Dubban mutane sun yi zanga-zanga a Jamus kan nasarar jam’iyyar masu ra’ayin riƙau

Asalin hoton, Getty Images
Dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a ƙofar Brandenburg da ke birnin Berlin, domin nuna adawa da nasarar da jam’iyyar AfD mai ra’ayin riƙau ta samu a zaɓen jihar Saxony-Anhalt.
Masu zanga-zangar sun yi kira da a haramta jam’iyyar, wadda hukumomin leƙen asirin Jamus suka ayyana a matsayin mai tsattsauran ra'ayi.
Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, ya ce ya firgita da sakamakon zaɓen, inda AfD ta samu kusan kashi 44 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa a Saxony-Anhalt.
Wakiliyar BBC ta ce abin da ake gani shi ne yadda mutane da dama suka gaji da jam’iyyun gargajiya da suka saba bai wa ra'ayinsu.
Jam’iyyar AfD ta ce za ta nemi goyon bayan sauran jam’iyyu ko kuma wasu daga cikin ƴan majalisar jihar domin samun damar kafa gwamnati a Saxony-Anhalt.


















