Yadda wani jirgin ruwa ya kama da wuta a tsakiyar tekun Philippines
Asalin hoton, Philippine Coast Guard
Hukumar tsaron gabar teku ta Philippines ta ce aƙalla mutum biyar ne suka mutu bayan wata gobara ta tashi a cikin wani jirgin ruwa na fasinja.
Hukumar ta ce sama da mutum 80 har yanzu ba a gano inda suke ba bayan gobarar da ta rutsa da jirgin MV June Aster, wanda ke kan hanyarsa daga birnin Manila zuwa tsibirin yawon buɗe ido na Coron a lardin Palawan.
Wakilin BBC ya ce akwai tambayoyi da dama kan yadda irin wannan abu zai faru Wani bidiyo da hukumar tsaron gabar tekun ta wallafa a intanet ya nuna jirgin gaba ɗayansa ya kama da wuta, yayin da ake ciro wasu fasinjoji daga cikin ruwa. Daga baya, hukumar ta bayyana cewa an ceto fiye da mutum 40 daga cikin waɗanda ke cikin jirgin.
Mutum 24 sun mutu a Ondo bayan shan giya
Asalin hoton, Getty Images
Akalla mutum 24 ne suka mutu bayan da ake zargin sun sha wata barasa da ake haɗawa a gida a ƙaramar hukumar Odigbo ta jihar Ondo.
Gwamnatin jihar ta ce ta ƙaddamar da bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa mutuwar mutanen, wadanda suka mutu tsakanin ranar 3 zuwa 7 ga watan Satumban 2026.
Ma’aikatar Lafiya ta jihar ta ce sakamakon binciken farko ya nuna cewa lamarin na da alaƙa da shan ɓarasa da ake hada wa a gida, wanda aka fi sani da “Monkey Tail”.
Mazauna yankin sun ce wasu daga cikin wadanda suka mutu sun rasu ne a gidajensu, yayin da wasu kuma suka mutu cikin barci.
Kwamishinan Lafiya na jihar Ondo, Dakta Banji Ajaka, ya ce hukumomi na daukar lamarin da matukar muhimmanci, sai dai yaƙi bayyana taƙamaiman sinadarin da ake zargin ya haddasa mutuwar inda ya ce sai an kammala binciken likitoci da gwaje-gwajen dakin bincike.
A halin yanzu, shugaban karamar hukumar Odigbo, Taiwo Adegoroye, ya sanya dokar hana sayarwa da shan barasa da ake haɗa wa a gida na tsawon wata guda a yankin, a matsayin matakin kariya.
Adegoroye ya ce wani bincike na farko da ma’aikatan lafiya na karamar hukumar suka gudanar, wanda ya hada da tambayoyi kan yanayin mutuwar wadanda abin ya shafa, ya nuna yiwuwar alaka tsakanin mace-macen da shan wasu abubuwan da ake samarwa a gida.
Ya ce: “An dauki matakin ne domin kare lafiyar jama’a yayin da hukumomin da abin ya shafa ke ci gaba da bincike kan lamarin.”
Ya ce ana ci gaba da gudanar da binciken sinadarai masu guba domin gano ainihin abin da ya haddasa mace-macen, tare da gargadin cewa duk wanda aka kama yana sayarwa ko rarraba abubuwan shan da aka haramta a lokacin dokar zai fuskanci kamawa da gurfanar da shi a gaban kotu.
An gano cewa mace-macen sun faru ne a garuruwan Araromi-Obu, Orita New Town da Odigbo, yayin da wasu mutane da dama ke karbar magani a asibitoci.
Zan ba kowane ɗan Amurka dala 5,000 idan jam'iyyarmu ta samu nasara a zaɓe - Trump
Asalin hoton, Reuters
Shugaban Trump, na Amurka ya ce zai bai wa kowane babba ɗan ƙasar dala 5,000 idan jam'iyyarsa ta Republican ta samu rinjaye a duka majalisun dokokin ƙasar a zaɓukan rabin wa'adi da za a gudanar a watan Nuwamba.
Sai dai har yanzu babu cikakken bayani kan yadda za a samar da kuɗin da kuma cewa ko hakan bai saba wa doka ba.
Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron farko na jam'iyyar Republican da aka shirya domin zaɓukan tsakiyar wa'adi, inda ya yi ƙoƙarin ƙarfafa magoya bayansa gabanin zaɓukan da ake kallon suna da matuƙar muhimmanci.
Ya ce sharadi daya kawai ya ke da shi , shi ne dole ne a kashe kudin a Amurka duk da raguwar amincewar jama'a da shugabancinsa a wasu ƙuri'un jin ra'ayi, shugaban ya buƙaci mahalarta taron da su fito ƙwansu da kwarkwatarsu su kaɗa ƙuri'a, yana mai cewa su yi hakan kamar shi kansa ne ke takara a zaɓen.