Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 17 ga watan Yuni 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Jagororin jam'iyyun adawa na farin ciki kan hukuncin kotun ƙoli

    Jagororin jam’iyyun adawa na ci gaba da bayyana farin cikinsu kan hukuncin da kotun ƙoli ta yanke na dakatar da aiwatar da hukuncin da kotun tarayya ta yanke na soke rajistar wasu jam’iyyun siyasa a ƙasar.

    Kotun ƙolin da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin da Alkali Peter Lifu ya yanke, wanda ya umarci hukumar zaɓe ta ƙasa INEC da ta soke rajistar jam’iyyun ADC da APP da AA da AP da ZLP.

    A hukuncin nata, kotun ta zargi alƙalin da saɓa wa umarnin da ta bayar tun farko, inda ta ce ya yi watsi da umarnin dakatar da sauraron shari’ar da kuma nuna halin girman kai a tsarin shari’a.

    Kotun ta bayyana matakin a matsayin mafi girman raini ga tsarin shari’a tana mai cewa alƙalin ya nuna halin rashin ladabi a aikin shari’a bisa ci gaba da shari’ar duk da umarnin da aka riga aka ba shi.

    A sakamakon haka, kotun ɗaukaka ƙolin ta amince da buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin, tare da umartar cewa a dakatar da duk wani mataki na aiwatar da hukuncin har sai an kammala sauraron ƙarar gaba ɗaya.

    A baya dai, kotun babbar tarayya ta umarci INEC da ta soke rajistar jam’iyyun biyar, bisa zargin gazawarsu wajen cika sharuddan ƙundin tsarin mulki da ke ba su damar ci gaba da kasancewa a matsayin jam’iyyun siyasa a ƙasar.

  2. Kuɗaɗen kira da saƙonnin waya na iya ƙaruwa a Najeriya

    Kuɗaɗen kira da saƙonnin waya a Najeriya na iya ƙaruwa, bayan da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta fara duba farashin haɗin gwiwar kamfanonin sadarwa, karo na farko cikin shekaru takwas.

    Farashin da ake kira Mobile Termination Rate shi ne kuɗin da wani kamfanin sadarwa ke biyan wani idan abokin hulɗarsa ya yi kira zuwa wata hanyar sadarwa daban, kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen tsara farashin kira da saƙonni.

    A halin yanzu, wannan farashi yana tsakanin naira 3.90 zuwa naira 4.70 a minti ɗaya, kuma masana na cewa duk wani ƙarin da aka yi zai iya jawo ƙarin kuɗi ga masu amfani.

    Sun kuma bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki kamar faduwar darajar naira, hauhawar farashi da tsadar kayan aiki tun daga 2018 ne suka sa ake wannan bita, domin farashin ya dace da yanayin da ake ciki a yanzu.

  3. Tankokin Iran uku sun kaucewa shingen da sojojin ruwan Amurka suka yi

    Shafukan da ke sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa sun bayar da rahoton cewa tankokin mai uku na Iran sun kaucewa shingen ruwan da rundunar sojan ruwan Amurka ta kafa, karo na farko cikin watanni biyu.

    Binciken BBC Verify ya tabbatar da cewa tankokin, waɗanda ke ƙarƙashin takunkumi kuma mallakin Kamfanin Tankokin Mai na Iran, sun ketare layin shingen ɗauke da mai gabaɗaya, kafin su shiga Tekun Arabian Sea.

    Rahoton ya ƙara da cewa duk da cewa na’urorin da ke nuna matsayin tankokin suna aiki, ba sa bayyana inda suke nufa, abin da ke nuna yadda ake ci gaba da safarar mai duk da tsauraran takunkuman da ake fuskanta.

  4. 'Za a kafa wa Iran gidauniya ta dala biliyan 300 domin farfaɗo da tattalin arziƙinta

    Rahoton Reuters ya nuna cewa yarjejeniyar da ke tsakanin Amurka da Iran ta ƙunshi kafa wani wata gidauniyar zuba jari ta dala biliyan 300 ga Iran, inda sama da rabin kuɗin an riga an yi alƙawarin samar da shi daga kamfanoni masu zaman kansu.

    Majiyar da ta san batun ta ce an tsara gidauniyar ne domin samar da ƙarfafawar tattalin arziki ga ɓangarorin biyu domin kai wa ga yarjejeniya ta ƙarshe, kuma za a kira shi “gidauniyar gyarawa da cigaba”.

    Rahoton ya ƙara da cewa wannan gidauniyar ba na gwamnati ba ne, kuma ba ya ƙunshe da tallafin kuɗi daga gwamnatoci, sai dai kamfanoni daga Amurka, ƙasashen Gulf, Asiya, Afirka da Kudancin Amurka ne za su zuba jari.

    Zuba jarin da ake sa ran yi zai haɗa da fannoni kamar makamashi, sufuri, lodawa da sauke kaya da kuma masana’antu.

    Wata babbar majiya daga Iran ta ce Tehran ta fara neman dala biliyan 400 a matsayin diyya daga Amurka, amma Washington ta ƙi, wanda ya sa aka samar da wannan tsari na gidauniyar.

    Rahoton ya kuma nuna cewa wannan tsarin ya bambanta da tattaunawar da ake yi kan ɗage takunkumi da kuma sakin kadarorin Iran da aka daskare, kuma ba zai fara aiki ba sai an cimma cikakkiyar yarjejeniya mai gamsarwa.

    A cewar rahotanni, Iran za ta ci gajiyar wannan gidauniyar ne kawai idan ta cika wasu sharuɗɗa, ciki har da dakatar da shirinta na nukiliya.

  5. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Laraba daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.