Trump ko Tinubu: Wa ya fi cin ribar ƙawancen tsaron Amurka da Najeriya?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Ƴan Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan yabon da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi wa gwamnatin Najeriya dangane da matakan da take ɗauka wajen yaƙi da matsalar tsaron ƙasar.

A baya Trump ya sha yin kira ga hukukomin Najeriya su ɗauki matakan da suka dace don yaƙi da matsalar tsaron ƙasar, musamman ikirarin da yake yi na yi wa Kiristoci kisan kiyashi a ƙasar, kodayake gwamnatin Najeriya ta sha musanta ikirarin.

To amma a ranar Laraba wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban Najeriya ta ce Shugaban Amurka Donald Trump ya yaba wa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu kan abin da ya kira "ƙwazon jagorancinsa" wajen yaƙi da ta'addanci da kuma magance matsalar tsaro a Najeriya.

Fadar shugaban ƙasar ta ce, a cikin wata wasiƙa da Trump ya aike wa Tinubu, ya ce yana yaba wa shugaban Najeriyar kan ƙudirin da yake da shi na magance matsalolin da suka addabi ƙasar, musamman hare-haren da ke shafar al'ummomin Kiristoci.

Me wasiƙar Trump ta ƙunsa?

Wasiƙar wadda da alama da martani ce kan wata wasiƙar da Tinubun ya aike wa Trump ta fara ne da gode wa shugaban na Najeriya.

"Na gode da wasiƙar da ka aiko mai cike da karamci. Kyawawan kalamanka na da matuƙar muhimmanci gare ni, kuma ina yaba wa jagorancinka mai cike da ƙwazo a madadin al'ummar Najeriya''.

Ina yabawa ƙudurinka na magance matsalolin da ke addabar ƙasarka, musamman tashin hankalin da ke shafar al'ummomin Kirista, kuma abin alfahari ne gare ni in tsaya tare da kai wajen yaƙi da ta'addanci da kuma tabbatar da cewa Najeriya ta zama ƙasa mafi ƙarfi da wadata.

Dangantakar da ke tsakanin Amurka da Najeriya na da matuƙar muhimmanci a wannan lokaci da rikice-rikice suke yaɗuwa a faɗin Yammacin Afirka da ma duniya baki ɗaya.

Dukkanmu muna da manufa ɗaya ta yaƙi da ta'addanci ta kowace siga, kuma sabon ƙawancen tsaro na Amurka da Najeriya na 2026 ya samar da ingantaccen harsashi domin cimma wannan buri.

Ina alfahari da tura rundunar musamman ta Amurka (United States Special Operations Forces) – waɗanda ke cikin ƙwararrun sojoji mafiya gogewa a duniya – domin bai wa dakarun Najeriya horon ƙwarewa da tattara bayanan sirri da suke buƙata don kare ƙasarku da tabbatar da tsaron ƴan ƙasa, musamman waɗanda hare-hare suka shafa saboda addininsu. Ina sa ran ci gaba da tattaunawarmu a tsawon lokacin shugabancina."

Ka huta lafiya,

Donald J. Trump

Shugaban Ƙasar Amurka

Yaushe ƙasashen suka ƙulla ƙawance?

A shekarar 2025 ne kasashen biyu suka kulla ƙawancen tsaro bayan Trump ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristocin Najeriya kisan kiyashi, tare da kira ga gwamnatin ƙasar ta magance matsalar.

A nata ɓangare gwamnatin Najeriya ta musanta batun kisan ''Kiristoci kaɗai'', tana mai cewa matsalar tsaron ƙasar na shafar kowane addini.

A ƙarshen shekarar da ta gabatan ne kuma ƙasashen biyu suka ƙulla yarjejeniyar tsaro domin yaƙi da matsalar tsaron Najeriya, inda a watan Disambar 2025 Amurka ta ƙaddamar da wani hari kan masu iƙirarin jihadi a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya.

Haka ma a farkon shekarar nan Amurka ta tura dakarunta kusan 200 zuwa Najeriya domin bayar da horo ga sojojin ƙasar kan yadda za su yaƙi ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.

Sai dai a farkon wannan da muke ciki, Amurka ta sanar da janye dakarun nata, bayan da take sun kammala aikin da ya kai su Najeriya, kwanaki bayan da Donald Trump ya ce an samu nasarar kawo ƙarshen kisan Kiristoci a Najeriya.

Wa ya fi cin riba?

Duka ɓangarorin biyu na ikirarin samun nasarar ƙawancen tsaron da ƙasashen biyu suka cimma, to amma abin da mutane ke tambaya shi ne waye ya fi cin ribar tsakanin Trump da Tinubu?

Dr Kabiru Adamu mai nazari kan harkokin tsaro a yankin Sahel ya ce a ganinsa Shugaba Tinubu na Najeriya ne ya fi cin ribar ƙawancen.

''Ni a ganina gwamnatin Najeriya ce ta ci ribar wannan ƙawance, saboda hakan ya taimaka wajen kyautata alaƙa tsakanin gwamnatocin ƙasashen''.

Masanin tsaron ya kafa hujja da yadda Amurka ta kama shugaban ƙasar Venezuela, bayan jerin gargaɗin da ta riƙa yi masa amma bai ɗauki mataki ba.

''Mun ga yadda sojojin Amurka suka kai samame har fadar gwamnatin Venezuela tare da kama shugaban ƙasar da mai ɗakinsa, suka kuma tafi da su Amurka'', in ji shi.

Ya ce a baya yadda Amurka ta riƙa yi wa gwamnatin Najeriya barazanar kai ɗauki, idan gwamnatin ƙasar ba ta magance matsalar ba.

''Amma ta kai yanzu da kansa Trump ya fitar da sanarwa yana yabon gwamnatin Najeriya, wannan ba ƙaramar nasara ba ce ga gwamnatin Tinubu'', in ji shi.

Haka shima Dr Audu Bulama Bukarti mai nazarin harkokin tsaro a ƙasashen Afirka ya ce gwamnatin Tinubu ce ta ci riba.

"Ai da fari ka ga ƙara aka kai gwamnatin Tinubu zuwa ga Trump domin a ɓata mata suna, amma sai gwamnatin ta yi amfani da damar wajen kyautata alaƙa da gwamnatin Trump har hanzu aka je idan Trump ke yabon gwamnatin Tinubu'', in ji Bukarti.

A ɓangaren Shugaba Trump kuwa masanan sun ce shi ma ya samu ribar ƙawancen.

Dr Kabiru Adamu ya ce akwai wasu muradu uku da Amurka ke son cimmawa a duk lokacin da ta ƙulla yarjejeniyar tsaro da wata ƙasa:

''Na farko shi ne kada dakarunta su jima wannan ƙasar bayan tura su, kuma hakan ne ya faru a Najeriya, dakarun Amurka ba su jima ba suka fita''.

''Na biyu shi ne dole ne ta amfana da batun tattalin arziki, kuma ka ga akwai wasu ma'adinan Najeriya da Amurka da China ke kokawar amfana da su, don haka wannan ƙawance zai taimaka wa Amurkan cimma hakan'', in ji Dr Kabiru Adamu.

Na uku shi ne batun kisan Kirista, wanda kuma ya ce har yanzu ana kai hare-haren, kuma shugabannin Kirista sun musanta nasara a wannan fanni.

Dr Bukarti ya ƙara da cewa ta yiwu gwamnatin Trump ta ci ribar cinikin makamai daga Najeriya, saboda wannan ƙawance da gwamnatocin biyu suka ƙulla.

'Da sauran rina a kaba'

Duk da wannan nasara da wasiƙar Trump ta yi iƙirarin samu a Najeriya masana tsaro na cewa har yanzu da sauran rina a kaba.

Dr Kabiru Adamu ya ce har yanzu ana kai hare-hare a jihohin Plateau da Benue da Taraba, waɗanda Kiristoci suka fi yawa.

''Kuma dama hare-haren da ake kai wa waɗannan jihohi ne ya sa Trump ya yi iƙirarin kisan Kiristoci a Najeriya'', in ji shi.

Dr Bulama Bukarti ya ce saɓanin yadda wasiƙar Trump ta yi iƙirarin magance matsalolin tsaro a Najeriya, har yanzu matsalar ba ta ƙara be.

''A dai iya cewa ƙawancen ya fara taimakawa, amma akwai buƙatar ci gaba da taimakawa domin magance matsalar baki ɗaya'', in ji Dr Bukarti.