Yadda kawo ƙarshen yaƙin Iran ya fallasa raunin Amurka

Asalin hoton, EPA
- Marubuci, Jeremy Bowen
- Aiko rahoto daga, Beirut
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Wannan yaƙin ya kasance wani babban kuskuren manufofin ƙasashen waje na Shugaba Donald Trump - ya zuwa yanzu.
Hakan ya rage irin kallon tsoron da abokan gaban Amurka ke yi ma ta.
Ta lalata dangantakarta da ke tsakaninta da shugabannin ƙasashen larabawa masu arzikin man fetur na yankin Gulf, lamarin da zai ɗauki dogon loakci kafin a iya dawo da shi yadda ya ke a baya.
A bayan fage, jami'an ƙasashen sun riga sun fara magana game da karkatar da mubaya'arsu, da kuma wajibcin neman hanyoyin zama tare da Iran, makwabciyarsu da ke ketaren ruwa. Ƙasar China za ta sa ido sosai yayin da Amurka ta ɓarnatar da makamanta da ke da wahalar samu ta kuma fuskanci gaskiyar rashin ƙarfin ikonta.
Idan har ba a samu wani cikas ba ana sa ran yarjejeniyar za ta kawo ƙarshen yaƙin da ya samo asali daga yadda Amurka da Isra'ila suka yi kuskure wurin raina ƙarfin maƙiyansu da ke Tehran. Hakan dai zai taimaka wruin kwantar da hankalin mutanen da yaƙin ya hargita musu rayuwarsu.
Yarjejeniyar za ta sake buɗe mashigar Hormuz, in ji Trump, tare da rage matsin lamba kan tattalin arzikin duniya da kuma haƙiƙanin rayuwar ɗaruruwan miliyoyin mutanen da ke cikin mawuyacin hali a duniya.
An kashe dubban mutane a Gabas ta Tsakiya. An lalata gidaje da wuraren kasuwanci. Samar da takin zamani da ya dogara da kayan da ake jigila ta mashigar na iya nufin mutane da ke ƙasashe matalauta za su yi fama da yunwa daga baya a cikin shekara, inda ƙasashen Afirka da ke yankin kudu da hamadar Sahara ke cikin haɗari.
Yarjejeniyar ba tazaman lafiya ba ce. Cikakkiyar yarjejeniyar, wanda masu shiga tsakani suka ce yana ɗauke da sharuɗɗa 14 akan shafuka biyu, har yanzu dai ba a wallafa ta ba. Sai dai baya ga sake buɗe mashigin ruwan, yarjejeniyar fahimtar juna ta ƙara tsawaita tsagaita wuta tare da dage takunkumin da sojojin ruwan Amurka suka yi wa tashar jiragen ruwa na Iran.
Ta dai ƙara tura muhimmin batu da ke cike da sarƙaƙiya zuwa zagayen tattaunawa na gaba . Wannan ajandar dai za ta haɗa da makomar shirin nukiliyar Iran da kuma matakin sassauta takunkumin da za ta samu domin samun sassauci.
A ƙarshe, an shata layi a ƙarƙashin yaƙin da Amurka da Isra'ila suka fara a ranar 28 ga Fabrairu.

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yanzu dai a mayar da hannun agogon baya zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu, yayin da sojojin Amurka da na Isra'ila ke shirin kai farmaki, suna shirya makaman jiragensu, tare da yiwa ma'aikatansu bayani, da kuma tsara wuraren da makamansu za su kai wa hari.
A Geneva, Iran da Amurka sun shiga cikin abin da aka bayyanawa duniya a matsayin muhimmiyar tattaunawa da nufin taƙaita shirin nukiliyar Iran. Majiyoyi da yawa sun shaida min da wasu cewa masu sasantawa na Iran sun yi imanin cewa suna cikin wani tsari mai mahimmanci kuma sun shirya hakura da wasu muhimman abubuwa yayin tattaunawar.
A gaɓar Tekun Fasha, mashigar ruwan Hormuz buɗe ta ke, wanda ke ba da damar wucewa da kusan kashi 20% na buƙatun duniya na mai da iskar gas, da kuma sauran sinadaran da ake iya tacewa daga ɗanyen mai waɗanda suka zama mahimman abubuwan rayuwa na zamani.
Yarjejeniyar ta fahimtar juna ta share hanyar da masu tattaunawa kan batun nukiliyar za su sake zama tare da bayar da damar da jiragen ruwa za su wuce ta mashigar ruwan. Matakin da su ke kai ke nan sa'o'i 24 kafin Amurka da Isra'ila su fara yaƙin.
A farkon jerin munanan hare-haren bazata, Isra'ila ta kashe jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Ali Khamenei da kuma na kusa da shi masu ba shi shawara. A lokaci guda kuma, wani harin da Amurka ta kai ya lalata wata makaranta a Minab a kudancin Iran, inda bincike da dama suka nuna cewa sama da fararen hula 150 ne aka kashe, cikinsu har da yara ƴan makaranta aƙalla 120, yawancinsu ƴan mata ƴan ƙasa da shekaru 12.
Da Trump da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, duk sun yi bidiyo don sanar da fara yaƙin da suka yi imanin ba za a daɗe ana yi ba, kuma za su yi nasara cikin ƙanƙanin lokaci. Wannan dai rashin lissafi ne da ya matuƙar bayar da mamaki.
A jawaban nasu sun yi hasashen faɗuwar gwamnatinTehran. Madadin haka, neman tsira ya ƙarfafa ƙwarin gwiwar gwamnatin. Babban abin da suka fi fargaba shi ne ne cikakken yunƙurin tabbatar da juyin mulki da Amurka da Isra'ila za su jagoranta. HAkan ya faru kuma bai yi nasara ba. Shugabannin Tehran da suka tsira sun ƙara samun ƙwarin gwiwa.
An maye gurbin Khamanei da masu ba shi shawara cikin sauri, da ɗansa Mojtaba a matsayin babban shugaba da kuma wasu matasa a matsayin kwamandoji, waɗanda manyan shugabannin dakarun kare juyin juya halin Musulunci suka mamaye. Kowannensu yana da aƙida irin ta mazan jiya, amma ba su da taka-tsan-tsan, a shirye suke su yi kasada a cikin abin da suka dauka a matsayin gwagwarmayar tabbatar da wanzuwar gwamnatin Musulunci a Iran.
Sun matsa ƙaimi kan wata dabarar da aka tsara ta rufe mashigar Hormuz da kai farmaki kan ƙasashen Larabawa maƙwabtan Iran da sojojin Amurka da sansanoninsu, da ita kanta Isra'ila. Kalaman sakataren tsaron Amurka Peter Hegseth na iƙirarin cewa ƙarfin Amurka ya gurgunta sojojin Iran ya kasance ƙarin gishiri kuma sun tabbata a matsayin rashin gaskiya.
Isra'ila ta kasance cikakkiyar ƙawar Amurka a yaƙin. Amma an cire ta daga tattaunawar kan yarjejeniyar fahimtar juna kuma tana kallon yarjejeniyar da idon damuwa.
Netanyahu ya faɗa a ranar 28 ga watan Fabrairu cewa, ya jira duk rayuwarsa ta siyasa don samun damar ruguza Jamhuriyar Musulunci, wadda yake kallo a matsayin maƙiya mafi hatsari ga Isra'ila. Yanzu haka yana fuskantar hare-hare daga abokan hamayyar siyasa saboda yin barazana ga tsaron Isra'ila.
Netanyahu zai ci gaba da fuskantar sakamakon matakan da ya ɗauka har zuwa lokacin babban zaɓen da ke gabatowa cikin sauri, wanda za a yi kafin ƙarshen watan Oktoba.

Asalin hoton, Abbas FAKIH / AFP via Getty Images
Wani abin da zai kawo cikas shi ne matakin da Isra'ila ta bayyana na ci gaba da mamaye wani yanki mai faɗi a kudancin Lebanon, inda ta kori fararen hula daga ciki, ta kuma lalata dubban gine-gine. Ministan tsaron Isra'ila ya ce za ta ci gaba da mamayar da take yi a kasashen Lebanon, da Siriya da Gaza har abada.
Netanyahu na fuskantar matsin lamba daga masu tsatsauran ra'ayi a majalisar ministocinsa da kuma ƴan adawar siyasa da ya ƙaddamar da wani mummunan aikin soji a Lebanon. Wasu na kira da a mamaye yankin kudancin ƙasar. Dole ne ya yi la'akari da ko zai iya yin kasadar ƙara dagula ƙawancen Isra'ila da Amurka ta hanyar bijirewa Trump, wanda ke nuna bacin ransa da Netanyahu a wasu hirarraki da ya yi a Amurka.
Harin da Isra'ila ta kai a kudancin birnin Beirut a ranar Lahadin da ta gabata wani yunƙuri ne ƙarara na kawo cikas ga tattaunawar a wani muhimmin lokaci. A madadin haka sai ya zama kamar ya ƙara zafafa tattaunawar ne, domin lokacin magana ya na neman ya ƙure.
Yanzu dai lokaci ne da za a ɗan dakata a sarara. Ya yi sauri a iya tabbatar da cewa za a iya faɗaɗa yarjejeniyar fahimtar junar ta rikiɗe zuwa ta zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran. Yarjejeniya irin wannan na iya sauya yanayin Gabas ta Tsakiya. Amma aƙida da rashin amana gaba ɗaya sun sa ana ganin da kamar wuya a iya samun hakan.
Wannan lamari ne da bai yi wa duk waɗanda abin ya shafa daɗi ba. Al'ummar Iran, wanda Trump ya yi musu alƙawarin samun ƴanci a ranar 28 ga watan Fabrairu, har yanzu suna ƙarƙashin mulkin rashin tausayi wanda a watan Janairu ya kashe dubban ƴan ƙasar saboda zanga-zangar da suka yi a kan tituna.
Amurka na da ƙarfin tattalin arziki da na soja. Sai dai matakin da Trump ya ɗauka na fara yaƙi da Iran ya zama matakin da wata ƙasa mai ƙarfin fada-a-ji da ke fafutukar ganin ta ci gaba da riƙe madafun iko a duniyar da ke sauyawa cikin hanzari.










