KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a ranar Laraba 09/09/2026

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Adeyemi Adeniyi
  • Abdourahamane Tchiani
  • Atiku Abubakar
  • NFF
  • Badriyyah Tijjani Kalarawi
  • Ranar Hausa: BBC
  • Danjuma Goje
  • Zainab
  • BBC
  • ABU
  • xxx
  • xxx
  • Khalifa Dokaji
  • Sheikh Jingir

Rahoto kai-tsaye

Daga Muslim Muhammad Yusuf

  1. Batun addini ne ke taka rawa a shari'ar El-Rufai - NSCIA

    El-Rufai

    Asalin hoton, El-Rufai/X

    Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya, NSCIA, ta nuna damuwa kan abin da ta kira alamun nuna wariyar addini a shari'ar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

    A wata sanarwa da Sakataren Janar na majalisar, Farfesa Is-haq Oloyede, ya fitar, NSCIA ta ce ta daɗe tana ƙoƙarin ganin ta kaurace wa yin tsokaci kan shari'ar, saboda tun farko ta ɗauke ta a matsayin shari'a ta yau da kullum, tare da tunanin cewa kotuna za su iya tabbatar da adalci.

    Sai dai majalisar ta ce wasu abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, sun sa ta fara ganin akwai alamun wariyar addini ce ke taka rawa a shari'ar.

    Wannan ya biyo bayan kalaman Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, wanda ya zargi El-Rufai da shirya kashe-kashe a Kudancin Kaduna a lokacin da yake gwamna.

    NSCIA ta ce waɗannan kalamai sun sa ta sauya matsayinta na ƙin tsoma baki a batun, tana mai cewa akwai abubuwan da ke nuna yiwuwar wani "son zuciya na wariyar addini" a kan tsohon gwamnan.

    Majalisar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma ɓangaren shari'a da su tabbatar da cewa ba a yi amfani da hukumomin gwamnati ko tsarin shari'a wajen aiwatar da wata manufa ta bangaranci a kan El-Rufai ba.

    Ta kuma yi kira ga jama'a da su guji kalaman tunzura jama'a da ka iya yin tasiri kan shari'ar El-Rufai ko kuma ƙara dagula yanayin tsaro a Najeriya.

  2. Amurka ta mayar da martani kan iƙirarin Iran na kama jirgin ruwanta

    Jirgin ruwan Amurka da Iran ta ƙwace

    Asalin hoton, Getty Images

    Hedikwatar Rundunar Sojin Amurka da ke kula da yankin Gabas ta Tsakiya (CENTCOM) ta mayar wa BBC martani kan ikirarin da Iran ta yi na cewa ta kama wani jirgin ruwa ƙarƙashin teku maras matuƙi na Amurka a mashigin Hormuz.

    A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun CENTCOM, Laftanar Kyaftin Tim Hawkins, ya ce jirgin ruwan ƙarƙashin tekun ya lalace ne fiye da kwana ɗaya da ya gabata.

    Ya ce jirgin yana sintiri ne a ruwan yankin domin tallafa wa ayyukan da sojojin Amurka ke ci gaba da gudanarwa.

    Hawkins ya ƙara da cewa, "jirgin tsohon samfuri wanda ba ya tattara muhimman bayanan sirri, kuma ba ya ɗauke da na'urorin radar ko na'urorin gano bayanai masu sirri."

    Ya kuma ce ayyukan sojojin Amurka a ruwan yankin na ci gaba kamar yadda aka saba.

    A sa'o'in da suka gabata ne kamfanin dillancin labarai na Fars, mai alaƙa da rundunar juyin juya halin Iran, ya ba da rahoton cewa Iran ta "kama" wani jirgin ruwa ƙarƙashin teku mai fasahar zamani na Amurka.

    A cewar Fars, jirgin na daga cikin sababbin jiragen ruwa marasa matuƙi masu zamani da sojojin Amurka ke amfani da su.

    Kamfanin ya kuma ce an kama jirgin ne a bakin shiga mashigar Hormuz.

  3. Laraba ta Bawa!!!

    Barka da Safiya daga BBC.

    Asalin hoton, Getty Images

    Barka da Safiya daga BBC Hausa a wannan rana ta Laraba.

    Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

    Za ku iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin kallon wasu hotuna da bidiyon hirarraki da muke wallafawa tare da yin tsokaci a kai.