Mutum 24 sun mutu a Ondo bayan shan giya
Akalla mutum 24 ne suka mutu bayan da ake zargin sun sha wata barasa da ake haɗawa a gida a ƙaramar hukumar Odigbo ta jihar Ondo.
Gwamnatin jihar ta ce ta ƙaddamar da bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa mutuwar mutanen, wadanda suka mutu tsakanin ranar 3 zuwa 7 ga watan Satumban 2026.
Ma’aikatar Lafiya ta jihar ta ce sakamakon binciken farko ya nuna cewa lamarin na da alaƙa da shan ɓarasa da ake hada wa a gida, wanda aka fi sani da “Monkey Tail”.
Mazauna yankin sun ce wasu daga cikin wadanda suka mutu sun rasu ne a gidajensu, yayin da wasu kuma suka mutu cikin barci.
Kwamishinan Lafiya na jihar Ondo, Dakta Banji Ajaka, ya ce hukumomi na daukar lamarin da matukar muhimmanci, sai dai yaƙi bayyana taƙamaiman sinadarin da ake zargin ya haddasa mutuwar inda ya ce sai an kammala binciken likitoci da gwaje-gwajen dakin bincike.
A halin yanzu, shugaban karamar hukumar Odigbo, Taiwo Adegoroye, ya sanya dokar hana sayarwa da shan barasa da ake haɗa wa a gida na tsawon wata guda a yankin, a matsayin matakin kariya.
Adegoroye ya ce wani bincike na farko da ma’aikatan lafiya na karamar hukumar suka gudanar, wanda ya hada da tambayoyi kan yanayin mutuwar wadanda abin ya shafa, ya nuna yiwuwar alaka tsakanin mace-macen da shan wasu abubuwan da ake samarwa a gida.
Ya ce: “An dauki matakin ne domin kare lafiyar jama’a yayin da hukumomin da abin ya shafa ke ci gaba da bincike kan lamarin.”
Ya ce ana ci gaba da gudanar da binciken sinadarai masu guba domin gano ainihin abin da ya haddasa mace-macen, tare da gargadin cewa duk wanda aka kama yana sayarwa ko rarraba abubuwan shan da aka haramta a lokacin dokar zai fuskanci kamawa da gurfanar da shi a gaban kotu.
An gano cewa mace-macen sun faru ne a garuruwan Araromi-Obu, Orita New Town da Odigbo, yayin da wasu mutane da dama ke karbar magani a asibitoci.