Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me zai faru idan INEC ta soke rijistar jam'iyyar ADC?
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
A Najeriya, ana ta cece-ku-ce kan wani hukuncin kotun da ya umurci hukumar zaɓe ƙasar, INEC ta soke rijistar ɗaya daga cikin manyan jam'iyyun adawa ADC, da wasu guda huɗu.
Kotun tarayyar ƙasar ta ce jam'iyyun da hukuncin ya shafa sun gaza cika sharuɗɗan da kundin tsarin mulki ya tanada, na samun aƙalla kashi 25 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓuka bayan yi musu rijista, ko kuma lashe aƙalla wata kujera ɗaya.
Jam'iyyun da hukuncin ya shafa su ne Accord, APP, AA, ADC da ZLP. Ƙungiyar Tsofaffin Ƴan Majalisu ta Ƙasar ne ta shigar da ƙarar.
Sai dai rahotanni sun ce kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta dakatar da aiwatar da hukuncin inda ta umarci INEC da kada ta ɗauki wani mataki na soke rajistar jam'iyyun har sai an kammala sauraron ƙarar da suka shigar kan hukuncin da kotun ƙasa ta yanke.
Faisal Kabir mai magana da yawun jam'iyyar ADC ya ce "INEC ce ta shigar da ƙorafin a kotun ɗaukaka ƙara kuma ta tuntuɓe su kafin shigar da ƙarar".
Jam'iyyun dai sun yi watsi da hukuncin tare da shan alwashin ƙalubalantar matakin, inda suka ce hukuncin ya ci karo da abin da yake a zahiri.
Abi da hukuncin yake nufi
A hukuncin da mai shari'a Peter Lifu, ya yanke a babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya umurci INEC da kada ta bari waɗannan jam'iyyu su shiga duk wasu zaɓuka masu zuwa, ciki har da babban zaben shekarar 2027, sai dai idan sun cika duk wata ƙa'ida da doka ta tanada.
Barista Aminu Abdulrasheed, ya ce kotun ta yi la'akari ne da kundin tsarin mulki sashe 225(A) da kuma sashe na 25(4) na kundin dokokin zaɓe na 2022.
Ya ce sashen ya ba hukumar zaɓe iko ta cire jam'iyyar da ka gaza cika sharuɗɗan, wanda saboda shi ne wasu tsoffin ƴan majalisar wakilai ta ƙasar suka shigar da ƙara a kai.
"Hukuncin ya yi daidai da duk tanade-tanaden da ke cikin kundin tsarin mulki na 1999," in ji Lauyan da ke nazari kan harkokin da suka shafi siyasa da lamuran yau da kullum.
Sai dai Faisal ya ce ita kanta INEC na ganin za a ɓata mata shiri idan aka yi wannan hukuncin yanzu, shi ya sa ta ƙalubalanci matakin inda za a ci gaba da shari'ar da ke gabanta.
Masana siyasa na ganin wannan hukuncin na iya kawo tsaiko ga jam'iyyun adawa a ƙasar, amma idan suka ɗauki matakin da ya dace da wuri za su yi wa tufkar hanci.
Farfesa Kamilu Sani Fagge, masani harkokin siyasa na ganin irin waɗannan abubuwan da ke faruwa na nuna yadda ake yi wa fannin shari'a katsalandan.
"Idan kotu na ba da hukunce-hukunce da ke cin karo da dokokin, to gaskiya hakan na nuna dimokraɗiyyarmu na da matsala," in ji shi.
Wane zaɓi ya rage wa jam'iyyun?
Jam'iyyar ADC dai ta ce za ta ƙalubalanci hukuncin a kotu.
Barita Abdulrasheed ya ce: "Idan aka yanke hukunci a shari'a, wanda bai gamsu ba yana ganin akwai kura-kurai, yana da haƙƙi ko ƴanci na ya ɗaukaka ƙara ya faɗi abin da yake ganin ya dace kotun gaba ta kalla domin ganin ko ya yi daidai da tanade-tanaden shari'o'i".
"Tun yanzu INEC idan ta ga dama za ta bi umurnin kotu saboda shi ne a ƙasa yanzu... idan kuma a wajen ɗaukaka ƙara aka shigar da roƙon kotun ta dakatar da zartar da wannan hukuci har sai an saurari shari'ar, to a nan ne INEC za ta jira," i ji Barista Abdulrasheed.
Farfesa Kamilu Sani Fagge na ganin tun da jam'iyyar ADC na da damar ƙalubalantar hukuncin, tana kuma iya haɗa ƙarfi da yankunan kudu da sauran jam'iyyun adawar da su ma irin wanan hukuncin zai iya shafarsu.
Farfesa Fagge ya ce jam'iyyun na da zaɓi biyu a yanzu. Su ɗaukaka ƙara kan matakin sannan ta buƙaci a dakatar da aiwatar da wannan hukunci tun da "bayanai sun tabbatar da cewa, ADC da wasu jam'iyyu sun lashe zaɓe a 2023."
"Zanga-zanga duk ba mafita ba ce, su ma su je kotu su ɗauki mataki don su ƙwato wa kansu haƙƙi".
Dama jam'iyyar ADC na fuskantar wata shari'ar da ta shafi rikicin shugabanci, inda har wata kotu ta taɓa ba da umurnin cire sunayen shugabanninta sakamakon ƙarar da Nafiu Bala ya shigar kan shugabancin David Mark.
Daga bayan ne aka maida sunayen shugabannin ƙarƙashin David Mark ɗin bayan da kotun ƙoli ta soke matakin da kotun tarayyar ta yi da farko, inda yanzu suka koma kotun ta ƙasa domi ci gaba da shari'ar.
Mataki na gaba
Jam'iyyar adawa ta ADC ta fitar da sanarwar watsi da hukuncin, inda ta buƙaci magoya bayansu da su kwantar da hankalinsu tare da tabbacin cewa za su shiga zaɓen 2027.
Sanarwar da Mallam Bolaji Abdullahi ya fitar ta zargi jam'iyya mai mulki da maƙarƙashiya wajen ganin ta murƙushe ƴan adawa.
Jam'iyyun dai sun musanta cewa ba su samu kujeru a zaɓukan 2023 ba. ADC ta bayyana hukuncin a matsayin wani yunƙuri na amfani da kotu domin raunana tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya.
ADC ta ƙara da cewa INEC ta bayyana a gaban kotu cewa jam'iyyar ba ta karya wata doka ba, kuma ta cika dukkan sharuɗɗan da ake buƙata.
Haka kuma jam'iyyar ta zargi kotun da karya tsarin shari'a, tana mai cewa an ci gaba da sauraron karar duk da umarnin kotun daukaka kara na dakatar da shari'ar, lamarin da ta ce na iya haifar da rikicin siyasa a kasar.
Sai dai Barista Abdulrasheed ya ce makomar ƴan takarar jam'iyyun da abin ya shafa na cikin ƙalubale, domin ba a san me kotun ɗaukaka ƙara za ta yi, abin da ke nufin ba su da wata madafar yin takara a ciki.
"Idan aka soke waɗannan jam'iyyun, ba su da wani tudun dafawa. A siyasance su kalli wace makoma ce ta rage musu. Domin ko ɗaukaka ƙarar suka yi, lokaci ne ke ƙure musu."
APC ke kunna wutar rikici a jam'iyyun adawa - ADC
A baya dai jama'iyyar hamayya ta ADCn ta sha nananta cewa jam'iyya mai mulki ta APC ce ke haddasa rikice-rikicen a cikin jam'iyyun adawa.
Faisal Kabir, jami'i ne a ofishin watsa labarai na jama'iyyar ta ADC bangaren David Mark, ya shaidawa BBC cewa ''akwai wasu mutane a cikin wannan gwamnatin ta APC da suka matsa wa shugaban hukumar zaɓe ka dolen dole sai ya kawo cikas a cikin shugabancin jam'iyyar ADC.''
Ya yi zargin cewa masu wannan matsin lamaba ga shugaban hukumar zaɓen sun yi nasarar shawo kansa bayan ɗaukar lokaci ana kai-komo, shi ya sa har ya amince da cewa a yanzu ba zai yarda da shugabancin dukkan ɓangarorin biyu ba, har zuwa lokacin da za a kammala shari'a.
''tun daga lokacin da aka ga mutane suna tururuwa suna shiga wannan jam'iyya tamu ta ADC, hankalin gwamnatin Tinubu ya tashi, ta san cewa ƴan Najeriya ba za su bari ta tsallake shekarar 2027 ba, duba da halin da suka sa Najeriya a ciki. Don haka wannan firgici ne da tsoro ya sa gwamnati ke ƙoƙarin lallai sai shugaba Tinubu ya rasa wanda zai kara da shi a zaɓen 2027.'' In ji Faisal Kabir.
Rikicin shugabancin jam'iyyar ADC ya kunno kai ne a watan Yulin 2025 lokacin da shugabannin jam'iyyar suka yi murabus, kuma David Mark ya zamo sabon shugaba na riƙon ƙwarya, inda aka zaɓi sauran ƴan kwamitin zartarwa babu hamayya.