Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid ta nace wa Rodri, Juve ta karɓo Randal Kolo Muani
Real Madrid na da ƙwarin guiwa kan ɗauko ɗanwasan tsakiya na Spain da Manchester City Rodri mai shekara 30- wanda shekara ɗaya ta rage kwantaraginsa ya ƙare a City - ana tunanin Madrid za ta biya fam miliyan 34 zuwa 43 kuma zuwa Alhamis ake sa ran kammala cinikin bayan tattaunawa. (AS - in Spanish)
Inter Milan na iya sake ɗaukar matakai na sabon tayi kan ɗanwasan tsakiya na Ingila mai shekaru 25, Curtis Jones daga Liverpool.
A ɗaya bangaren kuma, ɗauko ɗanwasan bayan Ingila John Stones, mai shekaru 32, ba tare da an biya kuɗin saye ba, na iya karya fatan ɗanwasan bayan Argentina mai shekaru 28, Cristian Romero, na komawa ƙungiyar ta Italiya daga Tottenham. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Juventus ta amince da yarjejeniya da Paris St-Germain kan ɗanwasan gaban Faransa Randal Kolo Muani. Ɗanwasan zai tafi ne a matsayin aro da zaɓin saya kan fam miliyan 50. (Sky Sports Italia - in Italian)
Brentford na dab da ɗauko ɗanwasan tsakiya na Lens da Mali Mamadou Sangare, mai shekara 24, domin maye gurbin Jordan Henderson. (Evening Standard)
Palmeiras ta yi watsi da tayin Aston Villa na fam miliyan 26 kan ɗanwasan gaba na Brazil Allan, mai shekara 22. (ESPN)
Hull City na tattaunawa da Aston Villa domin ɗauko ɗanwasan Jamaica Leon Bailey. (Sky Sports)
Royale Union Saint-Gilloise ta Belgium ta yi watsi da tayin Nottingham Forest kan ɗanwasanta na Isra'ila Anan Khalaili. (Athletic - subscription required)
Manchester United na tunanin sayar da golanta na Czech Radek Vitek da kuma ɗanwasan baya na Ingila Harry Amass, mai shekara 19. (Mail – subscription required)
Nottingham Forest na cikin ƙungiyoyin da ke son ɗauko ɗanwasan tsakiya na Portugal Gustavo Sa daga Famalicao, yayin da ake tunanin ɗanwasan mai shekara 21 zai tafi Olympiacos ta Girka a matsayin aro. (Athletic - subscription required)