Mawaƙan Najeriya da suka taba halartar tarukan duniya

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Aiko rahoto daga, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A taron gangamin fara gasar cin kofin duniya ta bana, mawaƙan Najeriya na cikin waɗanda suka baje-kolin fasaharsu ta waƙoƙi, inda suka yi haɗaka da mawaƙan duniya wajen nishaɗantar da mahalarta taron.

Mawaƙan Najeriya sun daɗe suna nuna bajinta a masa'antar waƙa ta duniya, inda tun a shekarun baya aka fara ganin tasirinsu.

Wannan taron fara gasar cin kofin duniyar ya ƙara fito a fasaha da ƙwarewar mawaƙan Najeriya a idon duniya, wataƙila saboda waɗanda suka yi haɗakar da su fitattun mawaƙa ne da ke amo a duniya.

Sai dai ba wannan ba ne karon farko da mawaƙan Najeriya suka yi wasa a taron buɗe gasar cin kofin, domin wasu mawaƙan Najeriya sun yi waƙoƙi a gasannin baya, da gasar zakarun turai da ma wasu manyan taruka na duniya.

Wannan ya sa wannan maƙalar ta tattaro wasu mawaƙan da suka taɓa gudanar da wasa a tarukan duniya.

Femi Kuti

Ɗaya daga cikin mawaƙan Najeriya na farko-farko da suka yi wasa a taron gasar kofin duniya shi ne Femi Kuti.

Tauraron waƙoƙin na salon Afrobeat ya kasance a cikin jerin mawaƙan da suka yi wasa a bikin buɗe gasar cin kofin duniya ta FIFA ta shekarar 2010 a Afirka ta Kudu. Bikin, wanda aka gudanar a filin wasa na Soccer City da ke Johannesburg, ya mayar da hankali sosai kan al'adun Afirka, sannan fitattun mawaƙan nahiyar ta Afirka da dama sun halarta.

2Baba

Wani fitaccen mawaƙin daga Najeriya da ya taka rawa a gasar cin kofin duniya shi ne Innocent Idibia, wanda aka fi sani da 2Baba.

Ya yi wasa a bikin rufe gasar cin kofin duniya ta 2010 a Johannesburg. FIFA ta zaɓe shi cikin gungun fitattun mawakan Afirka da suka yi bikin kammala gasar wadda aka fafata a Afirka.

Burna Boy

Mawaƙin da ya fi ɗaukar hankali shi Damini Ogulu, wanda aka fi sani da Burna Boy wanda ya nishaɗantar da mahalarta taron gasar cin kofin duniya da ake bugawa a yanzu.

Burna Boya ya kasance cikin waɗanda suka yi waƙar gasar a hukumance, maimakon kawai gabatar da waƙa ga mahalarta taron.

Yana cikin waɗanda suka yi waƙar gasar ta "Dai Dai" tare da fitacciyar mawaƙiya ƴar ƙasar Colombia, Shakira.

Sun gabatar da waƙar a bikin buɗe gasar da aka gudanar a birnin Mexico City ranar Alhamis, 11 ga Yuni, 2026.

Rema

Shi ma mawaƙin Afrobeats mai suna Divine Ikubor, wanda aka fi sani da Rema, ya yi wasa a ɓangare na bikin buɗe gasar cin kofin na duniya da aka gudanar a Amurka a ranar Juma'a, 12 ga Yuni, 2026. Ya yi wasa tare da manyan taurarin duniya kamar Katy Perry da Tyla daga Afirka ta Kudu.

Kafin fara gasar, FIFA ta ƙaddamar da wata waƙa mai alaƙa da gasar cin kofin duniya wadda ta haɗa Rema, Lisa da mawaƙiyar Brazil, Anitta.

Davido

Shi ma mawaƙi David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya taka rawa a wasannin share fagen fara gasar cin kofin duniya.

Wani abu da ya ƙara jan hankali shi ne yadda ya halarci taron sanye da rigar da ke ɗauke da sunayen ɗalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo.

Wannan ya sa mawaƙin ya samu yabo daga Najeriya kan yadda ya jawo hankali kan matsalar tsaro a Nijeriya tare da kira ga gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa domin ceto waɗanda har yanzu suke hannun masu garkuwa.

Patoranking

Shi ma mawaƙin reggae Patoranking ya halarci wani taro da ke da alaƙa da gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar a shekarar 2022.

Ya yi wasa kai tsaye a FIFA Fan Festival da ke Al Bidda Park a ranar 28 ga Nuwamba, 2022.

Wasu tarukan duniya da mawaƙan Najeriya da suka halarta

Rema

Sunansa Divine Ikubor amma an fi saninsa da Rema harkar waƙoƙin gambara.

ya halarci taron karrama gwarazan ƴan ƙwallon ƙafa ta Ballon d'Or wanda aka yi a ranar 30 ga Oktoban 2023, inda ya rera waƙasar ta 'Calm Down'.

Tiwa Savage

Sunanta Tiwatope Omolara Savage da aka fi sani da Tiwa mai shekara 44 kuma mawaƙiya ce kuma jarumar fina-finan Nollywood.

Ta shahara a fagen zuben waƙoƙi na Afirka da kuma gambara.

Tiwa ta halarci bikin naɗa Sarkin Ingila, Sarki Charles III.

Burna Boy

Burna Boy ya halarci ƙaddamar da Gasar Chamions League na Turai da aka yi a Filin Wasa na the Ataturk Olympic Stadium da ke Turkiyya a 10 ga watan Yunin 2023.

Wizkid

Shi ma Ayodeji Balogun wanda aka fi sani da Wizkid ya shirya taron kalankuwa a filin wasa na Tottenham Hotspur da ke London, a ranar 29 ga Yulin 29, 2023. Taron ya samu mahalarta 45,000.

Me ya sa ake barin mawaƙan Hausa a baya?

A wata tattaunawarsa da BBC kan me ya sa hakan ke faruwa? Dokta Ibrahim Sheme, wanda masani ne a kan harkokin Kannywood da fina-finai, inda ya ce yanayin harshen na cikin abubuwan da suka jawo hakan.

A cewarsa, "Yawanci mawaƙa ne na Hausa shi kuma Hausa harshe ne na wasu ba gama-gari ba."

Sai dai ya ce ko a Kudun akwai waƙoƙin Yarbawa da na Ibo, waɗanda ya bayyana cewa ba sa yin tasiri kamar na turancin.

"Ko a irin su YouTube masu amfani Turanci sun fi samun kuɗi a kan na Hausa. Shi ya sa ake gayyata na Turanci saboda su aka fi sani sannan sun fi mu wayewa da shiga wurare. Misali muna da mawaƙa a Turai irin su Chizo Germany da Bello Cisko amma an fi sanin na Turancin fiye da su. Turanci yare ne duniya."

A game da yadda za a yi domin mawaƙan su fara kai wa matakin duniya, Ibrahim Sheme cewa ya yi, "Su riƙa yin waƙoƙi da Turanci suna haɗa wa da na Hausa. Misali idan mutum ya yi na Hausa biyar, sai ya yi na Turanci ɗaya."