Wace irin alaƙa ce tsakanin China da Koriya ta Arewa?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Bayan jeka-ka-dawo, shugaban ƙasar China Xi Jinping ya gudanar da ziyara a ƙasar Koriya ta Arewa cikin wanan mako.

Ganawar da aka daɗe ana tsimaye ta faru ne tsakanin ranakun 8 zuwa 9 ga watan Yuni, bayan wata ganawar da shigaban Xi ya yi da takwarar aikinsa na Rasha Vladimir Putin da kuma na Amurka Donald Trump.

Kasancewar ziyararsa kai-tsaye zuwa birnin Pyongyang a matsayin ta farko zuwa wata ƙasa, hakan na ƙara nuna alaƙar ƙasarsa da maƙwafciyar tata.

Ƙasashen biyu na da alaƙa, amma ba wadda za a iya kira mai yauƙi ba, in ji Eun-ju Choi, mai bincike a cibiyar ilimi ta Sejong Institute da ke birnin Seol.

Ana kallon wannan ganawa a matsayin wadda za ta bai wa ƙasashen biyu wata sabuwar dama a dangantakar da ke tsakaninsu.

Soyayya ko tsana?

Daga waje, ƙasashen biyu za a iya cewa sun shawo tafiya mai nisa kuma mai sarƙaƙaiya, musamman game da alaƙarsu da ƙasashe masu maƙwaftaka.

A lokacin yaƙin Korea tsakanin shekarar 1950 zuwa 1953, China ta sadaukar da rayukan dubban ɗaruruwan sojojinta domin kare Koriya ta Arewa.

Shugaban China na wancan lokaci Mao Zedong ya yi wani shahararren kalami domin nuna muhimmancin Korea ta Arewa, inda ya ce "idan aka yanke leɓɓa, to asirin haƙora ya tonu."

To amma shugaban Koriya ta Arewa na farko Kim Il Sung ya nemi samun ƙarin tallafin soji ta hanyar ƙulla alaƙa da Tarayyar Soviet a shekarar 1961. Kwanaki kaɗan bayan ya ƙulla wata yarjejeniyar tsaro da China.

A tsarin Kim Il Sung, Koriya ta Arewa za ta nemi dogaro da janta, Amma samun goyon bayan manyan ƙasashe biyu masu ƙarfin soji na nufin za ta kauce wa haɗarin zama ƴar koren wata ƙasa guda ɗaya.

A wancan lokacin Koriya ta Arewa ta dogara da Tarayyar Soviet wajen samun tallafi da kuma man fetur, A ɓangare ɗaya tsananin yunwa da aka yi fama da ita ta tursasa wa ƴan ƙasar China tsallakawa zuwa Koriya ta Arewa. Inda wasu suka yi karatu a can, har ma suka yi amannar cewa ilimi a can ya fi inganci.

To sai dai Koriya ta Arewa ta yi hasarar babbar ƙasar ƙawancen soji a lokacin da Tarayyar Soviet ta wargaje a shekarar 1991. Wannan ya ƙara bai wa China dama.

China ta ci gaba da kasancewa babbar ƙawar kasuwanci da zuba jari da kuma dogaro ga Koriya ta Arewa, kuma a matsayin kariya daga Amurka.

"China ta riƙa samar wa Koriya ta Arewa tallafin tattalin arziƙi da zai ishe ta ci gaba da wanzuwa, amma kuma ba wanda zai ishe ta dogaro da kai ba," in ji Seong-Hyon Lee, wanda malamin wucin-gadi ne a jami'ar Harvard, kamar yadda ya shaida wa BBC.

A nata ɓangaren "China na son ganin Koriya ta Arewa ta kame kanta daga duk wani harka ko rikicin cikin gida na ƙasarta," in ji shi.

Ba a kodayaushe ne Koriya ta Arewa ta kiyaye hakan ba.

Muradin mallakar nukiliya

China za ta fi so a ce babu makamin nukiliya a yankin Koriya - amma duk da haka Koriya ta Arewa ta ci gaba da shirinta.

Kim Il Sung shi ne ya samar da tushen kafa rumbun nukiliya mafi ƙanƙanta, inda ya ƙaddamar da cibiyar binciken ayyukan nukiliya ta Yongbyon a shekarar 1964.

Duk da cewa ya sanya hannu kan dokar hana yaɗuwar makaman nukiliya ta 1985, ya yi watsi da sharuɗɗanta ya ci gaba da tara sanadarin plutonium. To amma bai yi tsawon rai zuwa lokacin da ƙasarsa ta mallaki makamin nukuliya ba.

Lokacin da ɗansa Kim Jond Il ya karɓi iko a 1994, ya yi amfani da shirin wajen samun tagomashi na diflomasiyya da tallafin tattalin arziki da kuma yin shiri da Amurka a matsayin fansar watsar da shirin.

A shekara 2003 Koriyabta Arewa ta fice daga yarjejeniyar hana yaɗuwar nukiliya. Shekara uku bayan haka ƙasar ta gudanar da gwajin makamanita na nukiliya karon farko - inda nan take Majalisar Dinkin Duniya ta ɗauki mataki ta hanyar ƙaƙaba wa ƙasar takunkumi.

Hakan ba zai yiwu ba ba tare da amincewar China ba. Wadda ta bayyana gwajina a matsayin aikin "ganganci", sannan ta buƙaci a raba yankin da makamin nukiliya - sai dai ta guje wa yin amfani da ƙarfin tattalin arziƙinta a matsayin makami.

"Rushewa ko kuma hargitsi a Koriya ta Arewa zai zamo abu mai haɗari ga China: za a samu kwararar ƴan gudun hijira, rashin tabbas kan makamin nukiliya da kuma haɗarin ƙara matsowar Amurka ko kuma Koriya ta Kudu zuwa arewaci," in ji Choi. Waɗannan damuwoyi sun fi muhimmanci a kan mallakar makamin nukuliya da Koriya ta Arewa ta yi.

Lokacin da Kim Jong Un ya hau karagar mulki a 2011, ya haɓɓaka samar da makaman roka fiye da yadda China za ta iya kwaɓawa.

Jim kaɗan bayan hawan sa kan mulki ya yi gyara ga kundin tdarin mulki tare da attana Koriya ta Arewa a matsayin ƙasar da ta mallaki nukiliya sannan ya yi gwaje-gwajen makamai daidai loacin da China ke gudanar da nata sauye-sauyen.

Gabanin rantsar da Xi a masayin shugana China a shekarara a watan Maris ɗin 2013, Kim ya yi gwajin nukiliya sau uku. Ya kuma zartar da hukuncin kisa kan kawunsa mai ra'ayin kawo sauyiJang Song-thaek, wanda ya taɓa zama jakada a China.

A matsayin martani, Xi ya goyi bayan tsaurara takunkumin Majalisar Dinkin Duniya a kan Koriya ta Arewa. Ya kuma goyi bayan ƙasar Koriya ta Arewa inda ya lashi takobin cewa "ba za a taɓa yarda da shirin nukiliya na Koriya ta Arewa ba".

Rasha ta zama sabuwar ƙawa

Yayin da Koriya ta Arewa ta ga maƙwaftanta sun haɗe mata kai, sai Kim ya yanke ƙauna da dogaro da China. Sai ya lura cewa a shirye Rasha take ta karɓe shi duk da cewa zai ɗauki lokaci kafin su sake ginda dangantakarsu.

A watan Afrilun 2014, Rasha ta yafe wa Kpriya ta Arewa kashi 90% na bashin da dala biliyan 11 da take nbon ta, sannan ƙasashen biyu suka ƙulla wasu yarjeniyoyi.

Sannan yaƙin da Rasha ta ƙaddamar kan Ukraine ya ƙara janyo Koriya ta Arewa kusa da ita.

Yayin da Vladimir Putin ke buƙatar makamai da sojoji, Kim kuma na buƙatar tallafi, da kasuwanci da kuma fasahar soji.

Amurka ta yi ƙiyasin cewa Koriya ta Arewa ta sayar wa Rasha makamam atilare sama da miliyan domin yaƙi a Ukraine, yayin da sama da sojojin Koriya ta Arewa 2,300 ne suka mutu suna yi wa Rasha yaƙi, kamar yadda binciken BBC ya bayyana.

Wani babban abu shi ne yadda a cikin watan Satumba, Xi ya karɓi baƙuncin Kim da Mutin a ranar murnar samun nasarar yaƙin duniya.

Wannan baje-kolin yauƙaƙar dangantaka ta kai ga sake buɗe sufurin jirgin ƙasan fasinja da kuma sufurin jirgin saman China kai-tsaye, tare kuma da zuyarar da Firimiyan China Li Qiang da ministan harkokin wajen ƙasar Wabg Yi suka kai Koriya ta ARewa.

Lee ya ce matakin China na baya-bayan nan na nuna goyon baya ga shirin nukiliyar Koriya ta Arewa ya nuna yadda ya sauya ra'ayi game da ƙasar mai bin tsarin mulki mai kamanceceniya.

Alamu na nuna cewa Xi yanzu ya karkata ga Koriya ta Arewa.

Ita kuwa Koriya ta Arewa tana amfai da badarar rashin bayar da kai cikin sauƙi.

"Ta ɓangarori da dama Koriya ta Arewa ce ta fi cin ribar wannan dangantaka mai ƙusurwa uku," in ji Kim. "Rasha da Cina kuwa duk sujan da dalilin da zai sa su janyo Koriya ta Arewa kusa da aus."

-Ƙarin bayani daga Grace Tsoi