Tinubu zai tafi Makkah don 'yi wa Najeriya addu'a'
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja babban birnin ƙasar a ranar Alhamis zuwa birnin Makkah da ke ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Umrah.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Bayo Onanuga ya fitar, ta ce wannan tafiya za ta bai wa shugaban ƙasar damar gudanar da ayyukan ibada da kuma yi wa Najeriya addu'o'in samun zaman lafiya, haɗin kai, kwanciyar hankali da ci gaba mai ɗorewa.
Kafin barin Abuja, Shugaban ƙasar zai ƙaddamar da wasu kayan aiki da rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta saya domin ayyukanta. Za a gudanar da bikin ƙaddamarwar a sashen shugaban ƙasa na filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Ana sa ran Tinubu zai koma Najeriya mako mai zuwa bayan kammala wannan aikin ibada.
A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne Bola Tinubu ya ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa a karo na biyu, a birnin Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Tinubu na shan suka daga ƴan adawa, inda suke zargin shi da gaza inganta tattalin arziƙi, yayin da manufofin gwamnatinsa suka haifar da tashin farashin kayan masarufi.