Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Qur'ani zalla: Asalinsu, aƙidarsu da tasirinsu a Najeriya
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
A cikin ƴan shekarun nan, an samu ƙaruwar muhawara a Arewacin Najeriya kan ƙungiyoyin da ake kira ƴan Qur'aniyyun ko ko Qur'ani zalla, wato mutanen da suke da ra'ayin cewa Alqur'ani kaɗai ya isa a matsayin tushen addinin Musulunci ba tare da komawa ga Hadisan Annabi Muhammad (SAW) da tsarin fiƙihun malamai ba.
Wannan muhawara ta ƙara ɗaukar hankali musamman sakamakon fitowar wasu masu wa'azi da masu sharhi a kafafen sada zumunta da ke yaɗa wannan fahimta, waɗanda ake tunanin suna ƙara zamanantar da tsarin.
A farkon makon nan ne wasu ƴanbindiga suka harbe fitaccen malamin da ya yi fice wajen yaɗa manufar, musamman a kafofin sadarwa na zamani wato Sheikh Yahaya Masussuka.
Ƙungiyar Ansaru mai alaƙa da ƙungiyar Al'Qaeda ce ta ɗauki alhakin kashe malamin, duk da cewa wasu daga ɗalibansa sun bayyana cewa suna da fahimtar akwai lauje cikin naɗi.
Shin mece ce karantarwar masu wannan aƙida? yaushe tsarin ya fara yaɗuwa? kuma ina asalinsu?
Asalin ra'ayin Qur'ani kaɗai a duniya
A takardarsa mai taken Scripture, Science & Sense: A Neo-Quranist's Discourse in Northern Nigeria, Dokta Murtala Uba Mohammed ya bayyana cewa fitowar wannan sabon salo na Qur'ani zalla a Arewacin Najeriya na wakiltar wani muhimmin sauyi a tunanin addinin Musulunci, domin yana ƙalubalantar tsarin ilimin Musulunci da aka gina tun ƙarni da ƙarnuka.
A cewar marubucin, ra'ayin cewa Alqur'ani kaɗai ya isa a hukunce-hukunce ba sabon abu ba ne gaba ɗaya, domin a cewarsa, tun farkon tarihin Musulunci an samu wasu ƙungiyoyi da suka yi muhawara kan matsayin Hadisi.
Ya ce akwai ƙungiyoyi irin su:
Mu'utazilawa
Waɗanda suka fi bai wa hankali muhimmanci wajen fahimtar addini.
Khawarij
Waɗanda suke cewa: "Lā hukma illa lillah" wato "Babu hukunci sai na Allah"
Sai dai marubucin ya yi gargaɗin cewa waɗannan ƙungiyoyi ba su yi watsi da Hadisi gaba ɗaya ba.
Kamar yadda ya rubuta: "Fitowarsu da ƙarfi a ƙarni 21 musamman yadda tattaunawarsu ta ƙaru a arewacin Najeriya ya buɗe ƙofar tattaunawa kan binciken addinin Musulunci, musamman kan fahimta da amfani da Qur'ani."
Dokta Murtala ya ce "yana da muhimmanci a fahimci yadda gyaran addini ya gudana a Arewacin Najeriya. Tun bayan shigowar Musulunci tsakanin ƙarni na 11 da na 14, an samu malamai da sarakuna waɗanda suka yi ƙoƙarin ƙarfafa koyarwar Musulunci," in ji shi.
Marubucin ya yi nuni da sarakuna kamar:
- Mai Humai da Mai Idris Alooma a Borno
- Sarkin Kano Alu Yaji
- Muhammadu Rumfa
- Malaman Katsina masu alaƙa da cibiyar Gobarau
Duk waɗannan sun yi aiki ne cikin tsarin Musuluncin Sunnah wanda ya haɗa Alqur'ani da Hadisi.
Sai dai marubucin ya nuna cewa babban juyi da sauyin da aka samu shi ne jihadin Sheikh Usmanu Danfodiyo a ƙarni na 19, wanda ya kafa Daular Usmaniyya tare da gina tsarin ilimi da shari'a bisa Alqur'ani da Hadisi da kuma fikihu.
Murtala Uba Mohammed ya jaddada cewa kusan dukkanin gyare-gyaren addinin da aka samu a tarihi sun kasance ne a cikin tsarin ilimin Musulunci na gargajiya.
"Gyara a tarihin Musulunci yawanci yana nufin gyarawa da ingantawa, ba rusa tsohon tsarin gaba ɗaya ba.
Bayyanar Qur'ani zalla a zamani
Marubucin ya nuna cewa a ƙarni na 19 da na 20 ne aka fara samun cikakken motsi na Qur'ani zalla na zamani.
Ya ce a Indiya da Pakistan, mutane irin su Sir Syed Ahmad Khan da Aslam Jairajpuri
Ghulam Ahmad Perwez ne suka fara kira da sake nazarin matsayin Hadisi.
"Daga baya aka samu ƙungiyar Ahl al-Qur'an, wacce ta fito fili tana iƙirarin cewa Alqur'ani ne kaɗai tushen addini."
Ya ƙara da cewa a ƙasar Masar kuma, "malamai irin su Muhammad Abduh sun ba da muhimmanci ga amfani da hankali wajen fahimtar addini. Kodayake ba su ƙi Hadisi ba, amma salon tunaninsu ya taimaka wajen buɗe hanya ga sabbin masu ra'ayin Qur'ani kaɗai."
Fitattun jagororin Qur'ani zalla a duniya
Marubucin ya ambaci wasu mutane da suka taka rawa wajen yaɗa wannan tunani kamar haka:
Rashad Khalifa
Wanda ya shahara da abin da ya kira Code 19, yana amfani da lissafi wajen fassara Alƙur'ani.
Ahmed Subhy Mansour
Ɗaya daga cikin fitattun masu yaɗa Qur'ani zalla ta kafafen intanet.
Edip Yüksel
Wanda ya mayar da hankali wajen haɗa Qur'ani zalla da hankali da binciken zamani.
Kassim Ahmad
Masanin falsafa daga Malaysia wanda littafinsa Hadis: Satu Penilaian Semula ya ƙara ɗora Qur'aniyyanci a kan turba.
A cewar marubucin: "Ɗaya daga cikin abubuwan da suka bambanta sabon yanayin Qur'ani zalla shi ne amfani da shafukan intanet da kafafen sada zumunta wajen yaɗa ra'ayinsa.
Zuwan Qur'aniyyanci Najeriya
A cewar Murtala Uba Mohammed, motsin Qur'ani zalla bai daɗe da samun karɓuwa a Arewacin Najeriya ba.
Ya bayyana cewa dukkan manyan ƙungiyoyin gyaran Musulunci a Najeriya, daga Shehu Danfodiyo zuwa Izala da sauran su, sun ci gaba da amincewa da Hadisi da fikihun malamai.
Sai dai akwai wasu ƙungiyoyi a tarihi da suka yi kama da Qur'ani zalla.
Daga cikinsu akwai:
- Salihawa
- Digawa
- Isawa
- Yanfukafukai
- Maitatsine
Mai binciken ya yi nuni da cewa wasu daga cikin waɗannan ƙungiyoyi sun kasance masu ƙin wasu nau'ikan Hadisi ko koyarwar malamai.
Sai dai marubucin ya ce sabbin ƴan Qur'ani zalla a yau sun bambanta domin suna amfani da kalmomin kimiyya, hankali da tsarin zamani wajen kare ra'ayinsu.
Masussuka da sabon Qur'ani zalla a Najeriya
Daga cikin mutanen da suka fi fito da wannan ra'ayi a Arewacin Najeriya akwai Malam Yahaya Masussuka.
Marubucin ya bayyana shi a matsayin: "Ɗaya daga cikin manyan wakilan ƴan Qur'ani zalla na wannan zamani a Arewacin Najeriya."
A cewarsa, Masussuka ya samo asali ne daga iyalin da suka fito daga Katsina amma suka zauna a ƙauyen Masussuka da ke Ningi a jihar Bauchi, sannan ya ce marigayin ya yi karatu a tsarin Tijjaniyya kafin daga baya ya rungumi ra'ayin Alqur'ani kaɗai.
Dokta Murtala ya ce malamin ya zo da sabon salo a tsarin, wajen zamantar da yaɗa fahimtar ta hanyar amfani da:
- Kafafen sada zumunta,
- Hirarraki a rediyo da talabijin
Fahimtar ƴan Qur'aniyyun
Alƙur'ani kaɗai ya isa
Malamin jami'ar ya ce babban ginshiƙi na aƙidarsu shi ne cewa Alƙur'ani cikakke ne kuma baya buƙatar Hadisi.
Ƙin karɓar Hadisi
Masu fahimtar suna kallon yawancin Hadisai a matsayin abubuwan da ba za a iya tabbatar da sahihancinsu ba, saboda haka suna ganin bai kamata su zama tushen hukunci ba.
Amfani da hankali
Suna ba da muhimmanci ga hankali da tunani wajen fahimtar addini.
Ƙin bin mazhabobi
Ba sa ganin wajibi ne bin Imam Malik da Abu Hanifa da Imam Shafi'i da Imam Ahmad ko wasu manyan malamai na fikihu.
Fassarar Alƙur'ani da Alƙur'ani
Masussuka yana amfani da abin da yake kira: "Tafsīr al-Qur'an bi al-Qur'an." wato
fassara ayoyin Alqur'ani da Alqur'ani.
Tasirin fahimtar
Murtala Uba Mohammed ya lura cewa wasu daga cikin masu ilimi sun yaba wa Masussuka, inda ya bayyana da shi da cewa, "Masussuka ya nuna cewa yana da zurfin sani a harkokin addini."
Saboda amfani da shafukan sada zumunta, ra'ayoyin ƴan Qur'ani zalla sun samu damar isa ga:
- Matasa,
- Ƴan boko,
- Masu amfani da intanet.
Sheikh Yayaha Masussuka
Sheikh Yahya Masussuka, fitaccen malamin addinin Musulunci ne daga jihar Katsina, ya shafe sama da shekaru 30 yana wa'azi, tun yana ɗan shekara 13.
An haifi Sheikh Yahya Masussuka a ranar 19 ga Satumba, 1979, a ƙauyen Biyawa, da a wancan lokaci ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Batsari, kafin ya koma ƙaramar hukumar Dutsinma a jihar Katsina, arewa maso yammacin Najeriya.
Yana da mata biyu da 'ya'ya bakwai. Cikin a'yansa akwai Yusuf, wanda ake sa ran zai ci gaba da ayyukan da'awa na mahaifinsa ya bari.
Sheikh Masussuka ya yi karatu a wurare daban-daban, musamman a makarantun allo da tsangaya, kafin ya zarce zuwa jami'ar Al-Azhar da ke Masar, da kuma ƙasar Oman.
Ya yi karatu a hannun malamai da dama, ciki har da wasu fitattu kamar Sheikh Alhassan Lamido da Sheikh Malam Usman Dangungu na Kaduna.
Ya fara wa'azi ne yana da shekara 13, abin da ya sa ya shafe fiye da shekaru 30 yana koyar da addini, kamar yadda sakatarensa, Dr Mustapha Haruna ya tabbatar wa BBC.
A tsawon rayuwarsa, malamin ya fuskanci ƙalubale daban-daban a yayin gudanar da ayyukan da'awarsa, ciki har da ƙoƙarin kama shi da kuma kiransa da jami'an tsaro ke yi.
An kuma taɓa ɗaure shi na tsawon watanni tara a gidan yari a jihar Katsina kan wani lamari da ya shafi wa'azinsa.
Ya rasu ne bayan wasu 'yan bindiga sun harbe shi a kofar gidansa da ke yankin Dutsen-Ma, kamar yadda 'yan sanda suka tabbatar.