Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manyan makaman Amurka uku da suka kusa ƙarewa a yaƙin Iran
Lokacin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi jawabi a taron ƙoli na tsaro da ƙirƙira a jihar Pennsylvania a farkon wannan wata, a gaban shugabannin manyan kamfanonin ƙera makamai na Amurka, saƙonsa guda ɗaya ne: a ƙara saurin kera makamai.
A lokacin jawabin, Sakataren Tsaron Amurka Pete Hegseth ma yana wurin. Gwamnatin Trump ta bayyana taron a matsayin wani ɓangare na shirin farfaɗo da masana'antun Amurka da kuma ƙarfafa ƙarfin yaƙin ƙasar.
Sai dai ba a bayyana a taron yawan makaman da Amurka ta kashe a yaƙin da ta yi da Iran ba, ko kuma adadin da ya rage a ma'ajiyarta bayan hare-haren da aka kai, waɗanda suka ɗauki kusan kwanaki 40.
A cewar gwamnatin Amurka, yaƙin ya ci kusan dala biliyan 37.5, kuma babban kaso na kuɗin ya tafi ne wajen amfani da makamai da alburusai.
Fadar White House ta ce tun bayan fara tsagaita wuta a ranar 8 ga Afrilu, sojojin Amurka sun kai hare-hare kan wurare sama da 13,000 a Iran.
A lokaci guda kuma, tsarin kare sararin samaniyar Amurka ya lalata sama da jiragen sama marasa matuƙa da makamai masu linzami sama da 1,700 da Iran ta harba.
Rahoton jaridar New York Times ya ce an shawarci Trump da ya guji tsananta yaƙin saboda raguwar makaman da Amurka ke fuskanta.
Sai dai a ranar Litinin, Trump ya musanta rahotannin da ke cewa makaman Amurka sun ragu.
"Muna da makamai fiye da kowace ƙasa a duniya, kuma sun fi yawan abin da muke buƙata," in ji shi.
Batun yawan makaman da suka rage ya daɗe yana zama abin muhawara a cikin gwamnatin Amurka.
Yadda rumbun makaman Amurka ya zagwanye
A watan da ya gabata, Sakataren Tsaro Pete Hegseth ya musanta cewa akwai ƙarancin makamai ko harsasai.
Amma yanzu alamu na nuna cewa matsalar tana ƙara fitowa fili. A makon da ya gabata ya gaya wa kwamitin Majalisar Dattawan Amurka cewa Pentagon na buƙatar ƙarin dala biliyan 87 domin sayen makamai da kayan aikin soja.
Duk da cewa cikakken bayani game da makaman da aka kashe da waɗanda suka rage sirri ne, bayanan da cibiyar Center for Strategic and International Studies (CSIS) ta tattara sun nuna cewa an samu raguwa mai yawa a wasu muhimman makamai.
"Ya danganta da irin makamin da ake magana a kai, amma ƙera makami mai linzami na iya ɗaukar shekara ɗaya zuwa biyar. Kuma babu wata hanyar da za ta sa hakan ya zama cikin gaggawa," Mark Cancian, tsohon kanal a rundunar Marines ta Amurka kuma mai ba da shawara a CSIS.
Makaman da aka fi amfani da su a yaƙin sun kasu kashi biyu:
- Makaman kai hare-hare daga nesa.
- Makaman kariyar sararin samaniya da kariyar makamai masu linzami.
Makamin Tomahawk
Ɗaya daga cikin makaman da aka fi amfani da su shi ne Tomahawk, wanda ake harbawa daga jiragen ruwa ko jiragen karkashin teku zuwa wuraren da ke nisan fiye da kilomita 1,600.
Wannan makami yana ba Amurka damar kai hare-hare ba tare da kuskurewa ba kan sansanonin soja da cibiyoyin umarni da sauran wuraren da aka ƙarfafa kariya.
CSIS ta kiyasta cewa an harba fiye da makamai Tomahawk 1,000 a yaƙin Iran, kuma ana sa ran ba za a dawo da adadinsu na kafin yaƙi ba sai zuwa shekarar 2031.
Farashin kowane Tomahawk na zamani ya kai kusan dala miliyan 2.6.
Makamin Patriot
Makamin kariya da aka fi amfani da shi shi ne Patriot, wanda ake amfani da shi wajen harbo jiragen sama, makamai masu linzami da kuma jirage maras matuƙa.
CSIS ta kiyasta cewa an yi amfani da kusan makaman Patriot 1,430 yayin yaƙin, daga cikin adadin kusan 2,330 da ake da su kafin yaƙin.
Farashin kowane Patriot ya kai kusan dala miliyan 4.
Duk da tsadarsa, ana ɗaukar sa a matsayin makami mai tasiri sosai saboda yana iya harbo jirgi maras matuƙi na Iran waɗanda farashinsu tsakanin dala dubu 20 zuwa 50 ne kacal.
Tsarin THAAD
An kuma yi amfani da tsarin kariya mafi zamani da ake kira THAAD.
Wannan tsarin ya fi Patriot ƙarfin kai hari daga nesa da kuma aiki a ƙololuwar sama mafi yawa.
CSIS ta kiyasta cewa an yi amfani da tsakanin 190 zuwa 290 daga cikin kusan 360 da ake da su kafin yaƙin.
A duniya baki ɗaya akwai batirorin THAAD guda tara ne kawai da ke aiki, bakwai daga cikinsu mallakin Amurka ne.
Masana sun yi gargadi cewa idan aka ci gaba da kashe waɗannan makamai ba tare da saurin maye gurbinsu ba, Amurka na iya fuskantar matsala wajen kare kanta daga barazanar makamai masu linzami daga ƙasashe irin su Rasha da China.
Bayanan da ake da su sun nuna cewa yaƙin Iran ya sa Amurka ta kashe manyan makamai masu tsada da yawa, musamman Tomahawk, Patriot da THAAD.
Duk da cewa gwamnatin Trump ta musanta cewa akwai matsalar ƙarancin makamai, masana da wasu rahotanni na nuna cewa sake cike ma'ajiyar waɗannan makamai na iya ɗaukar shekaru da dama.