Yadda Saudiyya ta shiga tsaka mai wuya kan yaƙin Iran da Amurka

Asalin hoton, AFP via Getty Images
- Marubuci, Frank Gardner
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC security correspondent
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Saudiyya na cikin tsaka mai wuya. Tun bayan da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da yaƙi kan Iran a ranar 28 ga watan Fabarairu, ƙasar Saudiyya ta yi ta ƙoƙarin ganin ba ta tsoma kanta ba a rikicin.
To amma a yanzu bayan da aka kai mata hari ta ɓangarori uku, an kai Saudiyya bango. A wannan mako Saudiyya tare da hadin gwiwar Amurka ta kai hari kan mayaƙan ƙungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran a ƙasar Iraqi, wadanda Saudiyya ke zargi da kai mata hari ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa.
Yanzu Saudiyya na cikin wani hali, kan ko za ta ci gaba da kai harin ne domin hana yunƙurin ci gaba da kai mata hari ko kuwa za ta ja baya ne a ƙoƙarin ganin yaƙin bai faɗaɗa ba?
A wannan hali wane ne ke kai hare-haren kuma a ina?
Da farko bari mu yi wani bayani a taƙaice. Muhimman ɓangarori biyu ne ke fafatawa a wannan yaƙi wanda yanzu haka yake addabar yankin Gulf da kuma Gabas ta Tsakiya tsawon wata biyar.
A bangare ɗaya akwai Iran da dakarunta na juyin juya hali (IRGC). Sai kuma ƙungiyoyin da ke goyon bayanta, kamar Houthi da ke Yemen, ƙungiyar da ta karɓe iko da mafi yawan ƙasar a shekarar 2014.
Haka nan kuma akwai wasu ƙungiyoyin da Iran ke tallafa mawa a Iraqi, waɗanda ake zargi da kai wa Saudiyya hare-hare a wurare 30, waɗanda Saudiyyar ta mayar da martani.
Sai kuma ƙungiyar Hezbollah da ke Yemen, wadda a yanzu ta sassauta.

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ɗaya ɓangaren yaƙin kuma, Amurka ce da cibiyar ayyukan sojinta na Centcom mai matuƙar ƙarfi da kuma ƙasashen Larabawa na yankin Gulf da kuma Jordan. Isra'ila ce kan gaba cikin ƙawayen Amurka da ke yaƙin, amma yanzu ta tsagaita da kai hare-hare kan Iran.
A baya-bayan nan kusan za a iya cewa Iran ta mayar da hare-harenta ne kacokan kan Jordan da Kuwait da Bahrain, sai kuma hare-haren da take kaiwa kan jiragen ruwan da ke ƙoƙarin ratsawa ta Mashigar Hormouz duk da gargaɗin da ta yi.
Shigowar ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai cikin yaƙin ya zama wani sabon abu, kuma hakan ya nuna yadda - idan har ba a cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin ba tsakanin Amurka da Iran - yaƙin zai iya ƙazancewa a yankin.
Akwai dalilan da suka sanya Saudiyya ke ƙoƙarin ganin ba ta shiga dumu-dumu cikin yaƙin ba.
Jagoran ƙasar, wato yarima mai jiran gado Mohammed Bin Salman na gudanar da wani shirin bunƙasa ƙasar da ya yi wa laƙabi da "Vision 2030''.
Manufarsa ita ce faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga na ƙasar a maimakon ɗanyen man fetur kawai, da kuma samar da kyakkyawan tsarin tattalin arziƙi da masana'antu waɗanda za su samar da ayyukan yi ga dubun-dubatar matasan ƙasar da ke kammala karatun jami'a a kowace shekara.
Ɗaya daga cikin ginshiƙan shirin shi ne janyo masu zuba jari na ƙasashen waje zuwa ƙasar. Kuma daga cikin shirin, shi ne za a gina rumbunan adanawa da sarrafa bayan intanet, waɗanda za su iya zama wurin da za a iya kai wa hari cikin sauƙi.
Ba zai zama abu mai kyau ba idan Saudiyya ta tsoma kanta cikin wannan yaƙi wanda zai iya haifar da gaba mai tsawo, wanda hakan zai sa ta zamo cikin barazanar hare-haren jirage marasa matuƙa a kudancin ƙasar daga mayakan Houthi na Yemen ko kuma miyagun makamai kai-tsaye daga Iran.
Idan muka waiwaya baya, a watan Satumban 2019 Saudiyya ta ci karo da wani hari da ya shammace ta.
Lokacin da dangantaka ta yi matuƙar tsami tsakaninta da Iran, ta wayi gari da wani mummunan hari da ƙungiyoyi masu goyon bayan Iran da ke Iraqi suka ƙaddamar a biyu daga cikin matatun man fetur ɗinta mafiya muhimmanci, wato Abqaiq da Khurais.
A wancan lokacin an yi zargin cewa mayaƙan Houthi daga Yemen ne suka kai harin, amma idan aka lura za a ga cewa ramukan da makaman suka burma duk suna kallon arewa ne.
Waɗannan hare-hare sun gurgunta rabin ayyukan fitar da ɗanyen man fetur na Saudiyya na tsawon kwanaki, kuma hakan ya sanya Saudiyya ta gane irin hadarin da muhimman kadarorin ƙasar ke ciki idan aka kawo irin wadannan hare-hare.
A ranar Litinin hotunan tauraron dan'adam sun nuna yadda ƙungiyoyi masu goyon bayan Iran suka sake kai hari da jirage marasa matuƙa kan matatar Abqaiq.
Sai kuma batun man fetur, wanda har yanzu shi ne ƙashin bayan tattalin arzikin Saudiyya.
Iran ta mayar da martani bayan ahre-haren da Amurka da Isra'ila suka kai mata a watan Fabarairu ta hanyar toshe Mashigar Hormuz, wata babbar hanyar da jiragen dakon mai ke ratsawa da ke tsakanin Iran da yankin Gulf, inda ta nan ne ake safarar kashi 20% na ɗanyen mai na duniya.

A nata martanin, Saudiyya ta ƙara yawan man fetur da take fitarwa - kimanin ganga miliyan biyar a rana ɗaya - ta hanyar bututunta wanda ya tashi daga gabas zuwa yamma, wanda ya haɗa da cibiyar fitar da man fetur dinta da ke kan tekun maliya a ɗaya ɓangaren.
Daga nan ne ake ɗaukar ɗanyen man a jiragen ruwan dakon mai zuwa kudu har zuwa ƙasashen yankin Asia.
To amma a ranar 13 ga watan Yuli Saudiyya ta jefa bama-bamai kan filin jirgin sama na Sanaa, babban birnin Yemen.
Gwamnatin Yemen da ke goyon bayan Saudiyya ta yi ikirarin kai harin, inda ta ce ta yi hakan ne domin hana wani jirgin sama na Iran daga sauka.
A matsayin martani, mayakan Houthi sun kai hari kan filayen jiragen sama mallakin Saudiyya a Abha da Jizan.
Wani abu da zai ƙara tayar da hankalin Saudiyya shi ne yadda mayaƙan Houthi suka fara kai hari kan jiragen ruwan Saudiyya da ke bi ta Maliya, wanda hakan ya sanya yake da matuƙar haɗari jiragen ruwa su bi ta mashigar Bab El Mandab da ke kudancin tekun Maliya.
Wannan zai hana Saudiyya fitar da ɗanyen mai.
Saudiyya ta kwashe shekara bakwai tana yi wa mayaƙan Houthi luguden wuta amma ta kasa gurgunta su.
Yaƙin da Saudiyya ta yi da ƴan Houthi ya ratsa dukkanin yankunan Yemen kuma ya haifar da ɗaya daga cikin yanayi mafi muni na jin ƙai a wannan zamani, wanda har yanzu ake shan wahala a kai.
A shekarar 2022, a don dole, Saudiyya ta amince da wata yarjejeniyar tsagaita wuta da mayakan Houthi, kuma akwai rahotanni cewa Saudiyya ta biya ƙungiyar wasu kuɗaɗe a matsayin diyya.
To amma a yanzu Saudiyya wadda ita ce ƙasa mafi ƙarfin arziƙi a yankin na sake fuskantar wata barazanar hare-haren ta kudancinta yayin da take fuskantar wata barazanar hare-haren ta arewaci daga Iraqi.
Babu ko ɗaya daga cikin waɗannan a gagarumin shirinta na bunƙasa ƙasar nan da shekarar 2030.












