Rodri zai yi jinya ta ɗan wani lokaci

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan tsakiya na Manchester City Rodri zai yi ɓatan dabo na wani ɗan lokaci ya yi jinya saboda tiyatar da aka yi masa.
Tun da fari sabon kocin ƙungiyar Enzo Maresca ya bayyana cewa za a yi masa tiyata ranar Litinin, dan haka "yana buƙatar hutu, yana buƙatar lokaci da zai warke sannan ya dawo".
Ba a sa lokacin dawowar shi ba ya zuwa yanzu.
City za ta fafata da Arsenal a wasan ƙarshe na Community Shield ranar 16 ga watan Agusta gabanin wasan da za su yi Premier da Bournemouth a ranar 23 ga watan na Agusta.
City ta ce Rodri "ya jima yana fama da rashin jin dadin bayansa amma yanzu anmasa aikin da zai kawo ƙarshen matsalar".
Rodri wanda yana da sauran shekara ɗaya da ta rage masa a kwantaraginsa, ana ta alaƙanta shi da REal Madrid bayan taimakawa ƙasarsa Spain da ya yi suka kai ga cin Kofin duniya. Kuma shi ne ya lashe kyautar ɗan wasan da ya fi kowa.















