Ko ƴan hamayya za su iya kayar da Tinubu a 2027 ba tare da haɗaka ba?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A yayin da shirye-shiryen ƴan hamayyar Najeriya na dunƙulewa wuri ɗaya don tunkarar Tinubu a zaɓen 2027 ke fuskantar koma-baya, wasu ƴanƙasar sun fara tunanin ko ƴan adawar za su iya kai kunyarsu a zaɓen mai zuwa.

An samu yunƙuri da dama daga 'yan siyasa da ƙungiyoyi domin ganin ƴan hamayyar sun haɗe wuri guda amma kuma har yanzu haƙarsu ba ta cimma ruwa ba.

Ƴan hamayyar da kansu sun sha yunƙurin haɗewa wuri ɗaya don tunkarar Tinubun, amma kuma ba su cimma hakan ba.

Tun bayan zaɓen 2023 dai 'yan hamayya suka ƙudiri aniyar tattaunawa tsakaninsu da nufin dunƙulewa wuri guda domin kawar da Tinubu a 2027.

Sai dai duk da tattaunawar, har yanzu akwai alamun saɓani da bambancin ra'ayi tsakanin wasu daga cikin fitattun jagororin adawar ƙasar.

Masana harkokin siyasa na ganin cewa ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ke fuskantar 'yan adawa shi ne yadda ƙuri'unsu ke rarrabuwa tsakanin jam'iyyu da ƴan takara daban-daban, lamarin da wasu ke cewa na iya rage musu ƙarfin da za su iya amfani da shi wajen ƙalubalantar APC.

Sai dai wasu na da ra'ayin cewa nasarar zaɓe ba lallai ta dogara kacokan kan haɗaka ba, musamman idan aka yi la'akari da matsalolin tattalin arziki da na tsaro da ke fuskantar ƙasar, waɗanda ka iya yin tasiri kan yadda masu zaɓe za su yanke hukunci a lokacin zaɓe.

Mene ne ƙarfin jam'iyyun hamayyar?

Jam'iyyu uku ne dai ake ganin suna da tasiri a ƙasar a halin yanzu saboda yawan mabiyansu da jiga-jigan ƴansiyasar da ke cikinsu.

  • ADC

Ana kallon ADC a matsayin na gaba-gaba cikin jam'iyyun hamayyar Najeriya a halin yanzu, kasancewar a cikinta jagoran adawar ƙasar, Atiku Abubakar ke takarar shugaban ƙasar.

A shekarar da ta gabata ne jiga-jigan yan hamayyar suka yanke shawarar haɗewa a cikinta.

Jam'iyyar na da sanatoci tsakanin takwas zuwa tar, yayain da ake da ƴanmajalisar wakilai 17.

ADC na da fitattun jiga-jigan yansiyasa a cikinta da suka haɗa da Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar, tsohon shugaban majalisar dattawan ƙasar, David Mark da tsoffin gwamnonin Sokoto da Kaduna, da tsoffin ministoci da dama.

Sai dai duka da haka jam'iyyar ba ta da gwamna ko ɗaya a yanzu haka, wani abu da ake ganin zai iya rage mata karsashi a zaɓukan da ke tafe.

  • NDC

Jam'iyyar NDC na daga cikin fitattun jam'iyyun hamayya a Najeriya, duk da cewa ba a jima da yi mata rajista ba, ta yi fice ne bayan komawar Peter Obi da Kwankwanso cikinta a farkon shekarar da muke ciki.

Yanzu haka jam'iyyar na da sanatoci huɗu a majalisar dattawa da kuma yanmajalisar wakilai 17.

Jam'iyyar na da jiga-jigan ƴan siyasa irin su Peter Obi da ke yi mata takarar shugaban ƙasa da Sanata Rabiu Kwankwaso da ke takarar mataimakin shugaban ƙasa.

NDC na ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Bayelso, Sanata Henry Seriake Dickon.

Ita ma kamar ADC ba ta da gwamna ko ɗaya a Najeriya, sai dai ana ganin tana da ƙarfin magoya baya a Kano mai yawan jama'a saboda Kwankwaso.

  • PDP da AMP

Jam'iyyun PDP da AMP ne sauran jam'iyyun hamayyar da masu nazarin siyasa ke ganin na da tasiri.

Jam'iyyar APM na da gwamnoni har guda biyu a Bauchi da Oyo, wani abu da masana siyasa ke ganin zai ba ta damar taka rawa a zaɓen 2027.

Ita kuwa PDP, duk da cewa a yanzu ba ta da gwamna ko ɗaya a ƙasa, har yanzu tana da tasiri a fagen siyasar ƙasar.

Ko jam'iyyun za su iya nasara a ɗaiɗaikunsu?

Farfesa Kamilu Sani Fagge malami a jami'ar Bayero da ke Kano kuma mai sharhi kan al'amuran siyasar ƙasar ya ce duka da cewa ba wanda zai iya bugar ƙirji ya ce ga abin da zai faru ba, amma rashin haɗewar tasu na rage musu dama.

''Tafiyar da rarrabe ba ƙaramin rage musu damar nasara yake yi ba a zaɓen 2027'', in ji masanin siyasar.

Malaimin jami'ar ya kuma ce idan ƴan hamayyar suka shiga zaɓen a rarrabe ƙuri'un su za su yi matuƙar rabuwa.

''Idan muka duba zaɓen 2023 da ya gabata, tazarar da ke tsakanin Tinubu da Atiku ba da da yawa, don haka in da a ce a haɗe suke da sun ci zaɓe'', in ji shi.

To sai dai Dokta Ibrahim Baba Shatambaya, malami a tsangayar nazarin kimiyyar siyasa a jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto na da saɓanin ra'ayi.

Dokta Shatambaya na ganin cewa jam'iyyun hamayyar za su yi nasara ko da babu haɗaka saboda yadda ya ce talakawa na fusace da mulkin APC.

''Idan ka duba yanayin da ƙasar ke ciki na taɓarɓarewar tsaro da tattalin arziki, ni ina ganin sun isa dalilan da za su saka ƴan ƙasar su zaɓi wata jam'iyyar ta adawa koda ba su haɗe ba'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa koda jam'iyyun hamayyar ba su dunƙule ba, za su iya kayar da Tinubu da APC.

Malamin jami'ar ya ce duk da cewa jam'iyyun ba su da gwamnoni, za su iya samun nasara saboda a cewarsa a yanzu gwamnoni ba su da tasiri a zaɓen ƙasar.

Shi ma Farfesa Fagge ya ce kodayake ƴanƙasar na fusace da jam'iyyar APC, amma da wahala ƴan hamayyar su iya kayar da ita matsawar ba su haɗe wuri guda ba.

''Akwai abubuwa da dama za su taimaka wa APC, matsawar ƴan hamayyar suka gaza haɗewa wuri guda'', in ji shi.

Ya lissafo wasu matsaloli kamar amfani da kuɗi da amfani da ƙarfin gwamnati wajen gudanar da zaɓen.

Me ya hana ƴan hamayyar Najeriya dunƙulewa?

Farfesa Kamilu Fagge ya ce akwai daliai da dama da suka hana ƴan hamayyar dunƙulewar gabanin 2027.

Wasu daga cikin dalilin da masanin siyasar ya lissafo sun haɗa da:

  • Son zuciya da biyan buƙatar kai
  • Zargin da ake yi wa wasu na yi wa APC aiki
  • Amfani da dokoki wajen rarraba kansu
  • Barazana daga hukumomin gwamnati