KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 29 ga watan Yulin 2026.

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • xxx
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi da Abdullahi Diginza

  1. Afirka ta Kudu na fuskantar ƙarancin ma'aikata bayan ficewar baƙi saboda ƙin jini

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Afirka ta Kudu na fuskantar ƙarancin ma’aikata bayan da fiye da baƙi 160,000 ne suka bar ƙasar sakamakon hare-haren da ake kai musu da kuma zanga-zangar ƙyamar da tsaurara matakan shige da fice.

    Lamarin ya fara shafar fannoni kamar noma, gine-gine, aikin gida da masana’antu, inda masu ɗaukar aiki ke kokawa kan rashin ma’aikatan da za su maye gurbin waɗanda suka tafi.

    Manoma da masu masana’antu sun ce ficewar ƙwararrun ma’aikatan ƙasashen waje na barazana ga yawan amfanin da suke samarwa, yayin da ƙungiyoyin ƙwadago ke zargin wasu kamfanoni da fifita baƙi saboda albashinsu ya fi rahusa.

    A halin yanzu, gwamnatin ƙasar na neman hanyar da za ta daidaita buƙatar samar da ayyukan yi ga ‘yan ƙasa da kuma buƙatar wasu sassa da ke dogaro da ma’aikatan ƙasashen waje.

    Yawancin waɗanda suka fice daga ƙasar sun ce sun yi hakan ne saboda tsoron hare-haren ƙin jinin baƙi da kuma farmakin jami’an tsaro kan waɗanda ba su da takardun zama.

  2. Iran ta musanta batun haɗa kai da Oman wajen kula da mashigar Hormuz

    Wani babban jami'in gwamnatin Iran ya musanta rahotannin da ke cewa ƙasar za ta haɗa kai da Oman wajen kula da mashigar ruwan Hormuz.

    A wata hira da kamfanin dillancin labarai na Reuters, jami'in ya bayyana cewa tsarin da zai bai wa Iran da Oman iko daidai wa-daida a kan mashigar ba ya cikin muradun Tehran, duk da muhimmancin dangantakar da ke tsakaninta da Oman.

    A ranar Talata ne Reuters ta ruwaito cewa Oman ta gabatar wa Iran da wata sabuwar shawara ta kafa tsarin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen yankin domin tafiyar da harkokin mashigar Hormuz.

    Rahoton ya ce shirin zai ba wa ƙasashen da suka shiga damar bayar da gudunmawa bisa raɗin kansu wajen gudanar da tsarin.

    Wata majiya daga yankin da ta nemi a ɓoye sunanta ta shaida wa Reuters cewa shawarar Oman ta samu goyon bayan wasu ƙasashen yankin.

    Sai dai jami'in na Iran ya tabbatar wa Reuters cewa ƙasarsa ba ta ganin tsarin haɗin gwiwar da aka gabatar zai yi daidai da manufofinta ko kuma ya kare muradunta a mashigar Hormuz.

  3. 'Iran ta sayi makamai masu linzami 300 zuwa 400 daga China'

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa Iran ta kulla yarjejeniya da China domin sayen makaman kare sararin samaniya da ake harbawa daga kafaɗa tsakanin guda 300 zuwa 400.

    Majiyoyi uku da suka san bayanan yarjejeniyar sun shaida wa Reuters cewa ana sa ran Iran za ta fara karɓar kason farko na waɗannan makamai cikin 'yan makonni masu zuwa.

    A cewar majiyoyin, darajar kwangilar ta kai dala miliyan 60 zuwa 70, kuma ana kallonta a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙoƙarin Iran na ƙarfafa kariyarta daga hare-haren jiragen sama.

    Sai dai wasu majiyoyin da ke da masaniya kan yarjejeniyar sun ce duk da an rattaba hannu kan kwangilar, har yanzu akwai yiwuwar sauye-sauye a jadawalin kai makaman, yawan da za a tura da kuma wasu bayanan aiwatar da ita.

    Sun ƙara da cewa bisa tsarin da Iran da China suka amince da shi, za a fara jigilar makaman ta jirgin sama daga birnin Urumqi da ke yammacin China, kafin daga bisani a bi ta Pakistan zuwa Iran.

    Wata majiya daga ɓangaren tsaron Turai ta shaida wa Reuters cewa jami'an ƙasarta suna sane yarjejeniyoyin sayar wa Iran makaman da China ke ƙerawa.

  4. Assalamu alaikum!

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,Barkanmu da Safiyar wannan rana ta Laraba.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.