Shin makaman Amurka sun kusa ƙarewa ne ya sa su dakatar da yaƙi da Iran?

- Marubuci, Bernd Debusmann Jr
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, White House reporter
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 9
Lokacin da Shugaban Amurka Donald Trump ya halarci wani taro tsaro na a Pennsylvania a farkon wannan watan tare da shugabannin manyan kamfanonin ƙera makamai na ƙasar, babban saƙonsa shi ne: a ƙera ƙarin makamai cikin sauri.
Trump ya shaida wa shugabannin kamfanonin ƙera makamai a taron da aka gudanar a Kwalejin Horas da Sojoji ta Amurka, tare da Sakataren Tsaro Pete Hegseth cewa, "Muna da makamai mafi inganci a duniya, amma muna buƙatar a riƙa ƙera su cikin sauri."
Gwamnatin Trump ta bayyana taron a matsayin wani ɓangare na shirin farfaɗo da masana'antun [ƙera makaman] Amurka da kuma ƙarfafa ƙarfin yaƙin ƙasar, abin da Hegseth ya kira "rumbun ƴanci" ko ma'ajiyar makaman 'yanci.
Sai dai abin da ba a fi mayar da hankali a kai ba shi ne yawan makamai masu tsada da kuma wahalar ƙerawa da Amurka ta lalata a kusan kwanaki 40 na hare-haren da ta kai Iran a ƙarƙashin Operation Epic Fury, da kuma hare-haren ramuwar gayya da suka biyo baya.
Gwamnatin Amurka ta ce zuwa yanzu yaƙin ya laƙume dala biliyan 37.5, inda mafi yawan kuɗin suka tafi wajen saye da amfani da makamai.
Kafin tsagaita wuta ta fara aiki a ranar 8 ga Afrilu, Fadar White House ta ce dakarun Amurka sun kai hare-hare kan wurare sama da 13,000 a faɗin Iran. Haka kuma na'urar kariyar sararin samaniyar Amurka ta kakkaɓo sama da jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami 1,700 da Iran ta harba a wannan lokaci.
A halin yanzu Amurka ta dakatar da hare-harenta domin bai wa tattaunawar diflomasiyya damar ci gaba.
Rahoton jaridar New York Times ya ce an shawarci Trump da ya dakatar da shirin ƙara tsananta yaƙin saboda hakan na iya ƙara rage yawan makaman da Amurka ke da su.
Sai dai Trump ya musanta cewa Amurka na fama da ƙarancin makamai.
A wata hira da Wall Street Journal, shugaban na Amurka ya ce ƙasarsa tana da makamai fiye da kowace ƙasa a duniya, kuma fiye da abin da take buƙata.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wannan batun ya daɗe yana tayar da muhawara a gwamnatin ƙasar. A watan da ya gabata, lokacin da aka tambayi Pete Hegseth kan lamarin, ya musanta cewa ma'ajiyar makaman Amurka na raguwa.
Sai dai alamu sun nuna ya sauya matsayinsa. A makon da ya gabata ya shaida wa Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Dattawan Amurka cewa Ma'aikatar Tsaro ta Pentagon na buƙatar ƙarin dala biliyan 87 domin cike "manyan giɓin" da ta fuskanta, ciki har da maye gurbin kayan aikin soja.
Har yanzu dai adadin makaman da Amurka ta kashe da kuma waɗanda suka rage a ma'ajiyarta na cikin bayanan sirri da ba a bayyana wa jama'a.
Sai dai bayanan da cibiyar bincike ta ƙasa da ƙasa ta Center for Strategic and International Studies (CSIS) da ke Washington ta tattara sun nuna cewa wasu nau'ukan makaman Amurka sun ragu matuƙa, kuma ba abu ne mai sauƙi a sake samar da su cikin ɗan lokaci ba.
Mark Cancian, tsohon Kanal a rundunar Marines ta Amurka kuma babban mai ba da shawara a cibiyar CSIS, ya ce "gwargwadon nau'in makamin, ana iya ɗaukar tsakanin shekara ɗaya zuwa biyar kafin a ƙera makami mai linzami guda."
Ya ƙara da cewa babu wata hanya da za a iya bi domin hanzarta wannan aikin.
Sai dai tambayar da ake ci gaba da yi ita ce ko da gaske Amurka na ƙarar da makamanta cikin sauri kuma hakan zai iya shafar ikonta na aiwatar da ayyukan soji da cimma manufofinta na tsaro.
An raunana ma'ajiyar makaman Amurka?
Makamai mafi muhimmanci da Amurka ta yi amfani da su a yaƙin sun kasu gida biyu: makaman kai hare-hare daga nesa, da kuma makaman kariyar sararin samaniya da ake amfani da su wajen kakkaɓo makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa.
Daga cikin makaman da ake kai hare-hare, Tomahawk Land Attack Missile (TLAM) na daga cikin waɗanda aka fi amfani da su. Ana harba wannan makami daga jiragen ruwa ko jiragen ruwa masu nutsewa, kuma yana iya kai hari kan wuraren da ke da nisan fiye da kilomita 1,600.
Waɗannan makamai na bai wa Amurka damar kai hare-hare kan wuraren soja masu muhimmanci, da kuma maɓoyar kwamandoji da sansanonin soja, ba tare da jefa matuƙan jiragenta cikin haɗari ba.
Binciken cibiyar CSIS ya ƙiyasta cewa an harba makaman Tomahawk sama da 1,000 a lokacin yaƙin, kuma ana ganin ma'ajiyar ba za ta koma yadda take kafin yaƙin ba sai zuwa shekarar 2031.
A cewar cibiyar, kowane sabon nau'in makamin Tomahawk na laƙume kusan dala miliyan 2.6.
A bangaren kariyar samaniya kuwa, makamin Patriot shi ne aka fi amfani da shi. Wannan makami ne da ake harbawa daga ƙasa domin kakkaɓo jiragen sama da makamai masu linzami.
CSIS ta kiyasta cewa an yi amfani da makaman Patriot har 1,430 a lokacin yaƙin, daga cikin kimanin makamai 2,330 da Amurka ke da su kafin yaƙin ya fara.
Kowane makamin Patriot yana laƙume kusan dala miliyan huɗu, duk da cewa ana amfani da shi wajen kakkaɓo jirage marasa matuƙa na Iran waɗanda farashinsu bai wuce tsakanin dala dubu 20 zuwa dubu 50 ba.
Masana sun ce maye gurbin waɗannan makamai ba abu ne mai sauƙi ba.
Mark Cancian, babban mai ba da shawara a cibiyar CSIS, ya ce ana ɗaukar shekaru da dama kafin a ƙera makami guda.
Ya ce ko da za a ware kuɗi a yau, ba za a samu sabon makami ba sai bayan shekaru uku ko huɗu, wani lokaci ma har biyar.
A cewarsa, makaman da ake karɓa a yanzu su ne waɗanda aka amince da kuɗinsu tun a shekarar 2023.
Hankali ya karkata kan Taiwan da Pacific
Yaƙin da Amurka ta yi da Iran ya zo ne a daidai lokacin da ake fara tattaunawa kan abin da wasu jami'an sojin Amurka ke kira "Davidson window", wato lokacin da ake ganin yiwuwar China ta kai hari kan Taiwan na ƙaruwa.
Wannan batu da aka daɗe ana muhawara a kai, wanda ke da muhimmanci ga sojin Amurka a yankin Pacific, ya samo asali ne daga wani zaman sauraron ƙorafi a Majalisar Dokokin Amurka a shekarar 2021.
A lokacin, Admiral Philip Davidson, wanda a wancan lokaci ke jagorantar dakarun Amurka a yankin, ya yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar mamayar Taiwan "cikin shekaru shida masu zuwa".
A shekarar 2023 kuma, tsohon Daraktan Hukumar Leken Asiri ta Amurka CIA, William Burns, ya yi hasashen cewa China na iya zama cikin a shirin kai hari kan Taiwan zuwa shekarar 2027.
China ta daɗe tana cewa za ta "sake haɗa" Taiwan da ƙasarta, inda take kallon tsibirin da ke mulkin kansa a matsayin wani lardi da ya balle daga cikinta. Duk da cewa ba ta ce za ta yi amfani da ƙarfi kai tsaye ba, ba ta taɓa kawar da yiwuwar hakan ba.
Har yanzu dai ana tababa kan ko Amurka za ta shiga yaƙi domin kare Taiwan idan China ta kai hari. Sai dai duk da rashin bayyana matsayinta a fili, Amurka na ci gaba da bai wa Taiwan makaman kariya.

Asalin hoton, Getty Images
Mark Cancian na cibiyar CSIS ya bayyana ƙarancin makaman Amurka a matsayin wani "rauni", inda yake cewa Amurka ba za ta samu yawan makaman da take so ba idan rikici ya ɓarke a yankin Pacific.
A cewarsa, hakan na iya ƙara haɗarin barin dakarun Amurka ba su shirya yadda ya kamata ba wajen fuskantar ɗimbin makamai masu linzami da jiragen yaƙin China.
Jami'an Amurka sun ce China na sa ido sosai kan yadda aka yi amfani da tsarin kariyar sama na Amurka a yaƙin Iran.
A cikin 'yan shekarun nan, Beijing ta zuba kuɗi masu tarin yawa wajen bunƙasa fasahar makamai masu linzami, ciki har da masu saurin gaske (hypersonic glide missiles) waɗanda suka fi na Iran ci gaba sosai.
Haka kuma China ta ƙara mayar da hankali wajen samar da dabarun amfani da ɗimbin jirage marasa matuƙa lokaci guda.
Sai dai ba kowa ne ke kallon raguwar ma'ajiyar makaman Amurka a matsayin matsala ba.
Jacob Olidort, tsohon jami'in leƙen asiri na CIA kuma tsohon mai ba da shawara kan manufofin Gabas ta Tsakiya a Ma'aikatar Tsaron Amurka, ya ce amfani da waɗannan makamai a fagen yaƙi yana aika wani saƙo mai ƙarfi ga abokan gaba da duniya baki ɗaya.
Yaya lamarin zai shafi Turai?
Takun-saƙar da ke tsakanin ci gaba da bai wa ƙawayen Amurka makamai da kuma kare ma'ajiyarta ta riga ta bayyana a yaƙin Ukraine.
A watan Oktoban 2025, watanni kafin fara Operation Epic Fury, Shugaba Donald Trump ya ƙi bai wa Ukraine makaman Tomahawk, inda ya ce hakan zai rage yawan makaman da Amurka ke da su.
Masana na ganin wannan mataki ya nuna irin yanayin da Amurka ke fuskanta yanzu bayan yaƙin Iran, tsakanin tallafa wa ƙawayenta da kuma kare nata ma'ajiyar makamai.
Jami'an Ukraine sun ce har yanzu suna matuƙar buƙatar makaman Patriot da sauran na kariyar sama domin dakile hare-haren jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami da Rasha ke ci gaba da kai musu.
A wata hira da BBC a watan Maris, Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce "yaƙin Iran ba wai kawai ya shafi farashin makamashi ba ne, har ma ya rage ma'ajiyar makaman Amurka da ƙarfin kamfanonin da ke ƙera makaman kariyar sama."
Ya ce hakan na nufin Ukraine ma na fuskantar ƙarancin makaman da take buƙata.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Zelensky ya bayyana cewa Amurka na ƙera makamai masu linzami tsakanin 60 zuwa 65 a kowane wata, wato kusan 700 zuwa 800 a shekara, inda aka yi amfani da makamai aƙalla 803 a ranar farko kaɗai ta yaƙinta da Amurka da Isra'ila..
Sai dai kwanan nan Trump ya ba jami'an Turai mamaki bayan ya amince a bai wa Ukraine damar ƙera makaman Patriot a cikin ƙasarta. Irin wannan tsari ya riga ya fara aiki a Jamus da Japan.
Elaine McCusker, wadda ta shafe shekara 13 tana aiki a Ma'aikatar Tsaron Amurka kuma yanzu ƙwararriya ce a cibiyar American Enterprise Institute, ta ce ƙwarewar da Ukraine ta samu wajen yaƙi da Rasha, da kuma ta Amurka a yaƙin Iran, na iya taimakawa wajen samar da sabbin makamai masu rahusa da za a iya ƙera su da yawa, domin su riƙa cike gurbin masu tsada da ƙarancin manyan makaman da ake amfani da su yanzu.
Duk da wannan batu da ake yi, masana sun ce babu wata alamar da ke nuna makaman Amurka na dab da ƙarewa da . Ba wai don ma'ajiyarta ba ta da iyaka ba ne, sai dai saboda ana ganin Iran ta fi fuskantar matsanancin ƙarancin makamai.
Mai magana da yawun Fadar White House, Anna Kelly, ta shaida wa BBC cewa sojojin Amurka na da isassun makamai da harsasai domin cimma dukkan manufofin tsaron Shugaba Donald Trump, har ma fiye da haka.
Sai dai ta ƙara da cewa duk da haka, Shugaba Trump ya ci gaba da ƙarfafa kamfanonin ƙera makaman Amurka su ƙara yawan makaman da suke samarwa.
A baya-bayan nan, hare-haren da Rundunar Tsakiyar Amurka (CENTCOM) ta sanar da cewa sun fi mayar da hankali ne kan raunana ƙarfin Iran da ke barazana ga zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.
Masana sun ce asarar da sojojin Iran suka yi ta fi ta Amurka nesa ba kusa ba, bayan jerin hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai, kuma Iran ba ta da ƙarfin da za ta iya maye gurbin waɗannan makamai cikin gaggawa.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Jason Brodsky, daraktan a hukumar ƴaki da mallakar makamin nukiliyar Iran ya ce mutane da dama na ɗaukar Iran a matsayin ƙasar da ke da makamai marasa iyaka, amma hakan ba gaskiya ba ne.
Ya ce hare-haren da ka kai mata sun yi mummunar illa ga wajen ƙera makaman Iran, tare da rage mata ƙarfin samar da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa a adadi mai yawa.
A cewarsa, makaman da suka rage wa Iran yanzu ana tanadar su ne domin yin barazana ga mashigar Hormuz, amma ya yi imanin cewa wannan ƙarfin ma na ci gaba da raguwa.
Ya ce gwamnatin Iran na fuskantar ƙarancin lokaci da za ta iya ci gaba da amfani da wannan damar.
Brodsky ya ƙara da cewa, a halin yanzu rikicin da ake yi da Iran shi ne abin da ya fi ɗaukar hankalin gwamnatin Amurka
Are you personally affected by the issues raised in this story?











