An gano gawar ƴan Nijar 50 da suka mutu a sahara

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun ce sun gano gawar aƙalla mutum 50 ta mutanen da suka rasu sakamakon ƙishirwa a cikin sahara.
Ayarin mutanen sun dawo ne daga wani taron addini daga ƙasar mali inda motarsu ta lalace a tsakiyar saharar.
Direban motar da fasinjojin sun kwashe kwanaki suna ƙoƙarin gyara motar sai dai daga bisani ruwan da suka yi guzuru ya ƙare masu.
Mutum biyu ne kaɗai daga cikin mutanen suka tsira bayan da suka kwashe sama da kilomita hamsin suna tafiya a ƙasa ba tare da sanar da hukumomi ba.
Tawagar masu aikin ceto sun binne mutanen a manyan kaburbura.




















