Za a binne jagoran addinin Iran Ali Khamenei ranar 8 ga Yuli

Asalin hoton, Getty Images
An sanar da cewa za a binne tsohon jagoran Iran, Ali Khameneia ranar 8 ga watan Yulin 2026, watanni uku bayan mutuwarsa a hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai masa.
A cewar sanarwar da ofishin wallafa ayyukansa ya fitar, za a fara gudanar da jana’izarsa a ranar 4 ga Yuli a Tehran, kafin a binne shi a ranar 8 ga watan Yuli a harabar masallacin Imam Reza da ke Mashhad.
An kuma ce za a gudanar da jana’izar wasu daga cikin ’yan uwansa da suka mutu tare da shi a hare-haren, a garuruwa daban-daban da suka haɗa da Tehran, Qom da Mashhad.
Haka zalika, jami’ai sun bayyana cewa ana sa ran taron zai tara miliyoyin jama’a, inda aka tsara shirye-shirye na musamman ciki har da gangamin jama’a na kwanaki uku.




















