Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 29/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 29/10/2026

Rahoto kai-tsaye

Aisha Aliyu Jaafar da Aminu Kutama

  1. 'Tangarɗar signar layin dogo ne musabbabin haɗarin jirgin ƙasan Iryo' - shugaban kamfanin

    Shugaban kamfanin jiragen ƙasa na Iryo, Fabrizio Favara, wanda jirginsa ya yi mummunan hatsarin da ya faru a wajen Madrid ranar Laraba, ya yi wa Majalisar Dattawan Sifaniya gargaɗi makonni uku da suka gabata kan matsalolin da ke tattare da tsarin siginar layin dogon.

    Favara ya yi wannan bayani ne yayin da yake gabatar da shaida a gaban wani kwamitin bincike da ke duba wasu hatsarin da ya faru a kasar. Tun da fari firai minista Pedro Sanchez ya ce gwamnati na kokarin gano musabbabin hatsarin.

    Ya ce tabbas za a yi bincike da gano dalilin hatsarin da kuma kaucewa faruwarsa nan gaba. Masu bincike a Sifaniya sun ce adadin waɗanda aka tabbatar sun rasu sun kai 69, ciki har da tsohuwar ministar kwadagon Sifaniya Fatima Banez.

  2. An dakatar da allunan talla na dijita a Masar bayan nuna hotunan batsa

    Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Masar ta umarci a kashe dukkan manyan allunan talla na dijital da ke birnin Alkahira, bayan da ɗaya daga cikinsu da ke kan wata babbar hanya ya nuna wani fim na batsa.

    A cikin wata sanarwa, kamfanin da ke da allon tallar, wato United Arab Advertising Company, ya ce wasu da ba a san ko su wanene ba sun yi kutse cikin nau’rar.

    A halin yanzu jami’an tsaro na gudanar da bincike kan lamarin.

    A ƙasan bidiyon da aka nuna akwai wani adireshin intanet da ke danganta da wata ƙungiyar masu kutse ta yanar gizo, wadda aka ce yawanci tana neman kuɗin fansa bayan kai hare-haren kutse ta internet.

    Wannan al’amari ya haifar da muhawara mai zafi a shafukan sada zumunta, inda wasu ke cewa ya kamata a kashe dukkan allunan talla na dijital har abada, saboda suna dauke hankalin direbobi kuma haskensu na damun masu amfani da hanya.

    Wani ganau ya wallafa cewa ya yi ta mamakin dalilin da ya sa cunkoson ababen hawa ke tafiya a hankali, kafin daga bisani ya fahimci abin da direbobin da ke wucewa suke kallo.

    Shekaru biyu da suka gabata, an kashe wani allon talla a birnin Giza bayan da ya nuna wani bidiyo mai suka ga Shugaban Masar, Abdel-Fattah al-Sisi.

  3. Fadar shugaban Najeriya ta musanta rashin lafiyar Tinubu

    Jami’an gwamnati a Najeriya sun musanta zarge-zargen cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tafi Saudiyya ne domin neman lafiya.

    A cikin wani saƙo daya daga cikin masu taimaka wa shugaban kan yada labarai ya wallafa a shafukan sada zumunta, ya sake jaddada bayanan da aka bayyana a baya cewa shugaba Tinubu, ya tafi Saudiyya ne domin yin Umara.

    Sanarwar ta ce yayin da yake can, shugaban zai yi wa Najeriya addu'ar samun zaman lafiya da tsaro da ake fama da shi. Haka kuma zai roƙi Allah ya yi masa jagoranci da sanya albarka a kokarin da ya ke yi na sake neman wa'adin mulki a karo na biyu a zaben shekara mai zuwa.

  4. Tinubu ya tafi Saudiyya domin aikin Umara

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bar Abuja babban birnin ƙasar zuwa Makkah da ke Saudiyya gudanar da aikin Umrah da ‘addu’o’i ga ƙasar’.

    A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fita a shafin X ta ce ziyarar za ta bai wa Tinubu damar natsuwa da yi wa Najeriya addu’o’in zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa.

    “A lokacin zaman nasa a Makkah, Shugaba Tinubu zai yi ayyukan ibada na Umara domin neman taimakon Allah da kuma albarka ga Najeriya da al’ummarta,” in ji sanarwar.

    Kafin barin babban filin jirgi na Abuja, Tinubu ya ƙaddamar da sabbin jiragen helikwafta guda biyar waɗanda rundunar sojin saman ƙasar ta saya.

    Jiragen sun haɗa da samfurin Airbus H-125 guda biyu da Agusta 109 Trekker B.

  5. APC ta dage kan takarar Uzodimma duk da hukuncin kotu

    Jam'iyyar APC a jihar Imo ta dage cewa Gwamna Hope Uzodimma ne ɗan takararta na kujerar Sanatan Imo ta Yamma a zaɓen shekarar 2027, duk da hukuncin babbar kotun tarayya da ta amince da tsohon gwamna Rochas Okorocha a matsayin ɗan takarar jam'iyyar.

    Jam'iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na jihar, Onwuasoanya Jones, ya sanya wa hannu a ranar Alhamis, a martanin da ta mayar kan hukuncin da Mai shari'a Obiora Egwuatu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yanke.

    Kotun ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta wallafa sunan Okorocha a matsayin ɗan takarar APC na kujerar sanatan, sannan ta umarci Uzodimma da ya daina gabatar da kansa a matsayin ɗan takarar jam'iyyar a zaɓen da za a gudanar ranar 16 ga Janairun 2027.

    Sai dai APC ta ce Uzodimma ne ɗan takararta, bayan ya lashe zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar tare da goyon bayan mafi yawan mambobinta.

    “Jam’iyyar na son bayyana karara cewa Mai Girma Sanata Hope Uzodimma, CON, shi ne ɗan takararmu na kujerar Sanatan Imo ta Yamma, bayan ya lashe zaɓen fitar da gwani na jam’iyyarmu tare da gagarumin goyon bayan mafi yawan mambobin jam’iyyar,” in ji sanarwar.

    Jam’iyyar ta ƙara da cewa sashen shari’arta zai nazarci hukuncin kotun domin tantance matakin da ya kamata ta ɗauka na gaba.

    “Sashen shari’a na jam’iyyar zai nazarci hukuncin da aka yanke kan wannan shari’a, sannan ya ɗauki matakin da ya dace,” in ji sanarwar.

  6. Gobara ta tashi a wani jirgin ruwa a mashigar Hormuz

    Cibiyar Kula da Harkokin Kasuwancin Jiragen Ruwa ta Birtaniya ta sanar da cewa ta samu rahoton tashin gobara a wani jirgin ruwa a mashigar Hormuz.

    A cewar sanarwar cibiyar, kyaftin ɗin wani jirgin ruwa ya bayar da rahoto da ƙarfe 3:00 na safiyar Alhamis, agogon Greenwich, cewa ya hango wani jirgin ruwa yana ci da wuta, mai tazarar mil tara na ruwa daga arewacin Khasab da ke ƙasar Oman.

    Har yanzu ba a fitar da wani bayani kan halin da ma'aikatan jirgin suke ciki ba, ko girman barnar da gobarar ta haddasa, ko kuma illolin da ta iya yi ga muhalli.

    Cibiyar Kula da Harkokin Kasuwancin Jiragen Ruwa ta Birtaniya ta buƙaci jiragen ruwa da su yi taka-tsantsan yayin wucewa ta yankin. Jami'ai na gudanar da bincike kan rahoton.

    Sanarwar ba ta ambaci musabbabin tashin gobarar ko kuma asalin rikicin.

  7. Sarki Felipe ya ziyarci asibitin da ke kula da waɗanda suka jikkata a hatsarin jirgin ƙasa

    Sarkin Spain, Felipe ya kai ziyara wani asibiti da ke birnin Toledo inda ake kula da mutanen da suka jikkata a hatsarin haɗuwar jiragen ƙasa da ya faru a ranar Laraba.

    Tun da farko an ruwaito cewa Sarkin da matarsa za su ziyarci asibitin domin tattaunawa da ma’aikatan lafiya da kuma waɗanda hatsarin ya shafa.

    A halin yanzu, ɗaruruwan jami’an agaji da na tsaro na ci gaba da kasancewa a wurin da hatsarin ya afku da kuma yankunan da ke kewaye da shi.

    A wani sabon bayani da Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Spain ta wallafa a dandalin X, an ce jami’ai 102 na hukumar Protección Civil suna aiki a wurin hatsarin da yankunan da ke kusa.

    Haka kuma, akwai jami’an ‘yan sanda 143 da kuma jami’ai 422 na rundunar Guardia Civil da ke ci gaba da gudanar da ayyukan ceto, tsaro da bincike dangane da lamarin.

    Hukumomi sun ce ana ci gaba da samar da agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa tare da gudanar da bincike domin gano musabbabin wannan mummunan hatsari.

  8. ‘Yansanda sun kama mutum biyu masu 'shigar dodanni' suna fashi a Akwa Ibom

    Jami’an rundunar ‘yansandan jihar Akwa Ibom sun kama wasu mutum biyu da ake zargin suna yin shigar dodannin Ekpo domin tsoratar da jamaʼa da kuma cin zarafin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

    Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Timfon John, ta fitar a madadin Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, CP Baba Mohammed Azare, an ce ce an kama waɗanda ake zargin ne a ranar Litinin a kan titin Abak zuwa Ukana yayin wani samame da jami’an ‘yan sanda suka gudanar.

    Sanarwar ta ce jamiʼan tsaro sun samu rahotannin cewa mutanen suna tsoratar da jama’a da kuma karɓar kuɗi daga matafiya da kuma kai hare-hare kan wasu mutane a sassan yankin Ikot Ekpene.

    An kuma ce jami’an sun samu kayan 'dodannin' Ekpo, tufafin kwaikwayo da adduna da masu da kibiyoyi a hannun waɗanda ake zargin.

    Rundunar ta bayyana cewa bincike na cigaba da gudana domin gano cikakken yadda lamarin ya faru da kuma gano ko akwai wasu mutane da ke da hannu a cikin zargin.

  9. NLC ta ƙalubalanci sabuwar buƙatar rance da Tinubu ya gabatar

    Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC), Kwamared Joe Ajaero, ya soki bukatar da Shugaba Bola Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dokoki ta Najeriya domin amincewa da sabon rancen waje da ya kai dala biliyan 20.5 da kuma Yuro biliyan 1.45.

    Yayin da yake bayani a shirin The Morning Brief na gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis, Ajaero ya ce har yanzu babu cikakken bayani kan dalilin da ya sa ake neman wannan rance.

    Jagoran ƙwadagon ya kuma yi zargin cewa Asusun ba da lamuni na Duniya (IMF), da sauran hukumomin da ke bai wa gwamnatin Najeriya bashi suna cutar da ƙasar maimakon taimaka mata.

    A cewarsa, yawan basussukan da ƙasar ke ci na ci gaba da durƙusar da tattalin arzikin Najeriya.

    A cewarsa, idan Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta yi watsi da buƙatar, gwamnatin tarayya ba za ta samu damar karɓar rancen ba.

    Wannan sabon buƙatar rance na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara mai zafi kan tsarin karɓar bashi na gwamnatin Tinubu da kuma yadda yawan basussukan ƙasar ke ƙaruwa.

  10. Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Maccido ya cika shekara 20 da rasuwa

    A rana irin ta yau, 29 ga watan Oktoba, shekara 20 ke nan da rasuwar marigayi Sarkin Musulmi na 19, Alhaji Muhammadu Maccido, a wani hatsarin jirgin sama da ya girgiza Najeriya tare da jefa al'ummar Musulmi cikin alhini.

    Marigayi Muhammadu Maccido ya rasu ne a ranar 29 ga Oktoba, 2006, lokacin da jirgin da yake ciki ya yi hatsari a kusa da Abuja.

    Lokacin bayan bikin Sallah ƙarama ne a shekarar 2006, inda Sarkin Musulmin ya tafi Abuja domin ganawa da shugaban ƙasa na lokacin, Olusegun Obasanjo.

    Sai dai yayin da yake komawa Sakkwato a cikin jirgin kamfanin ADC Airlines mai lamba 53, ya yi hatsari jim kaɗan bayan tashinsa.

    Yawancin fasinjojin da ke cikin jirgin sun mutu, ciki har da Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido, ɗansa Badamasi Maccido da kuma jikansa.

    Labarin rasuwarsa ya girgiza al'ummar Sakkwato da sauran sassan Najeriya, inda dubban mutane suka fito domin jimamin rasuwarsa.

    Sarki Muhammadu Maccido ya zama Sarkin Musulmi ne a ranar 21 ga Afrilu, 1996.

    Bayan rasuwarsa a shekarar 2006, an binne shi a Hubbare, makabartar sarakunan Sakkwato, kusa da kabarin mahaifinsa inda aka naɗa Sarkin Musulmi na yanzu Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III.

  11. Kotu ta soke takarar Uzodimma tare da bayar da ita ga Okorocha

    Wata Babbar Kotun Tarayya da ke babban birnin Najeriya Abuja ta umarci Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta (INEC) ta cire sunan gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, a matsayin ɗan takarar sanata mai wakiltar Imo ta Yamma.

    Kotun ta kuma umurci hukumar zaɓen da ta maye gurbin Uzodimma da tsohon gwamnan jihar, Rochas Okorocha, a matsayin ɗan takarar Jam'iyyar APC, kamar yadda jaridar DailyTrust ta ruwaito.

    Mai shari'a Obiora Egwuatu ne ya bayar da umarnin bayan ya yanke hukuncin cewa Uzodimma bai lashe zaɓen fidda gwani na jam'iyyar APC da aka gudanar a ranar 18 ga Mayu ba, wanda INEC ta sa ido a kansa.

    Yayin da yake yanke hukunci, mai shari'ar ya ce hujjojin da aka gabatar a gaban kotun sun tabbatar da cewa Okorocha ne ya samu mafi yawan ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen, don haka shi ne ya kamata a ayyana a matsayin wanda ya yi nasara.

    Daga nan sai Mai shari'a Egwuatu ya umarci APC da ta miƙa sunan Okorocha a matsayin ɗan takarar jam'iyyar a zaɓen sanatan Imo ta Yamma na babban zaɓen shekarar 2027.

    Kotun ta kuma haramta wa Uzodimma ci gaba da gabatar da kansa a matsayin ɗan takarar sanata na APC a zaɓen ranar 16 ga Janairu, 2027.

    Mai shari'ar, ya ce tsayar da Uzodimma takara ya saɓa wa sashe na 29 da na 32 na Dokar Zaɓe, kuma bai yi daidai da ƙa'idojin APC na gudanar da zaɓen fidda gwani ba.

    Haka kuma, Mai shari'a Egwuatu ya soki INEC kan amincewa da takarar Uzodimma duk da abin da ya bayyana a matsayin gamsassun hujjoji da ke nuna cewa gwamnan ba shi ne halastaccen wanda ya lashe zaɓen fidda gwanin ba.

  12. Rundunar IRGC ta yi iƙirarin kakkabo jirgi maras matuƙi na Amurka a Mashigar Hormuz

    Dakarun juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun ce sun tare wani jirgi maras matuƙi na Amurka kirar MQ-1, tare da harbo shi a sararin samaniyar gabashin mashigin Hormuz.

    A cewar sanarwar da sashen hulɗa da jama'a na IRGC ya fitar, an tare jirgin tare da lalata shi ne da safiyar Alhamis a kusa da gaɓar tekun Sirik da ke lardin Hormozgan.

    IRGC ta kuma yi iƙirarin cewa tun bayan fara yaƙin da Amurka da Isra'ila suka yi da Iran a watan Fabrairu, dakarun Iran sun harbo jimillar jirage marasa matuƙia na Amurka guda 54 kirar MQ-9 da kuma guda 14 kirar MQ-1.

    Zuwa yanzu dai jami'an Amurka ba su fitar da martani kan wannan rahoton ba.

  13. Najeriya ta amince da kashe dala miliyan 45 kan ƙarfafa matakan kariya a filayen jiragen sama

    Gwamnatin Najeriya ta amince da kashe dala miliyan 45.8 domin kafa tsarin kare lafiyar jama'a da kuma tunkarar barazana yaɗuwar cutuka a manyan filayen jiragen saman ƙasa da ƙasa guda biyar na Najeriya, domin ƙarfafa ƙarfin ƙasar wajen gano da kuma dakile yaɗuwar cututtuka masu yaɗuwa.

    Ministan Lafiya da Walwalar Jama'a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai bayani bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa, kamar yadda gidan talibijin na Channels ta ruwaito.

    Ya ce an shafe shekara biyu ana shirya wannan aiki, kuma za a aiwatar da shi ne ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu na tsawon shekara 20.

    A cewar Pate, an tsara wannan shiri ne domin cike giɓin da ke akwai a fannin lafiyar jama'a a kan iyakokin Najeriya, waɗanda sama da fasinjoji miliyan 18 ke bi ta cikinsu duk shekara.

    Shirin zai shafi Filin Jiragen Sama na Ƙasa da Ƙasa na Murtala Muhammed da ke Legas, Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, Mallam Aminu Kano da ke Kano, Akanu Ibiam da ke Enugu, da kuma Filin Jiragen Sama na Port Harcourt da ke Omagwa.

    Ya ce Najeriya ta daɗe tana sanya ido sosai a ƙofofin shigowa ƙasar tun kafin tabbatar da ɓullar Ebola a ranar 19 ga Oktoba.

    Ya ƙara da cewa mara lafiyar da aka gano da cutar ta samu sauƙi, yayin da ake ci gaba da bibiyar waɗanda suka yi hulɗa da ita.

  14. Saudiyya ta ce ta kakkabo makami mai linzami da 'yan Houthi suka harba gabashin ƙasar

    Ƙawancen soji ƙarƙashin jagorancin Saudiyya da ke yaƙi da 'yan tawayen Houthi a Yemen ya sanar da cewa na'urar kare sararin samaniyar ƙasar ta kakkabo tare da lalata wani makami mai linzami da 'yan Houthi suka harba zuwa yankin gabashin Saudiyya.

    Kakakin ƙawancen, Turki al-Maliki, ne ya bayyana hakan a wani rubutu da ya yi a shafinsa X ranar Alhamis.

    Saudiyya ta fuskanci hare-hare da dama daga 'yan Houthi masu samun goyon bayan Iran a wannan wata, ciki har da wani hari kan Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Riyadh, wanda aka bayyana a matsayin hari mafi muni da aka kai wa masarautar cikin shekaru masu yawa.

    A farkon wannan makon ma, 'yan Houthi sun sanar da cewa sun kai hari kan matatar man fetur ta Ras Tanura da ke yankin gabashin Saudiyya mai arzikin man fetur, ta hanyar amfani da makami mai linzami.

    Saudiyya ta zargi Iran da ƙarfafa 'yan Houthi su ƙara kaimi wajen kai hare-hare, amma Tehran ta musanta hannu a hare-haren.

    Bayan shekaru huɗu na aiwatar da tsagaita wuta mai cike da rauni, faɗace-faɗace sun sake ɓarkewa a Yemen a watan Yuli, 'yan watanni kaɗan bayan fara rikicin soja tsakanin Iran da Amurka wanda ya jefa yankin cikin babbar matsala.

  15. Ɗan takarar da ya sha kaye a zaɓen Brazil ya ayyana kansa a matsayin halastaccen shugaban ƙasa

    Ɗan takarar da ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasar Brazil, Flavio Bolsonaro ya ayyana kansa a matsayin halastaccen shugaban ƙasa.

    A cikin wata sanarwa da ya fitar bayan ya isa ƙasar Amurka, ya yi ƙorafin cewa an tafka maguɗi a zaɓen, sannan ya musanta zargin cewa ya tsere ne daga Brazil; inda ya bayyana cewa, ya fice ne domin kare lafiyar iyalinsa.

    Bayan Mista Bolsonaro ya lashe zagayen farko na zaɓen Brazil, Shugaba Lula da Silva ya lashe zagayen na biyu da tazarar ƙuri'u sama da miliyan huɗu, lamarin da aka danganta da fitowar mutane da yawa domin kaɗa kuri'a.

    Ana dai gudanar da bincike kan Mista Bolsonaro ne bisa zargin aikata laifin halasta kuɗin haram, kuma an ba shi umarnin ya mika fasfo ɗinsa.

  16. Wane mataki INEC za ta ɗauka kan Pantami da Gwarzo?

    Nan gaba a yau ne hukumar zaɓen Najeriya, INEC za ta fitar da matsaya kan wasu ƴantakarar gwamna da ta cire sunayensu daga cikin jerin yantakara a zaɓen 2027 da ke tafe.

    Daga cikin fitattun sunayen da ake sa ran ganin makomarsu a yau ɗin har da ɗantakarar gwamnan PDP a jihar Gombe, Farfesa Ali Isa Pantami, da ɗantakarar gwamnan Kano na NDC Comdr. Aminu Abdussalam gwarzo.

    Haka ma akwai sunayen ɗan takarar gwamnan Kaduna na NDC, Sanata Danjuma Laah da ɗan takarar gwamnan Jihar Benue na jam'iyyar SDP, Sebastine Hon.

    A makonnin da suka gabata ne INEC ta fitar da sunayen ƴantakarar gwamna, amma kuma babu sunayen waɗannan yantakara.

  17. Amurka ta umarci ma’aikatanta su fice daga Saudiyya saboda barazanar tsaro

    Ofishin Jakadancin Amurka da ke Saudiyya ya ce gwamnatin ƙasar ta umarci ma’aikatan da ba na musamman ba da kuma iyalansu su fice daga ƙasar daga ranar 23 ga Oktoba saboda barazanar tsaro.

    A cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin ya fitar sa’o’i kaɗan da suka gabata, ya ce sakamakon hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa da mayaƙan Houthi na Yemen suka kai kan filayen jiragen saman Saudiyya, ma’aikatan gwamnatin Amurka za su buƙaci samun izini na musamman kafin su yi amfani da kowane filin jirgin sama a ƙasar har sai nan gaba.

    Sanarwar ta ce hare-haren Houthi kan filayen jiragen sama da sauran muhimman kayayyakin more rayuwa na Saudiyya sun yi sanadin mutuwar fararen hula tare da haifar da mummunar tangarda ga zirga-zirgar jiragen sama, tare da gargaɗin cewa rikicin na iya ƙara kamari cikin sauri.

  18. 'Yan sanda sun kama matasa biyu kan zargin kitsa garkuwa da hakimi a Kano

    'Yan sanda a Jihar Kano sun ce sun kama wasu matasa biyu bisa zargin shirya yin garkuwa da hakimin ƙauyen Bangare da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa, bayan da suka yi masa barazana ta waya.

    Waɗanda ake zargin, sun shiga hannu ne bayan wani samame na sirri da aka gudanar sakamakon rahoton da hakimin ƙauyen, Malam Idris, ya kai wa jami'an tsaro kan barazanar da aka yi masa a ranar 24 ga Oktoba.

    Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, a cikin wata sanarwa ya ce hakimin ya kai rahoton lamarin hedikwatar 'yan sanda ta shiyyar Gezawa a ranar 26 ga Oktoba.

    Sanarwar ta ce wanda ya kira wayar ya yi barazanar yin garkuwa da hakimin da misalin ƙarfe 9:33 na dare, lamarin da ya sa jami'an 'yan sanda suka fara bincike, wanda ya kai ga kama mutanen biyu da ake zargi.

    'Yan sandan sun ce waɗanda ake zargin sun amsa aikata laifin, yayin da ake ci gaba da bincike kafin gurfanar da su a kotu.

  19. Netanyahu ya yi zargin maguɗi a zaɓen Isra'ila

    Jam’iyyar Likud ta Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ta zargi jam’iyyun Larabawan ƙasar da maguɗin zaɓe ta hanyar cin hanci da razanarwa da amfani da tashin hankali.

    A cikin wata sanarwa, jam’iyyar Likud ta ce ta miƙa ɗaruruwan hujjoji da suka shafi waɗannan zarge-zargen ga ƴansanda da hukumar tattara bayanan sirri ta cikin gida ta Isra’ila, Shin Bet, da kuma hukumomin zaɓe.

    Netanyahu ya ce: “An yi maguɗi a zaɓen Isra’ila, kuma jam’iyyun Larabawa da ke goyon bayan ta’addanci da rushe ƙasar Yahudawa ne suka aikata hakan.”

    Ya ƙara da cewa waɗannan jam’iyyun sun tattara masu kaɗa ƙuri’a ta hanyar barazana da bayar da cin hanci da tashin hankali da amfani da takardun bogi da shirye-shiryen da aka haramta.

    Sai dai, jam’iyyar Likud ce ta yi waɗannan zarge-zarge, kuma har zuwa yanzu babu tabbaci ta hukuma daga cibiyoyin da abin ya shafa.

    Ana dai ci gaba da ƙirga ƙuri’un zaɓen, kuma ana sa ran za a sanar da sakamakon zaɓen nan ba da daɗewa ba.

    Zuwa yanzu dai babu wata jam'iyya ɗaya da alamu suka nuna cewa za ta iya kafa gwamnati ba tare da ƙawance da wata ba.

  20. An fara makoki a Sifaniya bayan mutuwar mutum 68 a hatsarin jirgin ƙasa

    Spain ta fara zaman makoki na tsawon kwana uku, bayan hatsarin jirgin ƙasa a jiya Laraba, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 68 waɗanda har yanzu ba a gama gano da yawa daga cikinsu ba.

    Wani jirgin ƙasa da ke kan hanyarsa ta zuwa Seville daga Madrid ne ya ci karo da wani jirgin na daban da ke tsaye a kan layin dogon.

    Wakiliyar BBC ta ce Maganar da aka naɗa tsakanin masu kula da jirgin ƙasa a Madrid, da direbobin jirgin mai tafiya - sun nuna cewa an bai wa jirgin ƙasan mai gudun gaske izinin wucewa duk da cewa daya jirgin ya yi minti 17 a tsaye a kan layin.

    Wannan shi ne karo na biyu da aka yi mummunan hatsari a kan layin, cikin ƙasa da shekara daya.