Ko haɗakar Obi da Kwankwaso za ta iya kai su ga mulkin Najeriya?

Obi and Kwankwaso

Asalin hoton, Peter Obi/FACEBOOK

Bayanan hoto, Peter Obi da Kwankwaso bayan tabbatar masa da takara a jam'iyyar NDC
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Gawurtaccen ɗan siyasar Igbo da ke son kafa babban tarihin zama shugaban ƙasa, daga yankin da wasu ke gani yana da nuna ɗari-ɗari ga mutanen da suka fito daga wani sashe, addini da kuma fahimtar rayuwa daban, hamshaƙin ɗan kasuwa maras facaka, Peter Obi yana taƙama da zunzurutun matasa masu ra'ayin kawo sauyi a Najeriya.

A ƙasar da ko yaushe take neman wani zaƙaƙuri, da zai iya tsamo ta daga ɗumbin matsalolin da suka yi mata zargagungum, matasa masu goyon bayansa a shafukan sada zumunta na ɗaukaka Obi zuwa wani matsayi da ke nuna 'babu kamarsa'.

Da tutar jam'iyyar NDC yanzu a hannunsa, ga ƙawancen Kwankwasiyya, Obi na da kyakkyawan fatan shiga takara cikin gagga-gaggan 'yan siyasa kamarsu Atiku Abubakar da ke neman hamɓare Shugaba Tinubu daga kan mulki a zaɓen 2027.

A 2023, ya sha kaye a hannun Tinubu, inda ya zo na uku a bayan Atiku.

Wasu masu adawa da shi na cewa mai yiwuwa ne ya fi wasu 'yan takarar nagarta, amma shahararsa ba ta karaɗe faɗin ƙasar ta yadda har zai iya cin zaɓe ba.

Yayin da Najeriya ke tunkarar wani sabon zaɓen, Obi ya shiga ADC da farko tare da wasu manyan 'yan adawa kamar tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar da kuma wasu da suka ɓalle daga jam'iyyar APC mai mulki, amma tafiyar ba ta yi tsawo ba.

Obi da Kwankwaso, dukkansu tsoffin gwamnoni ne kuma suna da gagarumin faɗa-a-ji a tsakanin al'umma na ƙasa-ƙasa a yankunan da suka fito - abin da ya ba su damar kafa tafiyar haɗaka mai taken Obi-Kwankwaso (OK).

Obi

Asalin hoton, Peter Obi/FACEBOOK

Bayanan hoto, Peter Obi ya yi takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Labour a 2023

Duk da taƙaddama kan dukiyarsa, mulkinsa a matsayin gwamnan jihar Anambra ya zama babban abin misali wajen yaƙin neman zaɓensa tun a zaɓen 2023.

Magoya bayansa na kirarin cewa wanne ɗan siyasar Najeriya ne, da ya taɓa riƙe muƙami kuma ya sauka da cikakkiyar ƙimarsa.

Suna nuni da cewa ya zuba maƙudan kuɗi a fannin bunƙasa ilmi kuma ya riƙa biyan albashi a kan lokaci - waɗansu ƙananan abubuwa da gwamnonin jihohi da yawa a Najeriya kan yi biris da su.

Ya kuma bar ɗumbin kuɗi a baitulmalin jihar a ƙarshen mulkinsa na tsawon wa'adi biyu, wani abu da shi ma ba a saba gani ba.

A bai wa matasa ƙarin damammaki - Obi

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Peter Obi wanda a bana ya cika shekara 64 da haihuwa, ya yi takara a zaɓen 2023 a ƙarƙashin jam'iyyar Labour.

Tsohon gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabas, wannan ne karo na uku da yake takara. Karon farko ya yi wa Atiku Abubakar mataimaki a 2019 ƙarkashin jam'iyyar PDP.

Ya yi digiri a fannin falsafa kuma ya yi aiki a kantin gidansu kafin ya je ya fara kasuwancin ƙashin kansa, ta hanyar shigo da kayayyaki daga waje kama daga man salak zuwa mayukan kyawun fata da waken gwangwani da barasa.

Peter Obi ya kuma mallaki wani kamfanin sarrafa barasa kuma ya mallaki hannayen jari a wasu bankunan kasuwanci guda uku.

Ɗan siyasar, ba mutum ne mai fankama da fantamawa ba.

Ya taɓa nuni da cewa takalmansa guda biyu ne kacal kuma ya fi son sanya kwat ɗin Stein Mart wadda ba ta fi $200 ba zuwa nau'in Tom Ford ta $4,000. Mutum ne da kan dage cewa ya fi son ɗaukar jakunkunansa a lokacin tafiya, maimakon dogaro ga 'yan baranda su ɗaukar masa.

Hatta 'ya'yansa sun san Peter Obi wajen tsantseninsa.

Ya ce ya taɓa hana ɗansa mai shekara 33 mallakar mota, kuma akwai wani ɗansa da ya yi koyarwa a matsayin malamin firamare kuma cikin farin ciki - wannan ma wani abu ne da ba a cika gani ba a ƙasar da 'ya'yan manyan 'yan siyasa ke kallon irin wannan aiki a matsayin ƙasƙanci.

Yayin wani jawabi bayan tabbatar da takarar shugaban ƙasa a NDC, Peter Obi ya yi kiran a samu haɗin kan ƙasa kuma a ba da ƙarin damammaki ga matasa.

Takararsa da Kwankwaso dai ta sanya wasu da yawa na ganin za su ƙare ne kawai wajen tarwatsa ƙuri'un 'yan adawa - saɓanin dunƙulewa wuri ɗaya kamar yadda jam'iyyarsu ta baya wato ADC ta so - abin da kuma a ƙarshe zai iya sake bai wa APC nasara.

Sai dai masharhanta kamar Bala Yusuf sun faɗa wa BBC cewa takarar Obi a matsayin mai neman kujerar shugaban ƙasa da Kwankwaso a matsayin mataimaki tabbas wata babbar barazana ce ga jam'iyyar APC mai mulki.

Yayin da wasu ke cewa matuƙar Obi da Kwankwaso za su iya tsare tungogin da suka fi ƙarfi a siyasance, mai yiwuwa ne su iya haddasa wani gagarumin sauyi.

Burin haɓaka karɓuwa a Arewa

A matsayinsa na jajirtaccen ɗan ɗariƙar katolika daga Kudu maso gabashin Najeriya, Peter Obi na fatan janyo ra'ayin ƙarin ɗumbin masu zaɓe a yankin arewa, mai rinjayen Musulmai. Ana kallon ƙuri'un yankin a matsayin masu matuƙar muhimmanci ga duk ɗan takarar shugaban ƙasar da zai ci zaɓe.

Ko da yake ya sha wofantar da masu sukar sa saboda addininsa, Peter Obi ya yi suna wajen halartar tarukan cocin Pentecostal cike da ɗumbin mabiya, sannan ya riƙa kai ziyara lokacin yaƙin neman zaɓen 2023 garuruwan da Kiristoci suka fi rinjaye a arewa.

Hakan ya janyo masa suka daga masu adawa da shi waɗanda suka riƙa sukar shi da cewa shi mutum ne maras jure zama da mutanen da suka sha bamban a addinance da ƙoƙarin haifar da ɓaraka ta hanyar nuna bambancin addini, zarge-zargen da ya sha musantawa.

Ɗauko Rabi'u Kwankwaso a matsayin mataimakin takararsa daga Kano, mai yiwuwa wani babban lissafi ne da zai iya canza wancan tunani, kuma ga alama zai iya ba shi damar samun ƙarin karɓuwa ba kawai a tsakanin mabiyan Kwankwasiyya ba.

Haka zalika, masu sukarsa na tababa a kan ko da gaske Peter Obi ya yi hannun riga daga al'adar cin hanci da rashawan da yake yawan yi wa tofin ala-tsine, inda suke nuni da bayyanar sunansa cikin Takardun Pandora a 2021 waɗanda suka taɓa fallasa masu kuɗi da ƙarfin ikon da suka mallaki arziƙi a asirce

Ko da yake ba a taɓa zarginsa da satar kuɗi ba, amma ya gaza bayyana dukiya da asusun bankunan ƙetare da ke riƙe a hannun iyalansa, inda ya dage kan cewa ba shi da masaniya.

An kuma taɓa zarginsa da zuba kuɗi gwamnatin jihar Anambra cikin wani kamfani da ya yi hulɗa da shi. Amma ya ce bai aikata wani abu na ba daidai ba, ya ma yi nuni da cewa darajar jarin da ya zuba tuni ta haɓaka.

Daga shekara ta 2002, Peter Obi ya sauya jam'iyyun siyasa daga PDP zuwa LP, daga LP zuwa ADC, daga ADC zuwa NDC a yanzu.