Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Confluence (Confluence
University of Science and Technology - CUSTECH), mallakin gwamnatin jihar Kogi
da ke tsakiyar Najeriya, ta kori ɗalibai biyu bisa zargin aikata luwadi.
Jami’ar ta ce amince da hukuncin ne bayan ta yi nazarin
shawarwarin Kwamitin Ladabtar da Ɗalibai.
A cikin wata
sanarwa da jami’ar ta fitar ranar Juma’a, ta ce:
“An kori ɗalibai
biyu saboda shiga harkar luwadi, sannan an dakatar da wasu ɗalibai huɗu na
tsawon zangon karatu daya saboda laifin faɗa a harabar jami’a.”
Jami’ar ta ce
an ɗauki waɗannan matakan ne kamar kundin dokokin dalibtaka na makarantar ya
nuna.
Mahukuntan jami’ar
sun ce za su ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da ladabi da kuma samar da
yanayi mai kyau na karatu.
Sun ƙara da
cewa ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar tsauraran matakan ladabtarwa kan
duk wani ɗalibi da aka samu da laifin karya dokoki da ƙa’idojin jami’ar.
Haka kuma jami’ar
ta bukaci ɗalibai su san dokokinta sosai tare da gudanar da kansu yadda ya
dace.
Najeriya na
cikin ƙasashen Afirka da har yanzu ke haramta alaƙar jinsi tsakanin masu jinsi ɗaya.
A shekarar 2014
ne aka sanya wa dokar Haramta Auren Masu Jinsi Ɗaya (Same-Sex Marriage
(Prohibition) Act) hannu, wadda ta tanadi daurin shekaru 14 ga duk wanda ya
yi aure ko wata alaka ta jinsi iri ɗaya.
Dokar ta kuma
haramta nuna soyayya a bainar jama’a tsakanin masu jinsi ɗaya, inda ta tanadi
hukuncin ɗaurin shekara 10.
Ƙungiyoyin kare
haƙƙin ɗan Adam sun sha sukar wannan doka, suna cewa ta ƙara tsananta wariya,
cin zarafin masu sha’awar aure ko alakar auren jinsi.
Wani rahoto na Human
Rights Watch ya ce dokar ta “halatta cin zarafin mutanen LGBT a hukumance,
lamarin da ya ƙara muni kan halin da suke ciki.”
Masu fafutukar
kare haƙƙin ɗan Adam sun ce har yanzu ana ci gaba da samun rahotannin
hare-hare, dukan jama’a da kuma yi wa mutanen LGBT baƙar fata domin karɓar kuɗi,
suna masu cewa dokar ta samar da yanayin da irin waɗannan cin zarafe-zarafen ke
faruwa ba tare da cikakken ɗaukar mataki ba.
A faɗin Afirka
kuwa, ƙasashe da dama sun ƙara tsaurara dokokinsu yaki da auren jinsi. Kasashe
irin su Ghana da Uganda da Burkina Faso duk sun tanadi matakai masu tsauri kan
masu harkar.