Sancho ya yi watsi da tayin Getafe, PSG na son tsawaita zaman Doue

Jadon Sancho
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan gefe na Ingila, Jadon Sancho, ya ƙi amincewa da tayin da ya samu daga Getafe ta ƙasar Spain (La Liga), amma yana da wani tayin daga ƙasar Saudiyya. Ɗan wasan mai shekara 26 ba shi da ƙungiyar da yake bugawa wasa a halin yanzu, tun bayan barin Manchester United a bazara. (Marca)

Ɗan wasan gaba na Faransa, Desire Doue, mai shekara 21, yana tattaunawa kan tswaita kwantiraginsa da Paris St-Germain. Ƙungiyar ta Ligue 1 na son tabbatar da zaman sa na dogon lokaci, yayin da kungiyoyi irinsu Arsenal da Chelsea da Manchester City su ma ke nuna sha'awar ɗaukar sa. (Teamtalk)

Everton na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan gaba na Manchester United da Ingila, Marcus Rashford, mai shekara 28. (Football Insider)

Liverpool na tattaunawa da ɗan wasan tsakiya na Monaco kuma dan ƙasar Senegal, Lamine Camara, mai shekara 22, wanda ya kusan komawa Chelsea a bazarar da ta gabata. (Sun)

Chelsea na ci gaba da nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan baya na Everton kuma ɗan ƙasar Ingila, Jarrad Branthwaite, mai shekara 24, amma za ta fuskanci hamayya daga Manchester United. (Football Insider)

Everton na sa ido kan ɗan wasan gaba na Real Sociedad kuma ɗan ƙasar Iceland, Orri Oskarsson, mai shekara 22, yayin da ƙungiyar ke ƙoƙarin ƙarfafa ɓangaren ƴan wasan gabanta. (Teamtalk)

Chelsea na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Barcelona kuma ɗan ƙasar Spain, Fermin Lopez, yayin da Paris St-Germain ma ke nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan mai shekara 23. (CaughtOffside)

Leeds United za ta yi ƙoƙarin ɗaukar ɗan wasan baya na Porto, ɗan Najeriya Zaidu Sanusi mai shekara 29, a watan Janairu. (Football Insider)

Arsenal da Manchester United, da Chelsea na daga cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan tsakiya na Como, Nico Paz; duk da cewa ƙungiyar ta Serie A ba ta da niyyar sayar da ɗan wasan na Argentina mai shekara 22. (Teamtalk)