Ƴan siyasar Najeriya da ke kan ƙadami tun daga 1999

- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja.
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Tun daga lokacin da Najeriya ta koma mulkin dimokuraɗiyya a ranar 29 ga Mayu wato a Jamhuriya ta Huɗu a 1999, akwai wasu ƴansiyasa da suke kan ƙadamin mulki har zuwa yanzu ba a daina yi da su ba.
Jamhuriya ta Huɗu ta ƙyanƙyashe ƴansiyasa da dama, wasu sabon yanka ne, wasu kuma jamhuriyar ta gaje su ne daga Jamhuriya ta Biyu da ta Uku.
Sai dai wasu sun yi fice na ɗan lokaci kafin su ɓace daga fagen siyasar. Yayin da wasu kuma suka kasance ana ci gaba da damawa a ɓangarori daban-daban na siyasa da mulki, kuma har yanzu ana damawa da su.
Sai dai yawanci sun kasance suna sauya jam'iyya ko ɓangare ko dai a siyasar ko a harkar mulki.
Yayin da ƙasar ke tunkarar wani sabon zaɓe, ga wasu daga cikin fitattun ƴan siyasar da suka kasance ana damawa da su tun daga 1999, kuma har yanzu ba su gajiya ba.
Bayan kusan shekaru 27 da fara Jamhuriya ta Huɗu, waɗannan mutane har yanzu suna daga cikin fitattun sunayen siyasar Najeriya. Wasu na mulki, wasu na adawa, wasu kuma suna taka rawa a bayan fage.
Bola Ahmed Tinubu
Duk da cewa ba a shekarar ya fara siyasa ba, amma lokacin da aka dawo da mulkin farar hula a 1999, Bola Ahmed Tinubu ya zama Gwamnan Jihar Legas, inda ya yi wa'adi biyu a shekara takwas a jere.
Bayan ya sauka daga mulki a 2007 ne ya jagoranci muhimmiyar rawa wajen kafa jam'iyyun AC da ACN daga baya.
Haka ya kasance jigo wajen kafa jam'iyyar haɗaka da APC a 2013, inda har ya zama jagoran jam'iyyar, har suka samu nasarar kayar da PDP a shekarar 2015.
Rawa da ya taka:
- Gwamnan Jihar Legas (1999–2007)
- Jagoran jam'iyyun adawa AC da ACN (2007–2015)
- Jagoran APC na ƙasa (2015–2023)
- Shugaban Najeriya (2023 zuwa yanzu)
Atiku Abubakar
Atiku Abubakar na daga cikin ƴan siyasar da suka fi daɗewa suna tashe a siyasar Najeriya.
Ya yi mataimakin shugaban ƙasa a gwamnatin Olusegun Obasanjo daga 1999 zuwa 2007. Tun bayan nan kuma ya ci gaba da kasancewa cikin manyan masu neman kujerar shugaban ƙasa.
Ko da yake bai sake riƙe wani babban muƙamin gwamnati ba tun daga lokacin, ya ci gaba da kasancewa cikin manyan ƴan adawa da masu tasiri a siyasar Najeriya.
Rawa da ya taka:
- Mataimakin Shugaban Ƙasa (1999–2007)
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na AC 2007 zuwa yanzu
Rabiu Musa Kwankwaso

Asalin hoton, Rabiu Musa Kwankwaso/FB
Rabiu Musa Kwankwaso yana cikin waɗanda suke da tafiyar siyasa mafi ƙwari, musamman a arewacin Najeriya.
Ya fara zama Gwamnan Kano a 1999, daga bisani ya zama Ministan Tsaro. Ya sake dawowa gwamna a 2011, sannan ya shiga Majalisar Dattawa kafin ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa.
Rawa da ya taka
- Gwamnan Kano (1999–2003)
- Ministan Tsaro (2003–2007)
- Gwamnan Kano (2011–2015)
- Sanatan Kano ta Tsakiya (2015–2019)
- Takarar shugaban ƙasa (2019 zuwa yanzu)
Rotimi Amaechi
Rotimi Amaechi ya fara fitowa fili ne a matsayin shugaban majalisar dokokin Jihar Rivers.
Daga bisani ya zama Gwamna, inda har ya riƙe shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya, sannan ya zama ministan sufuri.
Manyan muƙaman da ya riƙe:
- Shugaban majalisar dokokin Rivers (1999–2007)
- Gwamnan Rivers (2007–2015)
- Shugaban Ƙungiyar Gwamnoni (2011–2015)
- Ministan Sufuri (2015–2022)
Aliyu Magatakarda Wamakko
Aliyu Wamakko ya kasance cikin tasirin siyasar Sakkwato tsawon shekaru fiye da ashirin.
Ya fara ne a matsayin Mataimakin Gwamna kafin ya zama Gwamna sannan daga baya Sanata.
Har yanzu yana daga cikin manyan masu tasiri a siyasar Arewa maso Yamma.
Manyan muƙaman da ya riƙe:
- Mataimakin Gwamnan Sakkwato (1999–2006)
- Gwamnan Sakkwato (2007–2015)
- Sanatan Sakkwato ta Arewa (2015 zuwa yanzu)
Danjuma Goje
Danjuma Goje na cikin fitattun ƴansiyasar Najeriya daga arewacin ƙasar da suka daɗe suna tasiri.
Ya yi ƙaramin minista kafin ya zama Gwamnan Gombe. Tun bayan barin kujerar gwamna kuma yake riƙe da kujerar sanata.
Manyan muƙaman da ya riƙe:
- Ƙaramin ministan wutar ƙarafa (1999–2001)
- Gwamnan Gombe (2003–2011)
- Sanatan Gombe ta Tsakiya (2011 zuwa yanzu)
Aminu Waziri Tambuwal

Asalin hoton, Aminu Waziri Tambuwal/FB
Tambuwal na daga cikin ƴan siyasar da suka fara siyasa daga ƙaramin matsayi har suka tsallaka.
Ya fara ne daga hadimin Sanata Senator Abdullahi Wali , ya koma majalisar wakilai, inda har ya zama shugaban majalisar. Daga bisani ya zama Gwamnan Sakkwato sannan ya koma Majalisar Dattawa.
Manyan muƙaman da ya riƙe:
- Hadimin Senator Abdullahi Wali (1999 - 2000)
- Ɗan Majalisar Wakilai (2003–2015)
- Shugaban Majalisar Wakilai (2011–2015)
- Gwamnan Sakkwato (2015–2023)
- Sanata (2023 zuwa yanzu)
Orji Uzor Kalu
Orji Uzor Kalu ya shiga Jamhuriya ta Huɗu a matsayin Gwamnan Abia, wato a shekarar 1999.
Bayan ya sauka daga mulki, ya kafa jam'iyyar PPA kuma ya ci gaba da kasancewa cikin tasiri. Daga bisani ya shiga APC sannan ya zama sanata.
Manyan muƙaman da ya riƙe:
- Gwamnan Abia (1999–2007)
- Wanda ya kafa kuma jagoran PPA (2006–2015)
- Sanatan Abia ta Arewa (2019 zuwa yanzu)
Nyesom Wike

Asalin hoton, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS/FB
Wani ɗan siyasar Najeriya da za a iya cewa bai taɓa fita daga madafun iko ba tun 1999 shi ne Nyesom Wike.
Ya fara siyasa a matakin ƙaramar hukuma, daga nan ya shiga gwamnatin jiha, ya koma gwamnatin tarayya a matsayin minista, ya zama gwamna, sannan ya sake komawa gwamnatin tarayya a matsayin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT).
Manyan muƙaman da ya riƙe:
- Shugaban Ƙaramar Hukumar Obio/Akpor, Jihar Rivers (1999–2007)
- Shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Rivers (2007–2011)
- Ƙaramin Ministan Ilimi (2011–2013)
- Ministan Ilimi (2013–2014)
- Gwamnan Jihar Rivers (2015–2023)
- Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) (2023–zuwa yanzu)
Abdullahi Umar Ganduje
Shi ma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya shiga cikin wannan jerin.
Ganduje ya kasance yana riƙe da manyan muƙamai na siyasa da gwamnati na kusan tsawon shekara 25.
Rawar da ya taka:
- Mataimakin Gwamnan Jihar Kano (1999–2003)
- Mai ba ministan tsaro shawara kan harkokin siyasa (2003–2007)
- Shugaban hukumar tafkin Chadi (2007)
- Mataimakin Gwamnan Jihar Kano (2011–2015)
- Gwamnan Jihar Kano (2015–2023)
- Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa (Agusta 2023 – Yuni 2025)
- Shugaban Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) (2025 zuwa yanzu)










