Illoli biyar da maganin ƙara ƙarfin maza ke haifarwa

magani

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Magungunan ƙara kuzari don haɓɓaka sha'awar jima'i na gargajiya su ne waɗanda ake haɗawa da tsirrai ko sassaƙe ko ganyayyaki da wasu haɗa-haɗe da ake sha ko shafawa domin ƙara ƙarfin gaba ko daɗewa ana jima'i.

A wasu lokutan ma, mutane sukan yi amfani da maganin da ake kira kuskura domin ƙara ƙarfin kuzarin.

Haka kuma akwai magungunan da ake samu a cikin kwalabe da sunan kamfani da lambar waya da adireshi.

A Najeriya, daga manyan harkokin kasuwancin da ke tafiya akwai sayar da magungunan maza.

A baya-bayan nan an samu labaran lokutan da ake tsinci gawar mutum mutane ko dai a gida ko a otel, inda a kan yi zargin cewa sun mutu ne bayan daɗewa suna jima'i, wanda wataƙila ya wuce ƙima.

A lokuta da dama idan hakan ya faru, ana zargin mazan da suka mutum da amfani da maganin maza domin daɗewa suna jima'i, wanda idan ba a yi dace ba sai zuciyaru ta buga su ce ga garinku nan.

Muhimmancin jima'i

Mutum ya kasance yana da lafiyar ta yin jima'i na da tasiri da lafiyar jikin ɗan'adam baki ɗaya da iyalai a zamantakewa da ma tattalin arzikin ɗaiɗaikun mutane da al'umma da ma ƙasashe kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana.

Samun damar maza da mata wajen cimma lafiyar jima'i da walwala ya dogara ne da fahimtar lafiyar jima'i a matsayin.

Wannan yana nufin jima'i na bayar da gudummawa wajen:

  • Lafiya ta jiki
  • Kwanciyar hankali
  • Lafiyar tunani
  • Iya mu'amala da jama'a cikin sauƙi

Illolin magungunan

Dr Ibrahim Balarabe Yahaya

Asalin hoton, Dr Ibrahim Balarabe Yahaya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dr Ibrahim Balarabe Yahaya, likitan da ke aiki a ɓangaren duba marasa lafiya da ake kira "Internal Medicine," a Asibitin Koyarwa na Barau Dikko da ke Kaduna. Ya ce babbar matsalar ita ce rashin sanin abin da ke ƙunshe a cikin magungunan.

"Shi ne mai sayarwa bai san da me aka haɗa ba, wataƙila kawai ya san maganin na ƙara kuzari, amma bai san sinadaran da ke ciki ba. Za ka ga akwai sinadarai da yawa, kuma kowane sinadari akwai inda yake aiki a jiki, wataƙila a ciki akwai mai ƙara kuzarin," in ji shi.

Dr Ibrahim ya ce akwai abubuwa da yawa da suke haifar da rage sha'awa ko rashin kuzari kamar haka:

  • Hawan jini
  • Ciwon suga
  • Ciwon hanta
  • Matsala a sinadarin ƴan aike na jikin mutum wato hormones
  • Rashin zaman lafiya da iyali

Likitan ya ce ko a asibiti ba kasafai ake so ana shan maganin ba, "saboda suma na asibitin suna da wasu illolin daban," in ji shi.

Babban likitan ya ce akwai binciken da ya nuna cewa kusan kashi 64 na maza suna amfani da maganin ƙara kuzari, "kuma kusan kashi 20 a ciki suna fuskantar matsala."

Daga cikin matsalolin da ake fuskantar, kamar yadda Dr Ibrahim ya zayyana akwai:

Ciwon kai

Ya ce matsalar ta fako ita ciwon kai. "Wasu ciwon na tsananin da sai an kai su asibiti, kuma ko mutum ya sha maganin ciwon kai ba zai tsaya ba sai maganin ya sake shi."

Ciwon ciki

Likitan ya ce akwai kuma ciwon ciki da mai shan maganin zai iya fuskanta. "Mutum ne zai sha maganin ya yi kwarkwaɗa, sai ciki ya ƙulle."

Cutar cancer

Dr Ibrahim ya ce rikicewar sinadarai ƴan aikin jiki wato hormones. "Idan ya zama mutum na yawan shan maganin, zai sa gaɓɓan da suke fitar da sinadaran hormones masu sa sha'awa su ƙara himma wajen fitarwa. Hakan zai sa gaɓɓan su rikice, sai su riƙa fitarwa sama da abin da ake buƙata, wanda hakan ke janyo cutar cancer."

Cutar koɗa

Likitan ya ce dama asali ƙoda ce mai aikin tacewa. "Don haka akwai sinadaran da ke janyo cutar ƙoda idan suka yi yawa a jikin mutum."

Dakatar da haihuwa

Dr Ibrahim ya ce za a iya samun sinadarai a cikin magungunan da za su shafi gaɓɓan da ke kula da haihuwa. "Shi ne za ka ga mutum ya samu matsalar haihuwa a yi ta zargin matansa, sai an je asibiti a gano matsalar."

Shawara

Dr Ibrahim Balarabe Yahaya ya ce akwai buƙatar sa ido sosai da kula wajen kula da lafiya.

"Matsalar na farawa ne tun daga lokacin aure, sai ka ga ana cewa za a shirya mutum. Idan da gaske sababbi ne, ya kamata ne su tsaya su daidaita kansu su tsara kansu ya yi daidai da asalin halittarsu, maimakon ƙarfin magani."

Likitan ya kuma ce akwai buƙatar idan mutum ya ga lafiyarsa ko yanayin kuzarinsa ya ragu, "sai mutum ya je asibiti a duba shi, idan an gano matsalar sai a yi magani," in ji Dr Ibrahim.

Maganin gargajiya

Magani

Asalin hoton, Getty Images

Ɗaya daga cikin manyan manufofin dabarar WHO kan magungunan gargajiya na duniya (2025–2034) shi ne haɗa ingantattun magungunan gargajiya, na ƙarin hanyoyin warkarwa da na haɗa‑haddar jinya cikin tsarin kiwon lafiya na ƙasa.

Sha'awar magungunan gargajiya tana ƙaruwa a duniya, in ji Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), inda ta nuna cewa har yanzu ƙasashe da dama na al'ummar Afirka na dogaro da su.

Saboda sauƙin samu kuma galibi suna da arha, jama'a da dama musamman masu ƙaramin ƙarfi suke fi son magungunan irin na gargajiya maimakon magungunan asibiti.

Sanannen al'amari ne yadda ake sayar da haɗa-haɗen magungunan gargajiya domin maganin cututtuka iri-iri kamar su 'Basir' da 'Ɗankanoma' da aka cin kasuwarsu musamman a Najeriya.

Akwai kuma magungunan da wasu ke iƙirarin cewa suna maganin kowace irin cuta a ko'ina, sannan akwai waɗanda suke iƙirarin suna da sahalewar hukumomi, musamman hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya wato NAFDAC.

Sai dai duk da cewa wasu na samun waraka ta hanyar amfani da magungunan, rashiN tsarin shan magani, da rashin tantance abubuwan da ke ƙunshe a ciki na jefa ƙaulani a zuciyar mutane.