke cikin ƙungiyoyin Premier da ke son ɗanwasan na Switzerland. (Mundo Deportivo - in Spanish, external)











