Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sauran sassan duniya, Asabar, 25/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo mulu labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sauran sassan duniya, Asabar, 25/04/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Amurka ta gargaɗi 'yan kasarta da ke zaune a Mali

    Rundunar sojin Mali ta ce ƴanbindiga sun ƙaddamar hare-haren haɗin gwiwa a birane da dama da suka haɗa da Bamako baban birnin ƙasar.

    Ƴan tawayen Azwad sun sanar da ƙwace muhimman yankuna a birnin Kidal bayan rahoton ɓarkewar rikici a Gao.

    Wasu rahotanni da ba a tantance ba sun ce, wata ƙungiya mai alaka da al'Qaeda wadda a baya bayan nan ke neman haɗin kan yan tawayen Azawad na cikin rikicin.

    Tuni ofishin jakadancin Amurka a Bamako ya gargadi Amurkawa mazauna Mali su nemi mafaka.

  2. Jam'iyyun adawa a Najeriya sun amince su fidda ɗan takara ɗaya a 2027

    Shugabannin jam'iyyun adawa a Najeriya sun sanar da shirinsu na haɗewa guri guda domin fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda a zaɓen 2027 mai zuwa.

    An yarda da wannan shawarar ne a wani taron shugabannin jam'iyyun adawa da ya gudana a Ibadan babbab birnin Oyo.

    Taron wanda gwamnan na jihar Oyo Sheyi Makinde ya jagoyanta, an gudanar da shi ne a ɗakin taro na Banquet Hall da ke gidan gwamnatin jihar.

    Jagorori daga jam'iyyar PDP da ADC da kuma NNPP sun halarta har da sauran wasu jam'iyyun.

    Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo aka tsara zai jagoranci taron, sai dai kuma bai samu halartar taron ba.

  3. 'Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a Lebanon sun kai 2,496'

    Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce adadin mutanen da Isra'ila ta kashe tun daga ranar 2 ga watan Maris zuwa yau ya kai 2,496.

    Cikin wata sanarwa da ta fitar a yau, ma'aikatar tace adadin waɗanda hare-haren Isra'ilan suka jikkata sun kai 7,725.

    Isra'ila ta ƙi dakatawa da kai hare-hare Lebanon, duk da cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran, ko da yake tace yarjejeniyar ba ta haɗa da Hezbollah da take kaiwa hare-hare ba.

    Ana ta yunkurin ƙara tattaunawa tsakanin Iran da Amurka wadda Pakistan ke shirin karɓar baƙunci a karo na biyu.

  4. Mu 'yan siyasa ba ma yi wa talakawa adalci - Sanata Ningi

    Sanata Abdul Ahmed Ningi mai wakiltar Bauchi ta tsakiya ya ce 'yan siyasa ba sa yi wa talakawan da suke jagoranta adalci da yau ba a tsinci kai inda ake ba.

    Sanata Ningi ya bayyana haka ne yayin wata hira da ya yi da BBC Hausa, inda ya ce lokutan kamfe 'yan siyasa na shiga lungu da saƙo domin neman ƙuri'un talakawa, amma da zarar sun ci zaɓe ba sa komawa domin sanin halin da talakawan ke ciki.

    "Ana ta kashe talakawan da muke wakilta, amma babu abin da yake gabanmu a yanzu sai lamuran zaɓe da siyasa", in ji Sanata Ningi.

    Ya ce a kullum sai ka ji rahoton kashe mutane a sassan arewacin Najeriya, kamar wadanda ba su da shugabanni.

    "Shi yasa muka nemi majalisa ta sa a dakatar a dakatar da harkokin siyasa a jihohi 8 na arewa da suka fi shiga wannan matsala har sai an shawo kan matsalar,".

  5. Labarai da dumi-dumi, Trump ya soke zuwan wakilan Amurka tattaunawar Islamabad

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya tabbatar da soke bulaguron wakilansa zuwa Islamabad domin tattaunawa da wakilan Iran da nufin kawo ƙarshen yaƙin.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Trump ya ce: "Na soke tafiyar wakilaina zuwa birnin Islamabad domin tattaunawa da wakilan Iran don kawo ƙarshen yaƙin ƙasar''.

    "An ɓata lokaci mai yawa a wannan bulaguro, ana ta kwan gaba kwan baya''.

    "Baya ga haka, akwai saɓani da rashin tabbas a tsakanin shugabanninsu, ba wanda ya san wa ke da iko, ciki har da su shugabannin'', in ji shi.

    "Kuma mu mun shirya, amma su ba su shirya ba, idan suna buƙatar tattaunawar, sa kira mu'', a cewar Shugaba Trump.

  6. Fatanmu shi ne sake buɗe mashigar Hormuz - Macron

    Shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron ya ce yana ƙoƙarin ganin an sake buɗe mashigar Hormuz.

    Yayin da yake jawabi a taron manema labarai a birnin Athens na ƙasar Girka, Mista Macron ya ce tsoro da firgicin da ake ciki a yankin ne ya haifar da ƙarancin makamashin.

    ''Fatanmu shi ne sake buɗe mashigar Hormuz cikin ƴan kwanaki ko makonni masu zuwa tare da bai wa jirage damar wucewa ba tare da matsalar ba'', in ji shi.

    Ya ci gaba da cewa bayan sake buɗe mashigar al'amura za su daidaita.

    Mashigar ta kasance a rufe tun bayan fara yaƙin Iran da Amurka da kuma Isra'ila, inda aka hana jiragen dakon kayayyaki wucewa ta mashigar.

    Lamarin da ya kawo tsaiko ga fiton kayayyakin da suka haɗa da man fetur da kayayyakin abinci da magunguna da takin zamani.

  7. 'Ministan harkokin wajen Iran ya bar Islamabad bayan tattaunawa'

    Kamfanin dillancin labaran Iran, IRNA ya bayar da rahoton cewa ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Araghchi ya fice daga Islamabad.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa wani hoto na jerin gwanon motocin da aka ce na Araghchi ne da ke kan hanyar barin Pakistani.

  8. Iran ta yi barazanar mayar da martani idan Amurka ta ci gaba da datse tasoshin ruwanta

    Dakarun tsaron Iran sun yi barazanar mayar da martani idan Amurka ta ci gaba da datse tasoshin ruwanta a mashigar Hormuz.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar da dama sun ambato wata sanarwa daga rundunar sojin ƙasar na cewa dakarunta za su mayar da martani idan Amurka ta ci gaba da datse tasoshin ruwanta.

    A baya-bayan nan Amurka ta kama wasu jiragen ruwan Iran bayan fara rufe tasoshin ruwan Iran a ranar 13 ga watan Afrilu.

  9. Iran ta bayyana wa Pakistan matsayinta kan kawo ƙarshen yaƙin ƙasar

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya fitar da wata sanarwa bayan ganawarsa da babban hafsan sojin Pakistan, Asim Munir.

    Sanarwar ta bayyana cewa sun tattauna ''batutuwa masu muhimmanci dangane da yarjejeniyar tsagaita wutar'' tsakanin Iran da Amurka.

    Haka ma sanarwar ta ce Araghchi ya bayyana wa Pakistan matsayinta da shawarwarinta kan kawo ƙarshen yaƙin.

    Sanarwar ta ƙara da cewa Asim Munir ya ce Pakistan a shirye take ta ci gaba da aikinta na shiga tsakani.

  10. Su wane ne wakilan Amurka a tattaunawarta da Iran?

    Steve Witkoff: Jakadan Amurka na musamman, Steve Witkoff, wanda amini ne ga Shugaba Trump kuma ƙwararren jami'in diplomasiyya.

    Ya taka muhimmiyar rawa a manyan al'amuran duniya ciki har da batun tsagaita wuta a yaƙin Gaza da na Ukraine.

    Jered Kushner: Suruki ne ga shugaba Trump, shi ma ya ƙware a fannin diplomasiyya.

    Ya taka rawar gani a diplomasiyyar yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da yarjejeniyar Abraham Accord.

    Kusher na gudanar da harkokinsa tsakanin kasuwanci da siyasar duniya.

  11. Isra'ila da Hezbollah sun ci gaba da musayar wuta

    Rundunar sojin Isra'ila, (IDF) ta ce ta kai hari kan motocin harba rokokin Hezbollah cike da makamai cikin dare a wurare har guda uku a kudancin Lebanon.

    IDF ta ce motocin harba rokokin "barazanar ce ga" sojojin IDF da kuma fararen hular Isra'ila, don haka za ta ci gaba da aiki domin kawar da duk waɗannan barazanar.

    A ɗaya ɓangaren kuma, Hezbollah ta bayyana cikin wata sanarwa da ta fitar a safiyar yau cewa ta kai hari kan sojojin Isra'ila.

    Hakan na zuwa ne bayan tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninsu da mako uku, kamar yadda shugaban Amurka ya bayyana.

    Duka ɓangarorin biyu na zargin juna da saɓa wa yarjejeniyar.

  12. 'Araghchi bai je Pakistan don tattauna batun nukiliya ba'

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ba zai "tattauna abin da ya shafi nukiliyar Iran'' a lokacin bulaguronsa zuwa Pakistan ba, kamar yadda shugaban kwamitin tsaron Iran ya bayyana.

    Yayin zantawarsa da manema labarai a birnin Tehran cikin daren da ya gabata, Ebrahim Azizi ya ce Araghchi na birnin Islamabad ne kawai domin tattauna batun ''ƙawancen ƙasashen biyu''.

    Azizi - wanda tsohon kwamanda ne a rundunar juyin juya halin ƙasar (IRGC) - ya ce tattaunawa game da nukiliyar Iran na ci gaba da kasancewa ''ɗaya daga cikin batutuwan da Iran ba ta sako-sako da su''.

    Amurka na kira ga Iran ta kawo ƙarshen shirin nukiliyarta, tana mai jaddada cewa hakan na cikin yarjejeniyar ƙarshe da za a cimma domin kawo ƙarshen yaƙin.

  13. Labarai da dumi-dumi, 'Ƴanbindiga sun ƙaddamar da hare-haren haɗin gwiwa a faɗin Mali'

    Rundunar sojin Mali ta ce ƴanbindiga sun ƙaddamar hare-haren haɗin gwiwa a faɗin ƙasar, ciki har da Bamako babban birnin ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da rundunar sojin ƙasar ta fitar a ranar Asabar da safe, ta ce har yanzu ana ci gaba da faɗa tsakanin sojoji da ƴanbindigar.

    ''Yanzu haka dakarun tsaronmu na fafatawa da ƴanbindigar domin daƙile hare-haren'', kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Shaidu sun faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sun riƙa jin ƙarar abubuwan fashewa da asubahin ranar Asabar a yankin Kati, wani babban sansanin soji da ke wajen birnin Bamako.

    Tuni aka girke sojoji domin toshe titunan yankin.

    An kuma samu rahotonnin hare-hare a yankin Gao da ke arewa maso gabashin ƙasar da kuma yankin Sevare da ke tsakiyar ƙasar.

    Ƙasar Mali na ƙarƙashin mulkin soji, wadda Janar Assimi Goïta ke jagoranta bayan ƙwace mulki a 2020, inda ya yi alƙawarin maido da tsaro tare da kawar da ƙungiyoyin ƴanbindiga, to amma har yanzu ƙasar na ci gaba da fuskantar hare-haren ƴanbindigar.

  14. Iran ta gabatar da tayi kuma za mu duba - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce Iran ta gabatar da tayi, amma kuma Amurka za ta duba ta gani, ko za ta iya amincewa da tayin.

    Mista Trump ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ''kawo yanzu ba mu san abin da tayin nasu ya ƙunsa ba''.

    Yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labaran ta waya, bai yi cikakken bayani kan yadda tattaunawar ɓangarorin biyu za ta kasance ba.

    Sai dai ya ce tawagarsa za ta ƙulla yarjejeniya ce da ''mutanen da ke riƙe da ikon Iran a hannunsu yanzu''.

    Shugaban na Amurka ya ƙara da cewa Iran na buƙatar tattaunawa domin kawo ƙarshen yaƙin.

    Ya ƙara da cewa Iran na shirin gabatar da tayin da nufin magance buƙatun Amurka.

  15. Isra'ila da Hezbollah na zargin juna da saɓa wa yarjejeniya

    Sojojin Isra'ila da ƙungiyar Hezbollah na zargin juna da saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta taimaka aka cimma tsakaninsu.

    Rundunar IDF ta ce saɓa yarjejeniya ta baya-bayan nan da Hezbollah ta yi, shi ne tura jirage marasa matuƙa ɗauke da abin fashewa zuwa kan sojojinta a kudancin Lebanon.

    "Wannan abu ya ƙara nuna saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma'', in ji IDF, inda ta ƙara da cewa ba a samu raunuka a lamarin ba.

    A nata ɓangar, Hezbollah ta ce ta aika jiragen marasa matuƙa ne har sau biyar kan sojojin Isra'ila a ranar Juma'a, a matsayin ''martani kan saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wutar da sojojin Isra'ilar suka yi''.

  16. Hotunan yadda Pakistan ta tsaurara tsaro gabanin tattaunawar Iran da Amurka

    Tehran ta ce ba za ta yi tattaunawar gaba da gaba da Amurka ba, amma wakilan ƙasar na birnin Islamabad domin tattaunawa da Pakistan.

    Yanzu haka dai tawagar Amurka na kan hanyar zuwa birnin na Islamabad .

    Pakistan ta tsaurara matakan tsaro, tun bayan da Donald Trump ya ce wakilansa za su koma ƙasar domin ci gaba da tattaunawar.

    Ga wasu daga cikin hotunan yadda ƙasar ta tsaurara tsaro a wannan safiya.

  17. Tawagar Iran ta gana da babban hafsan tsaron Pakistan

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi na ganawa da babban hafsan tsaron Pakistan, Field Marshal Asim Munir.

    Araghchi ya ce bayan ganawar ta Pakistan, zai kuma yi bulaguro zuwa ƙasashen Oman da Rasha.

    Makasudin ganawar, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, shi ne ''tattaunawa da ƙawayenmu kan abubuwan da suka shafi ƙawance da ci gaban yankinmu.''

  18. Assalamu alaikum

    Masu bin wannan shafi na kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku domin kawo muku halin da duniya ke ciki musamman batun ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin Iran.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.