Madrid za ta saurari tayin Utd kan Tchouaméni, Arsenal na neman Stones

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid a shirye take ta saurari tayin sayen ɗan wasan tsakiya na Faransa, Aurélien Tchouaméni, mai shekara 26, daga Manchester United. (The Sun)
Manchester United na kuma duba yiwuwar sayen ɗan wasan tsakiya na AS Roma kuma ɗan ƙasar Faransa, Manu Koné mai shekara 25, da kuma ɗan wasan Brighton kuma ɗan ƙasar Kamaru, Carlos Baleba mai shekara 22, domin ƙarfafa tsakiyarta. (Sky Sports)
Haka kuma, ɗan wasan tsakiya na Bournemouth ɗan Amurka, Tyler Adams mai shekara 27, wanda ake hasashen darajarsa ta kai fam miliyan 35, na cikin wadanda Manchester United ke nazari a kansu. (Daily Mail)
Arsenal na zawarcin 'yan wasan bayan Ingila biyu, John Stones mai shekara 32 da kuma Ezri Konsa mai shekara 28, bayan raunin da ɗan bayanta na Faransa William Saliba mai shekara 25 ya ji. Stones ya taɓa taka leda a Manchester City, yayin da Konsa ke buga wa Aston Villa wasa. (Sky Sports)
Chelsea ce ke kan gaba wajen ɗaukar matashin ɗan wasan Bosnia-Herzegovina, Kerim Alajbegovic mai shekara 18, daga Bayer Leverkusen. A lokaci guda kuma, ƙungiyar ta Jamus na tattaunawa da Crystal Palace kan sayar da ɗan bayan Faransa Axel Disasi mai shekara 28. (Telegraph)
Chelsea ta kuma cimma yarjejeniya da matashin ɗan wasan gefe na Amurka, Benji Flowers mai shekara 15, daga ƙungiyar FC Dallas. Sai dai zai koma Stamford Bridge ne idan ya cika shekara 18. (The Athletic)
Arsenal da Manchester City na cikin jerin ƙungiyoyin da ke fafatawa domin ɗaukar ɗan wasan gefe na Ivory Coast, Yan Diomande, daga RB Leipzig. A baya ƙungiyar ta Jamus ta yi watsi da tayin fam miliyan 69 da Liverpool ta gabatar mata kan ɗan wasan mai shekara 19. (Bild)
Liverpool na shirin tura ɗan bayanta na tawagar Ingila ta 'yan ƙasa da shekara 20, Amara Nallo mai shekara 19, zuwa ƙungiyar Finland ta HJK Helsinki aro na tsawon kakar wasa guda. (The Athletic)
Ɗan wasan gaba na Japan kuma tauraron Celtic, Daizen Maeda mai shekara 28, zai yi gwajin lafiya a ranar Juma'a domin kammala komawarsa Ipswich Town kan kuɗi fam miliyan 10. (Sky Sports)
Ɗan wasan gefe na Ingila, Jack Harrison mai shekara 29, yana dab da barin Leeds United zuwa ƙungiyar MLS ta Amurka, New England Revolution. (The Athletic)
Everton na zawarcin ɗan bayan dama na Celtic, Alistair Johnston mai shekara 27. Dan ƙasar Kanada ya burge a gasar Kofin Duniya, kuma ana kallonsa a matsayin wanda zai dace ya maye gurbin Seamus Coleman bayan ficewarsa daga Goodison Park. (Daily Record)
Aston Villa na sha'awar ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Everton kuma ɗan Ingila, James Garner mai shekara 25, a wannan bazarar. (Football Insider)















