Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ake cire ƙodar ƴan ci-rani a Libya
- Marubuci, Ben Milne
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Marubuci, Sue Mitchell
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Sama da ƴan cirani 300 da suke hanyar zuwa Birtaniya a bazarar da ta gabata aka yi garkuwa da su, tare da azabtar da su da yi musu barazanar cire sassan jikinsu ta ƙarfi, kamar yadda BBC ta gano.
Ƴan bindiga a Libya ne suka kama matasan waɗanda dukkaninsu ƴan Kurdistan ne a Iraki, inda suka buƙaci iyalan kowane murtum su biya kuɗin fansa dalar Amurka 5,000, kuma suka yi barazanar cire ƙodar waɗanda aka kama idan ba a biya su cikin gaggawa ba.
Mun zanta da wasu mutanen da aka yi garkuwa da su bayan an sako su, kuma muka ga hotuna da ke nuna cewa an azabtar da su.
Waɗanda aka yi garkuwa da su sun nuna mana shaidar azabtarwa, kuma sun ce an ajiye su a cikin matsanancin yanayi, inda kusan mutane 180 ke kwana a ɗaki guda.
Aƙalla mutum ɗaya da aka yi garkuwa da shi ne aka samu rahoton ya mutu, kuma ba a san adadin waɗanda aka yi garkuwa da su ba.
Ƴan bindigar ne ya kamata su jagoranci baƙin hauren ta Libya zuwa gabar tekun Bahar Rum. Sai dai an samu saɓani kan biyan kuɗadensu da wani wakilinsu ɗan ƙasar Iraƙi Nuhu Aaron ya kamata ya biya, wanda shi ne ya shirya musu tafiyar.
A yanzu dai Aaron yana zaman gidan kaso na tsawon shekaru 10 a ƙasar Faransa bisa samunsa da laifin halasta kuɗin haram da laifukan fasaƙwauri.
An samun bayanai game da garkuwa da mutanen a wani bincike da BBC ta gudanar a baya-bayan nan kan wani ɗan fasa kwauri, Kardo Jaf, wanda ya kai ga an kama shi a watan jiya.
An kyautata zaton cewa masu fasaƙwaurin sun yi aiki tare. Dukkansu biyun ƴan garin Ranya na Kurdistan da ke Iraƙi ne - yankin da ke fama da ayyukan fasaƙwauri", a cewar wani rahoto da wata cibiyar bincike ta Burtaniya, Chatham House ta fitar.
A watan Fabrairu, BBC ta yi bincike game da Jaf a Ranya, lokacin da wani mutumin yankin ya tuntube ta, inda ya ce dansa na cikin wadanda aka kama.
Mutumin ya shaida wa BBC cewa ƙungiyar masu fasaƙwaurin ta Aaron ta karɓi kuɗi a hannu ƴan uwansa da suka kai dubban daloli saboda shirya tafiyarsa zuwa Birtaniya, wadda za ta hada da bi ta arewacin Afirka, sannan ta tsallaka tekun Mediterrenean zuwa Turai.
Hanyar dai za ta bi ne ta ƙasar Libya, ƙasar da ba ta wata "tsayayyar gwamnati", a cewar Anthony Dunkerley, mashawarcin Majalisar Dinkin Duniya da ya binciki fataucin mutane a can.
Yawancin ƙasar Libya dai na ƙarƙashin ikon mayaƙa ne, kuma masu safarar mutane sun dogara da su ne domin samun haɗin kai.
Mun samu labarin cewa, a lokacin bazara a shekarar 2025, an tafi da gungun ƴan cirani da suka taso zuwa Libya daga Kurdistan na Iraki zuwa wani wurin da ake tsare da su kuma aka ɗaure su.
Daga nan ne ƴan bindigar suka buƙaci dala 5,000 daga iyalan duk waɗanda aka yi garkuwan da su, inda suka ce Aaron ya ƙi biyan kuɗin da suka yi yarjejeniya. Idan kuma aka ƙi kai kuɗin da sauri ba, sun yi barazanar cewa "za su cire musu ƙoda" a madadin kuɗin.
Ƴan Libyar sun kuma aika da hotuna da bidiyo na mutanen da aka yi garkuwa da su, waɗanda da yawa daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali da tashin hankali. A ɗaya daga cikin bidiyoyin, an ga yadda ake sanar da wani matashi cewa za a kai shi wurin likita ne domin a cire masa ƙoda.
Wani mutum a Ranya ya shaida mana cewa ya biya kuɗin fansar. Ɗansa yana cikin mutum 110 da aka yi garkuwa da su a watan Junairu, inda aka maida su Iraƙi a jirgin da gwmanati ta kai ya kwaso su. Sai dai ya nuna wani hoto da ke nuna ɗan nasa a lokacin da yake tsare, tare da raunuka a jikinsa, inda yake fargabar an cire masa wani sashe na jikinshi.
Ba a jima da fara tattaunawa da mutumin ba, gomman mutane suka zo da irin waɗannan hotunan na ƴan uwansu.
Mun nuna wa wani likita a Birtaniya ɗaya daga cikin hotunan, inda ya ce raunukan da ke jikinsu alamu ne na tiyatar cire ƙoda a jikin mutum. Amma ya ce ba za a iya tabbatar da cewa ko an cire musu wani sashin jikinsu ba.
Akwai rahotanni da dama na yin garkuwa da ƴan cirani a hanyar Libya. Masu aikata laifuka na amfani da wasu hanyoyi da dama a ƙasar, lamarin da ya sa ba a iya kama mutane sosai domin gudanar da bincike da gurfanar da su, in ji Dunkerley
An saki yawancin mutanen da aka kama ɗin. Wasu daga ciki ƴan uwansu ne suka biya kuɗin fansa a kan lokaci, amma hukumomi a Kurdistan na zargin wasu sun biya ne da sassan jikinsu.
BBC ta tattauna da wasu da suka dawo Ranya.
Wani matashi ya ce an azabtar da shi tare da ƙona mishi ƙafa. Ya janye wandonsa har ya nuna mana raunin.
Matashin ɗan kimanin shekaru 16 ya ce yana daga cikin mutum 178 da aka tsare a ɗaki guda.
"Ba mu ga rana ba na tsawon watanni shida," in ji shi.
Ya bayyana cewa wajen a matse yake sosai ta yadda kowa sai dai ya yi bacci a tsaye. Duka waɗanda aka kama suna amfani da banɗaki guda ɗaya ne kuma idan mutum ya daɗe a bayi za mishi duka.
Food consisted of one piece of bread per day, the hostages' families told the BBC - but only if they paid the captors extra money.
Ana ba su burodi sau ɗaya a matsayin abincinsu na kowace rana, kamar yadda ƴan uwan waɗanda aka kama suka shaida wa BBC, amma idan suka biya ƙarin kuɗi za a sayo musu abinci.
Duk da irin hatsarin da ke tattare da lamarin, ba a daina samun kwararar baƙin haure daga Kurdistan na Iraƙi zuwa Turai ba, a cewar Hemn Merany, babban jami'i a ma'aikatar harkokin cikin gida ta yankin Kurdistan.
Ya buƙaci waɗanda aka yi garkuwa da su, su faɗa wa abokai da ƴan uwansu abubuwan da suka faru da su na ban tsoro, don hana su yin irin wannan tafiya.
Ya ba mu labarin wani mahaifi da ɗansa ya mutu a Libya bayan da ake zargin an cire masa wasu sassan jikinsa ta ƙarfin tsiya. A wajen jana'izarsa da aka yi a Ranya, mutumin ya samu labarin cewa wasu ƴaƴan ɗan uwansa biyu sun tafi Turai kwanan nan.
"Babban abin damuwar shi ne mutane sun kasa ɗaukar darasi," in ji Merany.