Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 14/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Lahadi, 14 ga watan Yuni, 2026.

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Kutama
  • xxx
  • XXX
  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Aisha Babangida da Isiyaku Muhammed

  1. Dole ne kowa ya bi umarnin jagoran addininmu kan tattaunawa da Amurka - Iran

    .....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya jaddada cewa dole dukkan masu ruwa da tsaki su bi duk wata shawara da jagoran addinin ƙasar ya amince da ita wajen tattaunawa da Amurka, yana mai cewa wannan shi ne ginshiƙin yanke hukunci.

    Ya bayyana cewa amincewar Majalisar Tsaron Ƙasa ita ce mafi aminci kuma duk abin da jagoran juyin juya hali ya sahale zshine ai zama wajibi ga kowa ya bi, ko da kuwa ra’ayinsa ya bambanta da na jagoranci.

    A gefe guda kuma, kwamandan rundunar sararin samaniyar juyin juya halin Iran, Majid Mousavi, ya yi kira ga al’umma da su tsaya tsayin daka tare da goyon bayan jagororin ƙasa, ba tare da ja da baya ko ƙarin gaba ba.

    Rahotanni sun kuma nuna cewa wasu ‘yan ra’ayin tsattsauran ra’ayi sun gudanar da zanga-zanga a Tehran, inda suka rika sukar manyan masu tattaunawa da Amurka, yayin da ake fargabar yarjejeniyar da ake shirin kulla tsakanin Iran da Amurka.

  2. Sojojin Najeriya sun fatattaki masu fasa bututun mai a jihar Rivers

    ....

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Rundunar Sojin Ruwan Najeriya ta ce ta fatattaki masu satar mai da fasa bututu da ke ƙoƙarin sake kafa matatun mai ba bisa ƙa’ida ba a Jihar Rivers, a wani farmaki da aka kai ƙarƙashin shirin Operation DELTA SENTINEL.

    A cikin wata sanarwa, rundunar ta bayyana cewa jami’anta na sun kai farmakin ne bayan samun sahihan bayanan sirri a yankin Oseokishikpa da ke ƙaramar hukumar Ogba-Egbema-Ndoni, inda suka gano wuraren matatun mai ba bisa ka'ida ba guda biyu.

    An ce a yayin farmakin, an gano rijiyoyi da tankunan adana mai guda takwas da ke ɗauke da kimanin lita 15,000 na danyen mai da kuma lita 105,000 na man dizal da ake zargin an sarrafa ba bisa ka’ida ba.

    Rundunar ta ce wannan nasara ta hana ‘yan ta’adda sake farfaɗo da harkokinsu da kuma lalata muhalli a yankin.

    Rundunar ta ƙara da cewa an bi ƙa’idojin da suka dace wajen gudanar da wannan aikin da kuma kayan da aka kwace tare da hana masu laifi ci gaba da amfani da su.

    Ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da kai hare-haren bayanan sirri domin rusa hanyoyin satar mai da kare tattalin arzikin ƙasa a yankin Neja Delta. make that first paragraph tally with the headline Sojojin Najeriya sun fatattaki masu fasa bututun mai a jihar Rivers

    .....

    Asalin hoton, Nigerian Army

  3. Za mu mayar da martani kan harin Isra’ila a Lebanon - Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta yi gargadin cewa za ta mayar da martani kan harin da Isra’ila ta kai a kudancin Beirut, yayin da Amurka ta bukaci a dakatar da hare-hare domin bai wa tattaunawar zaman lafiya dama.

    Shugaban Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, Mohammad Baqer Zolqadr, ya bayyana cewa ƙasar ba za ta lamunci karya layukanta ba, yana mai cewa martanin mayaƙan Iran na nan tafe.

    Ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan harin da Isra’ila ta kai harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku da kuma jikkata wasu shida, a cewar hukumomin kare fararen hula na Lebanon.

    Shi ma shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya zargi Amurka da goyon bayan hare-haren Isra’ila, yana mai cewa hakan na nuna Amurka ba ta da niyya ko ƙarfin cika alƙawurranta.

    Sai dai shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira da a dakatar da duk wani hari, yana mai cewa bai kamata Isra;ila ta kai wa Beirut hari ba, musamman a lokacin da ake daf da cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Iran, inda ya yi kira ga ɓangarorin da su nuna haƙuri domin kada a rasa wannan dama.

  4. 'Yanbindiga da masu ɗaukar nauyinsu su miƙa wuya ko su fuskanci ƙarfin gwamnati – Tinubu

    .....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya jaddada cewa “‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da masu ɗaukar nauyin ta’addanci su miƙa wuya ko kuma su fuskanci cikakken ƙarfin gwamnatin Najeriya,” yayin da yake mayar da martani kan matsalar tsaro da kuma rasuwar tsohon Manjo Janar Rabe Abubakar.

    A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, shugaban ya ce gwamnati ba za ta taɓa amincewa da buƙatun ‘yan ta’adda na sakin wasu daga cikinsu da ke hannun jami’an tsaro ba.

    Ya kuma yi gargadi cewa wannan damar da ake bai wa masu aikata laifuffuka ta miƙa wuya ba za ta daɗe ba, yana mai cewa ba za a nuna jinƙai ga waɗanda ke zubar da jinin ‘yan Najeriya ba.

    Tinubu ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kasance cikin haɗin kai da juna domin yaƙar ta’addanci, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar.

  5. Ya kamata Isra’ila ta daina kai hare-hare a Lebanon - Trump

    .....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira da a dakatar da duk wani hari da ake kai wa Lebanon da Isra’ila, yana mai cewa lokaci ya yi da za a nuna hakuri domin kauce wa rikici.

    Trump ya bayyana hakan ne a shafinsa na Truth Social, awa guda bayan harin da Isra’ila ta kai yankin Dahiyeh a Beirut, inda ya ce harin bai kamata ya faru ba, musamman a lokacin da ake kusantar cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Iran.

    Ya jaddada bukatar a nuna takatsantsan daga bangarorin biyu, yana mai cewa bai kamata Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a Lebanon ba, kamar yadda bai kamata Hezbollah ko wasu ƙungiyoyi su kai hare-hare kan Isra’ila ba.

    Sai dai bayan wannan hari, Iran ta yi barazanar dakatar da tattaunawa da Amurka, yayin da mataimakin shugaban rundunar Khatam al-Anbiya ya ce harin ba zai tafi a haka ba tare da daukar mataki ba.

  6. Babu wata yarjejeniya da za a ƙulla a lokacin da Trump ya ayyana - Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata majiya kusa da tawagar tattaunawar Iran ta bayyana cewa babu wata yarjejeniya da za a ƙulla a lokacin da shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar.

    A cewar kamfanin dillancin labarai na Fars, majiyar ta ce duk da cewa Trump ya bayyana cewa za a rattaba hannu kan yarjejeniya nan take tare da buɗe mashigar Hormuz ga dukkan jiragen ruwa, har yanzu ba a kammala tattaunawar ba.

    Rahotanni sun kuma nuna cewa, sa’o’i kaɗan kafin harin da Isra’ila ta kai a kudancin Beirut, wata tawagar Qatar tana Tehran domin isar da buƙatun Iran zuwa ɓangaren Amurka, ciki har da cikakkun sharuddan da Tehran ke son a saka a cikin yarjejeniyar.

    Majiyar ta jaddada cewa ko da tattaunawar ta ci gaba da tafiya gaba da baya, babbar buƙatar Iran ita ce a yi la’akari da dukkan damuwarta gaba ɗaya, tana mai cewa ko da an amince da sharadanta, hakan ba yana nufin za a rattaba hannu kan yarjejeniya a lokacin da Trump ya ayyana ba.

  7. Ko kankana na iya maye gurbin maganin karfin maza?

    Kankana

    Asalin hoton, Getty Images

    Kankana tana da matuƙar amfani kuma tana da fa'idodi da yawa ga lafiyar jiki.

    Masu bincike a Amurka sun kwatanta aikin kankana a jikin mutum da irin wanda maganin karfin maza ke yi.

    Kankana tana ɗauke da sinadarin citrulline, wani sinadari mai kama da wanda ke cikin maganin karfin maza da ake kira Viagra.

  8. Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe ‘yan ta’adda 27

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar Sojojin Najeriya ta sanar da cewa sojojinta sun samu gagarumar nasara a hare-haren da suka kai a sassa daban-daban na ƙasar, inda suka kashe ‘yan ta’adda 27 tare da kama mutum 10 da ake zargi da aikata laifuka.

    Rundunar ta kuma bayyana cewa sojojinta sun ceto mutane 8 da aka yi garkuwa da su cikin awanni 48 kacal da suka gabata.

    A cewar sanarwar da rundunar ta fitar, hare-haren sun gudana ne tare da haɗin gwiwar sojojin ƙasa da na sama a jihohin Borno da Plateau da Nasarawa da Akwa Ibom, da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT), bisa ingantattun bayanan sirri da suka samu.

    Hakan ya taimaka wajen dagula ayyukan ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a waɗannan yankuna.

    Rundunar ta jaddada ƙudurin ci gaba da kai hare-hare, tare da roƙon jama’a su ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasa.

  9. Za mu iya daina tattaunawa da Amurka saboda rashin cika alkwari - Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya bayyana cewa ba zai yiwu a ci gaba da tafiyar da tattaunawa da Amurka ba idan har ba ta da niyya ko ƙwarewar cika alƙawurranta ba.

    Qalibaf ya faɗi hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X bayan harin da Isra’ila ta kai unguwar Dahiyeh a Beirut, wadda ake ɗauka a matsayin cibiyar ƙarfi ta Hezbollah.

    Ya zargi Amurka da bayar da dama ga Isra’ila wajen kai hare-haren.

    Ya ƙara da cewa ba za a iya samun wata nasara ba idan aka ci gaba da ba da goyon baya ga irin waɗannan hare-hare.

    A wani saƙo daban, Qalibaf ya ce Isra’ila ba ta mutunta tsagaita wuta ko yarjejeniyoyi ba, yana mai nuni da keta yarjejeniyar da ta shafi Lebanon, tare da jaddada cewa suna fahimtar amfani da ƙarfi ne kawai.

  10. An kama tsohon shugaban ƴansandan Bangladesh bisa zarginsa da almundahana

    Bangladesh

    Asalin hoton, Getty Images

    Bangladesh ta ce jami'anta sun samu nasarar kama tsohon shugaban ƴansandan ƙasar a Dubai bisa zarginsa da almundahana bayan daɗewa ana nemansa.

    Ministan harkokin ciki gidan ƙasar Salahuddin Ahmed ne ya bayyana hakan, inda ya ce sun kama tsohon shugaban ƴansandan mai suna Benazir Ahmed ne tare da haɗin gwiwar ƴansanda na ƙasa da ƙasa, sannan ya ƙara da cewa tuni sun fara shirye-shiryen mayar da shi ƙasar.

    Mista Ahmed ya riƙe shugaban ƴansandan ƙasar a zamanin mulkin Firaminista Sheikh Hasina, wadda aka hamɓarar a zanga-zangar ƙasar ta Agustan 2024.

    Hukumar yaƙi da cin hanci ta ƙasar ta zarge shi da tara arzikin da a cewarta ta hanyoyin da ba su dace ba ne.

  11. Mutuwar Janar Rabe za ta ƙarfafa mana gwiwa cewa babu sulhu da ‘yanbindiga kuma maƙiyanmu ne – Tinubu

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana matuƙar kaduwarsa bisa rasuwar tsohon Manjo Janar Rabe Abubakar wanda ya rasu a hannun ‘yan ta’adda a Jihar Katsina ranar Asabar

    A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, shugaban ya bayyana cewa marigayin ya yi dogon lokaci yana yi wa ƙasa hidima cikin aminci da ƙwarewa kafin ya yi ritaya shekaru da suka gabata.

    Shugaban ya kuma ce mutuwar Janar Rabe za ta ƙarfafa gwiwar gwamnati wajen tabbatar da cewa babu wata sulhu da ‘yan bindiga, yana mai cewa dole ne a ɗauke su a matsayin maƙiyan ƙasa.

    Shugaban ƙasar ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, musamman matarsa, da gwamnatin Jihar Katsina, da rundunar sojojin Najeriya baki ɗaya.

    Ya nanata cewa wannan lamari ya zama babban darasi a yaƙin da ake yi da ‘yan ta’adda, inda ya ce babu wani sassauci ko sulhu da za a yi da su, tare da ƙarfafa ƙudurin gwamnati na murƙushe duk wani nau’i na ta’addanci a ƙasar.

  12. 'Yarjejeniyar Iran da Amurka ita ce mafi girman gazawar tsaro da harkokin wajen Isra’ila'

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon firaministan Isra’ila kuma jagoran ‘yan adawa, Yair Lapid, ya soki firaminista Benjamin Netanyahu kan yarjejeniyar da ake zargin an kulla tsakanin Iran da Amurka, yana mai kiran ta babbar gazawar tsaro da harkokin wajen Isra’ila'

    Lapid ya ce Netanyahu ya gaza shawo kan Amurka kan mahimman batutuwa kamar lalata cibiyoyin mai na Iran da kuma saka batun makamai masu linzami a cikin tattaunawa.

    Ya kuma zarge shi da yin kuskure a lissafin tasirin Turkiyya da kuma rashin kula da muhimmancin zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.

  13. Isra'ila ta kai hari a Lebanon ana tsaka da tsammanin yarjejeniya tsakanin Iran da Amurka

    Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    A wani yanayi da ka iya kawo tsaiko a yunƙurin tabbatar da yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran, Isra'ila ta ƙaddamar da hari a wani gari da ta yi maɓoyar mayaƙan Hezbollah a kudancin birnin Beirut.

    Wani faifan bidiyo ya nuna yadda hayaƙi ya turnuƙe a yankin da ake kai harin.

    Ita dai Isra'ila ta ce ta yi harin ne a matsayin martani kan harin da te ce mayaƙan Hezbollah sun kai yankunanta.

    Tun da farko, rundunar sojin Isra'ila ya ƙara yaɗa saƙonnin gargaɗi tare da kira ga mutane su fice daga yankunan aƙalla ƙauyuka 9 a kudancin Lebanon kafin fara hare-hare.

    Iran dai ta nanata cewa dole a saka Lebanon a cikin duk maganar da za a yi ta shiga ko tsara yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da ake yi.

  14. 'Har yanzu matar Janar Rabe na hannun masu garkuwa'

    Rabe

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Yarinyar marigayi Janar Abubakar Rabe, wanda ya rasu a hannun ƴanbindiga ta ce suna cikin tashin hankali mara misaltuwa na abin da ya faru da iyayensu.

    Bilkisu Rabe Abubakar ta bayyana cewa an jana'izar mafhaifinsu a jiya Asabar da misalin ƙarfe 6:15 na yamma bayan an yi masa Sallah a Masallacin GRA da ke Katsina.

    Sai dai ta ce har yanzu mahaifiyarsu wadda aka sace tare da mahaifinsu har yanzu tana hannun masu garkuwar, har zuwa lokacin haɗa wannan labarin.

    Hukumomi dai sun lashi takobin tabbatar da cewa sun ceto ta.

    An yi garkuwa da Manjo Janar Rabe Abubakar da matarsa a Jihar Katsina a watan da ya gabata, bayan da 'yan bindiga suka kai hari kan motarsu.

    Kwanaki kadan kafin mutuwarsa, an ga bullar wani bidiyonsa a daji da ke nuna shi da wani ciwo a kafarsa ta hagu, to sai dai mahukunta a jihar Katsinan sun ce ya rasu a hannun 'yan fashin dajin ne sakamakon fama da ciwon suga da hawan jini.

    A cikin shekarun baya-bayan nan, wasu manyan jami’an soja sun rasa rayukansu sakamakon masu garkuwa da mutanen.

  15. Ƴanbindiga sun yi garkuwa da jami'in ma'aikatar tsaron Haiti

    Haiti

    Asalin hoton, EPA

    Rahotanni daga ƙasar Haiti na cewa wasu mutane masu ɗauke da makamai sun yi garkuwa da babban jami'in ma'aikatar ministan tsaron ƙasar a babban birnin ƙasar, Port-au-Prince.

    James Boyard, wanda fitaccen masanin harkokin tsaro ne, kuma babban sifeton 'yan sanda na ƙasar, ana kyautata zaton shi ne jami'i mafi girma da aka yi garkuwa da shi a Haiti cikin 'yan shekarun nan.

    Wasu mutane biyu da suka san yadda lamarin ya faru sun tabbatar wa jaridar The New York Times da batun sace shi. Kafofin watsa labarai na cikin gida sun ruwaito cewa an yi garkuwa da Boyard ne a yankin Bourdon, ɗaya daga cikin wuraren da ake ganin har yanzu suna da ɗan tsaro a babban birnin kasar.

    Ƙasar Haiti, wadda ita ce ƙasa mafi yawan al'umma a yankin Karebiyan, ta shafe shekaru tana fama da tashe-tashen hankula da ayyukan ƙungiyoyin masu laifi. Rikicin ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba sama da mutum miliyan ɗaya da muhallansu.

  16. Ana kaɗa ƙuri'ar ƙayyade yawan al'ummar Switzerland

    Zabe

    Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images

    Masu kaɗa ƙuri'a a ƙasar Switzerland na yanke hukunci a yau kan wata shawara da ke neman kayyade yawan al'ummar ƙasar zuwa miliyan goma.

    Fiye da kashi ɗaya cikin huɗu na mutanen ƙasar miliyan 9.1 ba 'yan ƙasa ba ne, kuma wannan shiri ya fito ne daga jam'iyyar masu ra'ayin riƙau ta Swiss People's Party.

    Jam'iyyar ta ce idan masu kaɗa ƙuri'a suka amince da shawarar, hakan zai rage matsin lamba kan gidaje, da ayyukan gwamnati da kuma muhalli.

    Sai dai gwamnati da shugabannin harkokin kasuwanci da kuma sauran manyan jam'iyyun siyasar ƙasar na adawa da wannan mataki, suna masu cewa hakan zai hana Switzerland samun ma'aikatan da take matuƙar buƙata, tare da kawo cikas ga yarjejeniyoyin da aka daɗe ana kullawa da tarayyar Turai.

    Babu wata ƙasa da ta taɓa yunƙurin sanya iyaka kai tsaye ga yawan al'ummarta a baya, kuma ana sa ran duniya za ta zura ido sosai kan sakamakon ƙuri'ar da za a yi a Switzerland.

  17. China ta nuna fushinta bayan Amurka ta zargi wasu kamfanonin ƙasar ''da tallafa wa soji''

    China

    Asalin hoton, Reuters

    Mahukuntan a China sun nuna fushinsu, bayan wata sanarwar da Washington ta fitar a farkon makon nan cewa ta ƙara wasu kamfanonin kasar cikin jerin kamfanonin da Ma'aikatar Tsaron Amurka (Pentagon) ke zargi da tallafa wa rundunar sojin China.

    Ma'aikatar Kasuwancin kasar ta ce a ranar Asabar ba ta gamsu ko kaɗan da wannan mataki ba, wanda ya sa aka saka kamfanoni irin su kamfanin kera motoci na BYD da kuma katafaren kamfanin kasuwancin intanet na Alibaba cikin wannan jeri.

    Ma'aikatar ta kuma yi gargaɗin cewa idan har Amurka ba ta yi mi'ara koma baya ba, Beijing za ta ɗauki matakan ramuwar gayya.

  18. Manyan hafsoshin sojin Najeriya da matsalar tsaro ta rutsa da su

    Tsaro

    Asalin hoton, AFP via Getty/Tsiga/Getty/BBC Collage

    A Najeriya, sacewa da mutuwar tsohon mai magana da yawun rundunar tsaron ƙasar, Manjo Janar Abubakar Rabe su haifar da muhawara, musamman a kafofin sadarwa, inda wasu ke fargabar lamarin na ta'azzara.

    A ranar Asabar, 13 ga Yunin shekarar 2026 ne gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da cewa tsohon hafsan tsaron ya rasu bayan kwanaki a hannun waɗanda suka yi garkuwa da shi.

    Yadda ƴanbindiga suka riƙa fitar da bidiyon janar ɗin tare da matarsa ya ja hankali matuƙa, inda ake ganin matsayinsa ya wuce haka, har wasu ke cewa alamu na nuna cewa kowa zai iya shiga matsalar.

  19. Yau za mu saka hannu a yarjejeniya da Iran - Amurka

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi iƙirarin cewa za a rattaba hannu kan yarjejeniya da Iran wadda za ta hana ƙasar samar da makamin nukiliya, tare da tabbatar da sake buɗe mashigar Hormuz a yau Lahadi.

    Sai dai wannan saƙo da shugaban ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ya zo ne bayan kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya nuna har yanzu babu lokacin sanya hannu kan yarjejeniyar.

    Wakilin BBC ya ce Iran ta fi nuna taka-tsantsan kan lokacin sanya hannun, watakila saboda har yanzu ba su daddale komai game da batun ba.

    Jiya Asabar ita ma Pakistan, wadda ke taka muhimmiyar rawa wajen sasanta ɓangarorin, ta ce ana sa ran kammala yarjejeniyar cikin sa'o'i 24 masu zuwa, tare da bayyana cewa ana shirye-shiryen sanya hannu ta Internet.

  20. Buɗewa

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa barkanmu da ganin safiyar yau Asabar.

    Aisha Babangida ce ke fatan kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na Facebook da X da kuma Whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.