Mahukunta sun tabbatar da mutuwar yara ƴan makaranta aƙalla 24, a lokacin da suke ƙoƙarin tserewa daga gobarar da ta tashi a cikin wasu makarantu biyu, a birnin Bukavu da ke gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, lamarin da ya janyo ruɗani sosai.
An kuma bayar da rahoton mutuwar wasu manya a wajen, yayin da hukumomi ke bayyana fargabar ƙaruwar yawan mutanen da za gobarar ta kashe saboda akwai wasu da aka garzaya da su asibiti domin duba lafiyar su.
Hotunan da aka yaɗa na wajen da abin ya faru sun nuna ƙananan yara a kwance a ƙasa, a cikin asibiti, suna kuka saboda tsananin azabar ƙunar wuta.
Gidaje 300 wutar ta ƙona, kuma har yanzu ba a gano abin da ya tayar da ita ba.
Mahukunta sun ce lamarin ya faru ne a birnin Bukavu da ke gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo da ke ƙarƙashin ikon ƴan tawaye, inda ake fama da cunkoson jama'a.
Bayanan da mayaƙan ƴan tawaye da ke iko da wajen suka fitar sun nuna cewa mutanen da suka rasu sun kai 24, amma akwai fargabar adadin zai ƙaru.
Hotunan da aka yaɗa a kafafen sada zumunta sun nuna ƙananan yara kwance a ƙasa, kuma da alama gawarwaki ne.
Shaidun da kamfanin dillanci labarai na Reuters ya zanta da su sun ce tun da rana aka kashe wutar, amma ana ci gaba da ganin hayaƙi da ke ɓullowa daga ƙarƙashin gine-ginen da aka rusa domin kashe gibarar.
Bukavu, babban birnin kudancin lardin Kivu kuma yankin da ya fi cunkoson jama'a a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ya faɗa a ƙarƙashin ikon mayaƙan tawaye na M23 ne a watan Faburairun bara.
Amma gwamnati a Kinshasa ta wallafa sanarwa a shafin X, ba tare da ta bayyana yawan mutanen da gobarar ta kashe ba.
Sanarwar ta ce "Ma'aikatar ilimi da kula da ƴan ƙasa ta bayyana damuwa matuƙa kan mummunar gobarar da ta tashi,''
"An yi asarar rayuka da yawa kuma wasu da dama sun ji rauni. Ministan Ilimi na aikewa da ta'aziya ga iyalan waɗanda lamarin ya ritsa da su, kuma ya bayar da umarnin tantance halin da makarantun da abin ya shafa suke ciki, tare da tabbatar da ganin an ci gaba da harkokin karatu.''
Gobarar biyu sun faru ne bayan wata gobarar ta daban a ƙarshen makon da ya gabat a Kinshasa, inda aka samu asarar rayuka wajen turereniyar neman guduwa daga gobarar da ta tashi a wajen wani ɗakin taro ana tsakiyar biki.
Gwamnatin ƙasar ta bayar da umarnin tsaurara matakan rigakafi, kuma ta tura jami'ai a sannan ƙasar domin sanya ido da tabbatar da kaucewa tashin gobara a wuraren da mutane ke taruwa.