Wane ne Abu Salim al-Barnawi, mai ɗaukar hoton ISWAP da sojojin Najeriya suka kashe?

Abu Salim

Asalin hoton, HQ Nigerian Army

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Ana cigaba da tattaunawa kan irin sauya salon yaƙi da mayaƙan Boko Haram da Iswap suka yi, musamman ta hanyar amfani da salon yaɗa labarai domin cimma burin yaɗa farfaganda.

Wannan wani salo ne da mayaƙan suka aro suka yafa daga ƙungiyoyin mayaƙa manya, inda suke amfani da kafofin sadarwa wajen yaɗa nasarorinsu da manufar ƙungiyar da kuma nuna ƙwanjinsu.

Wannan ya sa kashe Abu Salim al-Barnawi, wanda shi ne babban mai ɗaukar hoto na ƙungiyar ISWAP ya ɗauki hankali

A baya, mayaƙa ne kaɗai suke da muhimmanci, amma yanzu alamu na nuna cewa ƙungiyoyin sun fara bunƙasa tare da muhimmantar da wasu masu kula da wasu ɓangarori na ƙungiyar.

Sojojin Najeriya sun ce sun kashe Abu Salim tare da wasu masu taya shi aiki a sashen yaɗa labaran ISWAP a wani gumurzu da suka yi a ranar 12 ga Yuli 2026.

Wane Abu Salim? kuma wace rawa yake takawa a ƙungiyar da ya sa yake da muhimmanci a cikinta?

Wane ne Abu Salim?

Sojojin sun ce an gano kyamara daga cikin kayayyakin da aka ƙwato bayan gumurzun da aka yi har aka kashe shi, wanda a cewar rundunar ya ƙara tabbatar da wane ne shi da kuma aikin da yake yi.

Abu Salim shi ne yake jagorantar zuwa ɗauko hotuna da bidiyo na hare-haren ƙungiyar, tare da jagorantar fitar da hotuna da bidiyo na ƙungiyar a kafofin sadarwa wajen farfagandar ƙungiyar.

Rundunar sojin ta bayyana Abu Salim a matsayin tsohon kwamanda da ya jagoranci ƙaddamar da hare-hare, inda ya kasance cikin wasu hare-haren da ƙungiyar ta kai a bakin iyakar Najeriya da Kamaru, kafin daga bisani aka mayar da shi ɓangaren yaɗa labaran ISWAP.

Sauyin matsayinsa ya nuna yadda ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya ke canza salon yaƙi, inda suke amfani da mayaƙa wajen ƙaddamar da hare-hare, da kuma wasu a gefe da suke yaɗa ayyukan ƙungiyar.

Yaya muhimmancinsa?

Rundunar sojin ta ce ISWAP ta tabbatar da mutuwar Abu Salim ta hanyar fitar da wani bidiyon jimami.

BBC ta ga bidiyon da ake yaɗawa, duk da ba mu tabbatar da kafar da aka wallafa shi a farko ba, inda a ciki aka nuna yadda Abu Salim ke gudanar da aikace-aikacensa a ƙungiyar.

Ga ISWAP, hotunan nasarar hare-hare da bidiyoyin mayaƙanta da saƙonnin da take yaɗawa sun kasance masu muhimmanci wajen nuna cewa ƙungiyar na da ƙarfi duk da matsin lambar da take fuskanta daga jami'an tsaro.

Daga cikin muhimmancin ɓangaren sadarwa a ƙungiyar, akwai yaɗa hotuna da bidiyo da saƙonnin farfaganda da ake amfani da su wajen yaɗa manufofin ƙungiyar da jawo sabbin mambobi.

Tasirin kashe shi

Rahoton kashe Abu Salim ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ƙoƙarin yaƙi da ƙungiyar ta hanyar amfani da soji da kuma raunana hanyoyin ayyukan ƙungiyar, ciki har da sadarwa da sauran abubuwan rayuwa da suke buƙata.

Sojojin sun ce an kashe wasu manyan mayaƙan ƙungiyar ciki har da Abu Umar Khattab and Abu Khalid Usman a gumurzun na Cross Kauwa, yayin da wasu suka samu raunuka yayin da suke tserewa.

Sai dai tambayar da ake yi ita ce: shin rasa masu yaɗa farfaganda zai iya yin babban tasiri wajen raunana ƙungiyar da ta shafe sama da shekaru goma tana fafatawa da gwamnati?

Duk da cewa makamai da mayaƙa ne suka fi muhimmanci ga ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, sadarwa da ɗaukar sabbin mambobi da kuma yaɗa farfaganda ma na da matuƙar muhimmanci.