Arsenal na nazari kan Vinícius, RB Leipzig ta ƙi tayin Madrid na Diomande

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal na duba yiwuwar zawarcin ɗan wasan gaba na gefe na Brazil, Vinícius Júnior, idan har ɗan wasan mai shekara 26 bai sabunta kwantiraginsa da Real Madrid ba. (The Athletic)

Sai dai sabon kocin Real Madrid, José Mourinho, na adawa da duk wani yunƙurin da Arsenal za ta yi na ɗaukar Vinícius a wannan bazarar, inda ya bayyana wa shugabannin ƙungiyar cewa yana son manyan taurarin tawagarsa su ci gaba da zama. (The Telegraph)

Arsenal a shirye take ta karya tarihin kuɗin cinikin ɗan wasa a Birtaniya domin ɗaukar ɗan wasan gaban Argentina, Julián Álvarez mai shekara 26, daga Atletico Madrid. (TeamTalk)

Inter Milan na sha'awar ɗaukar ɗan bayan Argentina, Cristian Romero mai shekara 28, daga Tottenham Hotspur. (Sky Sports)

RB Leipzig ta yi watsi da tayin fam miliyan 85.4 da Real Madrid ta gabatar domin sayen ɗan wasan gefen Ivory Coast, Yan Diomande mai shekara 19. Haka kuma Liverpool da Manchester City na cikin ƙungiyoyin da ke zawarcinsa. (Sky Sports)

AS Roma na nuna rashin jin daɗi kan yadda Manchester United ke jan ƙafa wajen gabatar da tayin sayen ɗan wasan tsakiya na Faransa, Manu Koné mai shekara 25. (Corriere dello Sport)

Juventus na nazarin yiwuwar ɗaukar kyaftin ɗin Manchester United, Bruno Fernandes mai shekara 31, bayan tattaunawa da wakilan ɗan wasan na Portugal. (CaughtOffside)

Chelsea ta yi watsi da tayi na uku da ƙungiyar Como ta yi domin sayen ɗan bayan Ingila, Trevoh Chalobah mai shekara 27. (Talksport)

Napoli na sha'awar ɗaukar tsohon wasa Faransa na Chelsea, Benoît Badiashile mai shekara 25. (The Sun)

Ɗan wasan tsakiyar Jamus, Julian Brandt mai shekara 30, yana da tayi daga Leeds United da kuma Ajax, bayan ya bar Borussia Dortmund a matsayin ɗan wasa mai cin gashin kansa. (Sky Sports)

Nottingham Forest ta gabatar da ingantaccen tayi na fam miliyan 17.5 domin sayen ɗan baya na dama na Feyenoord, Givairo Read mai shekara 20. (Daily Mail)

West Ham United ta yi watsi da tayin da Brentford ta gabatar domin sayen ɗan baya na hagu na Senegal, El Hadji Malick Diouf mai shekara 21, tana mai jaddada cewa ba ta da niyyar sayar da shi. (Talksport)

Middlesbrough na sha'awar ɗaukar mai tsaron ragar Czech na Manchester United, Radek Vitek mai shekara 22, wanda ya buga aro a Bristol City a kakar wasan da ta gabata. (Sky Sports)