'Muna zargin kashe shi aka yi' - iyalan Abubakar Lawal ɗan wasan Najeriya da ya mutu a Uganda

Asalin hoton, @VipersSC
Dangin ɗan wasan ƙwallon ƙafa ɗan Najeriya, Abubakar Lawal, wanda ya rasu a Uganda a shekarar da ta gabata, sun bayyana damuwarsu da ƙorafi kan rashin samun rahoton binciken abin da ya yi sanadin mutawarsa duk da shafe fiye da shekara guda da aukuwar lamarin.
Sun kuma yi korafin cewa har yanzu kulob ɗin da yake bugawa wasa a Uganda, Vipers SC, bai cika alkawarin biyan wasu haƙƙoƙinsa da suka yi wa iyalinsa ba.
A lokacin rasuwar tasa, 'yan sandan Uganda sun bayyana cewa Lawal ya mutu ne sakamakon fadowa daga saman wani bene.
Sai dai iyalansa sun ce har yanzu ba su gamsu da wannan bayani ba.
Ƙorafin iyalan Lawal
Da yake magana da BBC, ƙanin marigayin, Mansur Lawal, ya ce babban abin da iyalan ke nema shi ne a fito musu da sakamakon binciken hukuma.
"Abin da muke so yanzu shi ne a ba mu rahoton abin da ya faru da shi. Yau shekara ɗaya da wata uku kenan amma babu wani bayani na hukuma da aka ba mu," in ji shi.
Ya ce sun yi ƙoƙarin tuntuɓar jami'an Najeriya a Uganda domin neman bayani, amma har yanzu ba su samu wani ci gaba ba.
Mansur ya ce ko jakadan Najeriya da suka riƙa tuntuɓa a baya bai samu rahoto daga hukumomin Uganda ba kafin ya bar ƙasar.
"A duk lokacin da muka yi magana da shi, yana gaya mana cewa ana ci gaba da bincike. Har ya taɓa zuwa ofishin 'yan sanda amma aka ce masa binciken bai kammala ba," in ji shi.
Iyalan marigayin sun ce dalilin da ya sa suke matsa lamba a ba su rahoton sakamakon binciken abun da ya faru da shi shi ne saboda suna zargin cewa ba hatsari ya yi sanadin mutuwarsa ba.
Mansur ya ƙara da cewa ɗan uwansa yana cikin ƙoshin lafiya lokacin da suka yi magana ta wayar tarho a ranar da lamarin ya faru.
"Ni ne mutum na ƙarshe da ya yi magana da shi. Mun yi waya yana cikin ƙoshin lafiya, amma bayan kusan minti 30 sai aka kira mu aka ce wai ya yi hatsari," in ji shi.
Da aka tambaye shi game da rahoton 'yan sanda da ke cewa marigayin ya faɗo daga saman wani rukunin shaguna da ya je sayayya, Mansur ya ce ba su amince da wannan bayanin ba.
A cewarsa, marigayin ƙwararren ɗan wasa ne kuma ba su san yana da wata matsalar da za ta iya sa ya faɗo daga bene ba.
"Wannan ba gaskiya ba ne, mutum wanda yake cikin hankalin kan shi kuma ɗan wasa, ba ya da wata matsala ta taɓin hankali kuma a ce mana ya faɗo daga saman bene, wannan ba abu ne da hankali zai ɗauka ba."
'Dalilinmu na cewa kashe shi a ka yi'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ƙara da cewa bayan da aka dawo da mayar da gawarsa Najeriya, sun lura da wasu raunuka da suka sa suke tunanin an kai masa hari kafin mutuwarsa.
"Kuma da aka kawo mana shi, mun ga abun da ya faru da shi, mu gan cewa wannan sai da aka yi masa rauni sannan aka jefo shi daga sama, ko likitoci a nan Sokoto sun tabbatar mana da cewa an zuba masa acid a fuskan shi sannan suka aikata masa abun da suka aikata."
Duk da zargin da suke yi, Mansur ya amince cewa iyalan ba su da wata hujja kai tsaye da za ta nuna wanda ya aikata laifin.
Sai dai ya ce bayanan da suka samu daga binciken farko sun nuna cewa akwai wasu mutane biyu da aka ambata a wurin da lamarin ya faru.
"Takaimai ba mu da hujjar zargin kowa. Amma a rahoton farko an ambaci wani namiji da kuma wata mace da ta ce ta bar shi yana shan shayi tare da wani mutum kafin abin ya faru," in ji shi.
Ya ce an kuma ba su labarin cewa lokacin da jami'an tsaro suka isa wurin, sun tarar da wayoyinsa, maƙullan motarsa da kuma kofin shayin da yake sha.
'Har yanzu ba mu ga wani mataki daga gwamnatin Najeriya ko Uganda ba'
Mansur ya ce iyalan sun yi ƙoƙarin neman taimakon hukumomin Najeriya da na Uganda domin a ci gaba da binciken lamarin, amma har yanzu ba su ga wani gagarumin ci gaba ba.
"Gaskiyar magana, har yanzu ba mu ga wani mataki daga gwamnatin Najeriya ko ta Uganda da ya nuna cewa za a warware wannan lamari ko a tabbatar an ba shi haƙƙinsa ba," in ji shi.
Ya kuma ce iyalan na ci gaba da neman a kammala bincike tare da fitar da sakamakon da zai fayyace abin da ya janyo mutuwar ɗan wasan.
A halin yanzu, hukumomin Uganda sun tsaya kan bayaninsu na farko cewa mutuwar Abubakar Lawal ta faru ne sakamakon faɗuwa daga wani bene, yayin da iyalansa ke ci gaba da neman ƙarin bayani da kuma cikakken rahoton binciken hukuma.
Wane ne Abubakar Lawal?
Abubakar Lawal ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan Najeriya da aka haifa a ranar 3 ga Satumba, 1995 a jihar Sokoto.
Ya rasu a ranar 23 ga Fabrairu, 2025 a Kajjansi, Uganda.
Lawal ya fara rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa ne a Najeriya, inda ya fara buga wasa da ƙungiyar Wikki Tourists a watan Janairu 2019. A lokacin da yake tare da wannan kulob, ya nuna ƙwazo da kuzari abin da ya sa ya fara jan hankalin masu bibiyar wasanni.
Ya shafe kakar wasa guda a Wikki Tourists kafin daga baya ya koma Nasarawa United a watan Nuwamba 2020, inda ya ci gaba da haɓaka fasaharsa a matsayin centre-forward
Bayan wannan mataki, a watan Yulin 2022 ya tsallaka zuwa ƙasar Rwanda inda ya rattaɓa hannu da AS Kigali. Wannan sauyin ya ƙara masa kwarewa a matakin ƙwallon ƙafa na ƙasashen waje, inda ya fara samun gogewa a gasannin ƙwallon ƙafa na nahiyar Afirka.
Daga baya, Lawal ya koma Uganda inda ya shiga ƙungiyar Vipers SC, kulob ɗin da ya fi shahara da shi a ƙarshen rayuwarsa ta wasa.
A nan ne ya kafa ɗaya daga cikin manyan abubuwan da za a riƙa tunawa da shi a tarihi, lokacin da ya zura ƙwallo ta farko a tarihin Vipers SC a CAF Champions League. Wannan ƙwallo ta taimaka wa ƙungiyarsa samun 1–1 da Raja Casablanca, ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a Arewacin Afirka.
Masu horar da shi da abokan wasansa sun sha bayyana shi a matsayin ɗan wasa mai jajircewa, wanda ba ya gajiya cikin wasa











