Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Najeriya ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 490 a gidan yari da aka yanke wa tsohon shugaban bankin shige da fitar da kayayyaki a Najeriya na NEXIM, Robert Orya.
Kotun ta ce ta same shi da laifi kan tuhume-tuhume 49, inda aka yanke masa hukuncin shekaru 10 a kan kowanne tuhuma, wanda ya kai jimillar shekaru 490, kuma hukuncin zai gudana ne a lokaci guda.
Robert Orya ya rike muƙamin Manajan Daraktan bankin NEXIM tsakanin shekarar 2009 da 2016 a zamanin mulkin marigayi Shugaba Umaru Yar’Adua, sannan tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya sake naɗa shi a 2014.
Bayan ya bar muƙaminsa, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta gurfanar da shi a gaban kotu a shekarar 2021 kan tuhume-tuhume 49 da suka haɗa da karɓar kuɗi ta hanyar yaudara da zamba da suka kai naira biliyan 2.4.
A ranar 5 ga Fabrairu 2026, wata Babbar Kotun Babban Tarayya da ke Abuja ta same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 490 a gidan yari, wanda za a yi a lokaci guda.
A hukuncin da kwamitin alkalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙara suka yanke, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Muhammed Danjuma, kotun ta ce alkalin kotun farko, Mai Shari’a Messiri, ya yi daidai wajen yanke hukuncin.
Mai Shari’a Danjuma, tare da sauran alkalan biyu, Ntong Ntong da Ele Enenche, sun ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da tuhumar da ake yi wa Orya ba tare da wata tantama ba.