Wane mutum ne ya fi kowa tsufa a duniya yanzu haka?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Ku san mutum mafi tsufa a duniya da kuma wasu daga cikin waɗanda suka taɓa riƙe wannan kambun.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sister André, Bafaranshiyar da ta mutu a 2023 tana da shekara 118.

Ɗan'adam mafi tsufa da aka taɓa tabbatar da ya rayu a duniya ita ce Jeanne Louise Calment, wadda ta rayu har zuwa shekara 122 da kwana 164 a duniya.

A ƙa'ida idan aka ce mutum mafi tsufa a duniya, ana nufin wanda aka tabbatar da shekarunsa ta hanyar takardar haihuwa ko bayanan haihuwarsa na asibiti a hukumance.

Abin mamaki ne idan aka yi tunanin irin abubuwan da ita Calment da sauran mutanen da suka kai shekara 110 ko fiye suka gani a rayuwarsu.

Ka yi tunanin yadda rayuwa ta kasance a lokacin da suke matasa a shekarun 1920, da yadda suka shaida Yaƙin Duniya na Farko da na Biyu, suka ga saukar ɗan Adam a duniyar wata suna cikin shekaru 50 ko 60 na rayuwarsu, sannan suka ci gaba da rayuwa har zuwa ƙarni na 21 inda suka shaida gagarumin ci gaban kimiyya da fasaha.

Ya zuwa watan Satumban 2026, mutum mafi tsufa a duniya da ke raye ita ce Ethel Caterham ta Birtaniya, wadda kwanan nan ta cika shekara 117.

Wannan shekara ta zarce matsakaicin tsawon rayuwar ɗan Adam da nisa.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lokacin da Sarki Charles III ya ziyarci Ethel Caterham, wadda a yanzu ke da shekara 117 a duniya.

A Birtaniya, matsakaicin tsawon rayuwar maza shi ne shekara 79.1, yayin da mata ke rayuwa har zuwa matsakaicin shekara 83, a cewar Hukumar Kididdiga ta Ƙasar (ONS).

A Amurka kuma, matsakaicin shekarun rayuwa sun ɗan ragu kaɗan, inda ake sa ran maza za su rayu zuwa shekara 76.5, yayin da mata za su kai shekara 81.4.

Tsawon rayuwar mutane na bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa, har ma daga yanki zuwa wani a cikin ƙasa ɗaya, saboda dalilai daban-daban da suka haɗa da al'adu da yanayin kiwon lafiya da tsafta da kuma ci gaban kimiyya.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi hasashe a shekarar 2024 cewa matsakaicin tsawon rayuwar mutane a duniya ya kai shekara 73.3, wanda ya zarce na shekarar 1995 da kusan shekara takwas.

Wane mutum ne ya fi kowa tsufa a duniya yanzu haka?

Mutum mafi tsufa da ke raye a duniya zuwa watan Satumban 2026 ita ce Ethel Caterham, mai shekara 117 a duniya.

An haifi Ethel Caterham a ranar 21 ga Agustan shekara ta 1909 a yankin Hampshire na Ingila, a zamanin mulkin Sarki Edward VII.

A cewar kundin adana tarihi na 'Guinness World Records', ita ce ta biyu cikin yara takwas da iyayenta suka haifa.

Abin mamaki kuma, ƙanwarta Gladys Babilas ita ma ta rayu fiye da shekara 100, inda ta rasu tana da shekara 104 da kwana 78.

Mijinta, wanda suka fara haɗuwa a shekarar 1931, ya rasu a 1976.

Ya bar mata motarsa ƙirar Triumph Dolomite, wadda Ethel ta ci gaba da tuƙawa har sai da ta kai shekara 97.

Sai dai abin baƙin ciki shi ne, Ethel ta rayu har ta ga rasuwar ƴaƴanta biyu gabanta.

Mutanen da suka taɓa riƙe kambin mafiya tsufa a duniya

Jeanne Louise Calment - Mafi tsufa da aka tabbatar a duniya

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jeanne Louise Calment

Jeanne Louise Calment ce mutum mafi tsufa da aka taɓa tabbatar da ta rayu a tarihi.

A hukumance an amince da tarihin rayuwarta, inda Bafaranshiyar ta rayu har zuwa shekaru 122 da kwana 164 a duniya.

An haife ta ne a ranar 21 ga Fabrairun 1875, kuma ta rasu a ranar 4 ga Agustan 1997 tana da shekaru 122.

A cewar kundin Guinness World Records, Calment kan ci kusan kilogram ɗaya na cakulan a kowane mako, sannan ta fara shan taba sigari tana da shekara 21, wata ɗabi'a da ta daina tana da shekara 117.

Har ila yau, ta taɓa cewa ta sayar wa fitaccen mai zanen nan na Holland, Vincent van Gogh, zane-zane, inda ta bayyana shi a matsayin mutum mara kyan fuska, mai saurin fushi kuma mai wari kamar na barasa.

Jiroemon Kimura – Namijin da ya fi kowa jimawa a duniya

.

Asalin hoton, Getty Images

Jiroemon Kimura ya rayu har zuwa shekara 116 da kwana 54.

An haifi mutumin ɗan ƙasar Japan a ranar 19 ga Afrilun 1897, kuma ya rasu a ranar 12 ga Yunin 2013.

A cewar Guinness World Records, ya taɓa cewa: "Ka rage cin abinci idan kana son tsawaita rayuwa."

Har ila yau, ya ci gaba da aikin noma har sai da ya kai shekara 90 a duniya.

Lucile Randon – Shekara 118

Wata Bafaranshiya kuma, Lucile Randon, ta rayu har zuwa shekara 118 da kwana 340.

An haife ta a ranar 11 ga Fabrairun 1904, kuma ta rasu a ranar 17 ga Janairun 2023.

Kane Tanaka – Shekara 119

An haifi Kane Tanaka a ranar 2 ga Janairun 1903, kuma ta rasu a ranar 19 ga Afrilun 2022.

Wannan mata 'yar ƙasar Japan ta rayu har zuwa shekara 119 da kwana 107.

Chiyo Miyako – Shekara 117

Wata 'yar ƙasar Japan kuma, Chiyo Miyako, an haife ta a ranar 2 ga Mayun 1901, kuma ta rasu a ranar 22 ga Yulin 2018.

Ta rayu har zuwa shekara 117 da kwana 81.

Nabi Tajima – Shekara 117

.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Nabi Tajima ta rayu har shekara 117

Wata 'yar ƙasar Japan kuma, Nabi Tajima, ta rayu har zuwa shekara 117 da kwana 260.

An haife ta a ranar 4 ga Agustan 1900, kuma ta rasu a ranar 21 ga Afrilun 2018.

Violet Brown – Shekara 117

Idan muka koma ƙasar Jamaica, za mu tarar da Violet Brown, wadda ta rayu har zuwa shekara 117 da kwana 189.

An haife ta a ranar 10 ga Maris 1900, kuma ta rasu a ranar 15 ga Satumban 2017.

Emma Martina Luigia Morano – Shekara 117

.

Asalin hoton, OLIVIER MORIN/AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Emma Morano a 2016

'Yar ƙasar Italiya, Emma Martina Luigia Morano, ta rayu har zuwa shekaru 117 da kwana 137.

An haife ta ne a ranar 29 ga Nuwamban 1899, sannan ta rasu a ranar 15 ga Afrilun 2017.

María Branyas Morera – shekaru 117

María Branyas Morera ta rasu tana da shekaru 117 da kwana 168 a watan Agustan 2024.

A lokacin rasuwarta, ita ce mutum ta takwas mafi tsufa da aka taɓa tabbatar da ya rayu a tarihi.

An haife ta ne a ranar 4 ga Maris, 1907 a birnin San Francisco na jihar California a Amurka, kuma ta yi rayuwa a jihohin Texas da New Orleans kafin iyalinta 'yan asalin Spain su koma yankin Catalonia a lokacin Yaƙin Duniya na Farko.

A cewar Guinness World Records, ta taɓa bayyana cewa sirrin tsawon rayuwarta shi ne kasancewa cikin "tsari mai kyau da kuma kyakkyawar alaƙa da jama'a... rayuwa mai kyau ba tare da wuce gona da iri ba."

Susannah Mushatt Jones – Shekaru 116

Ba'amurkiya Susannah Mushatt Jones ta rayu har zuwa shekaru 116 da kwana 311.

An haife ta ne a ranar 6 ga Yulin 1899, sannan ta rasu a ranar 12 ga Mayun 2016.

Jeralean Talley – Miaka 116

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jeralean Talley a 2015

Mutum na ƙarshe a wannan jerin ita ce Jeralean Talley daga Amurka.

Ta rayu har zuwa shekara 116 da kwana 25 a duniya. An haife ta a ranar 23 ga Mayun 1899, sannan ta rasu a ranar 17 ga Yunin 2015.