Atiku ya gargaɗi majalisa kan amincewa da sabon bashin Tinubu

Asalin hoton, Atiku/X
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya buƙaci Majalisar Dokokin Najeriya da kada ta amince da buƙatar sabon bashin da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar har sai Gwamnatin Tarayya ta bayyana cikakkun bayanan ayyukan da za a aiwatar da kuɗaɗen.
Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Atiku ya ce bai kamata majalisar ta amince da "ko dala daya tak" ba sai gwamnati ta fitar da bayanan kowane aiki, kwangila, kuɗin gudanarwa, sunan ɗan ƙwangila, sharuɗɗan bashin da kuma yadda za a biya bashin.
Ɗan takarar shugaban ƙasar na ADC ya bayyana hakan ne bayan Shugaba Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Dattawa domin karbar bashin dala biliyan 20.52 da kuma euro biliyan 1.045.
Sanarawar ta kuma ce Atiku ya ce wannan buƙatar ta tabbatar da gargaɗin da ya yi tun ranar 12 ga Oktoba kan shirin gwamnatin na neman bashin da zai kai kusan dala biliyan 20.
Ya kuma soki Shugaba Tinubu bisa rashin gabatar da cikakken bayani kan yadda za a kashe kuɗaɗen bashin, yana mai cewa ambaton manyan fannoni kawai bai isa ya tabbatar da dacewar neman irin wannan gagarumin bashi ba.





























